Wednesday, November 11
Shadow

Tawagar Me baiwa shugaban kasa Shawara kan harkar siyasa, Ibrahim Masari ta yi Hadari

Rahotanni sun bayyana cewa, Tawagar me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar siyasa, Ibrahim Masari ta yi hadari.

Hadarin ya farune a karamar Hukumar Kafur ta jihar yayin da ya je yin wata gaisuwa.

Rahoton yace mutane 2 sun rigamu gidan gaskiya.

Hadimin Ibrahim Masarin me amfani da sunan Wazirin Kabir Ibrahim Masari ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook kamar haka:

“Innalillahi wa’innailaihir raju’u😭😭 Acikin tawagar da suka raka Alh Ibrahim Masari Ta’aziyya Dantitture Yanzu nan ansamu Hatsarin mota wasu sun rasu mutum 2 munkawo wata asibiti

Allah ya jiqansu da rahama, su Kuma masu rauni Allah ya basu lapia.”

Karanta Wannan  An min Wahayi cewa nan gaba a saman wata da kuke gani a sama zamu je mu yi zaman taro>>Inji Pastor Enoch Adeboye

Da fatan Allah ya jikansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *