Thursday, March 26
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Dan Najeriya da ya je Kasar Jamhuriyar Nijar yace Nijar din zai bi yayi Sallah Gobe, ba zai cika Azumi 30 ba

Kalli Bidiyon: Dan Najeriya da ya je Kasar Jamhuriyar Nijar yace Nijar din zai bi yayi Sallah Gobe, ba zai cika Azumi 30 ba

Duk Labarai
Dan Najeriya, Faruk da ya je Nijar yace a kasar ta Nijar an ga watan Shawwal na sallah dan haka gobe za'a yi sallah. Yace shima gobe zai ajiye Azuminsa yayi Sallah ba zai cika Azumi 30 ba kamar yanda za'a yi a Najeriya ba. https://www.tiktok.com/@faruq_abuja_back_up/video/7618709603345288468?_r=1&_t=ZS-94nsQ1H1uz3&sp_source=7537614245375297080
An kama sojan Najeriya da fashi da makami

An kama sojan Najeriya da fashi da makami

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Abia na cewa an kama sojan Najeriya me suna Lance Corporal Chukwu Ebuka da zargin fashi da makami. Sojan yawa wani mutum da ba'a tantance kowanene ba fashin Naira Miliyan 4.9 Sojan yace yana aiki ne da bataliyar 14 Brigade dake Ohafia a jihar Abia. A Bidiyon sojan da ya watsu a kafafen sada zumunta an ji wani babban soja na masa tambayoyi. Sojan dai ya amsa duka laifukan da ake zarginsa da aikatawa a Bidiyon. https://twitter.com/i/status/2034319639384138193
Kalli Bidiyon: Duk wanda baya gamsar da matarsa, akwai yiyuwar zata bi maza>>Inji Alkarmawi

Kalli Bidiyon: Duk wanda baya gamsar da matarsa, akwai yiyuwar zata bi maza>>Inji Alkarmawi

Duk Labarai
Malam Alkarmawi na Kano ya bayyana cewa, yana da muhimmanci magidanci ya rika gamsar da matarsa. Yace idan ya zamana magidanci baya iya gamsar da matarsa, a irin hakane a ke samun matan aure na bibiyar maza. https://www.tiktok.com/@binkabeer35/video/7618292854976269589?_r=1&_t=ZS-94nIA3BWkEL&sp_source=7537614245375297080 Yace suma mata masu kin yiwa mazansu biyayya, su ji tsoron Allah.
Kalli Bidiyon; Wasu da ke ikirarin su musulmai ne amma basa Sallah, basa Azumi, saidai Zikiri da jan Charbi

Kalli Bidiyon; Wasu da ke ikirarin su musulmai ne amma basa Sallah, basa Azumi, saidai Zikiri da jan Charbi

Duk Labarai
Wata Kungiya dake ikirarin Musulunci amma basa sallah basa Azumi a kasar Senegal sun shirya wani Biki. Kungiyar me sunan Baye Fall an kafata ne sama da shekaru 100 da suka gabata saboda wani shehi da yayi zamani wanda ke da zuhudu. Sukan bar gashi dada da kuma saka kaya yagaggu dan koyi da shehin nasu. Kuma sukan ria jan carbi amma basa sallah kuma basa Azumi. Saidai suna taya Musulmai masu azumi murna har ma sukan dafa abinci su basu. https://twitter.com/i/status/2034218340000870774
Kotu tace doka ta baiwa ‘yan Najeriya damar daukar ‘yansanda Bidiyo yayin da suke gudanar da aikinsu

Kotu tace doka ta baiwa ‘yan Najeriya damar daukar ‘yansanda Bidiyo yayin da suke gudanar da aikinsu

Duk Labarai
Kotu tace doka ta baiwa 'yan Najeriya damar daukar 'yansanda Bidiyo yayin da suke gudanar da aiki. Babbar Kotun tarayya dake Warri, Jihar Delta ce ta yi wannan hukuncin. A karkashin mai shari'a, Justice H. A. Nganjiwa inda tace 'yan Najeriya na da damar daukar 'yansanda Bidiyo yayin da suke aiki a bainar jama'a. Sannan ta baiwa wanda ya shigar da karar, Maxwell Uwaifo nasara akan 'yansanda nasara inda tace a biyashi diyyar Naira Miliyan 5 sannan a bashi wata Naira Miliyan 2 dan ya biya kudin daukar lauya da wahalhalun karar da ya shigar.
Da Duminsa: Gwamnatin Kano ta bayyana sarkin da ta amince yayi hawan Sallah a Kano

Da Duminsa: Gwamnatin Kano ta bayyana sarkin da ta amince yayi hawan Sallah a Kano

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta fitar da sanarwar sarkin data amince yayi hawan Sallah a Kano. Gwamnatin tace Sarki Muhammad Sanusi II ne ta amince yayi hawan saidai ta saka doka dan gujewa tashin hankali. Kwamishinan watsa labarai na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya fitar da sanarwar a ranar Laraba inda yace an saka dokoki wajan hawan ne bayan bayanan sirri da suka samu cewa wasu na shirin tayar da rikici a wajan hawan Sallar. Da Dumi Dumi Gwamnatin Kano ta ce Sarki Muhammad Sanusi II ne zai yi Hawan Sallah Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta fitar da sabbin tsauraran matakai kan bukukuwan Sallah domin kauce wa rikici da tabbatar da zaman lafiya. A cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar ya fitar, gwamnatin ta ce ta samu sahihan bayanan ...