Ku kawo mana rahoton duk wanda bashi da aikin yi amma yake rayuwar kece raini>>Inji Ministan tsaro,Bello Matawalle
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana cewa, a kawo musu rahoton duk wani da baya da aikin yi amma yana wadaka da kudade a cikin al'umma.
Ministan ya bayyana hakane a gidan gwamnatin jihar Sokoto.
Yace irin wadannan mutane ka iya zama wakilan 'yan Bindiga masu basu bayanan sirri akan jama'a suna zuwa suna cutar dasu.
Ya kuma nemi jama'ar jihar da su taimakawa jami'an tsaro da bayanan sirri wanda dasune zasu yi amfani wajan samun nasara.
Ministan ya ziyarci jihar ta Sokoto tare da shuwagabannin hukumomin tsaro ne bisa umarnin shugaban kasa dan magance matsalar tsaro.