Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Dan takarar jam’iyyar Adawa na kasar Kamaru yace shine ya lashe zaben shugaban kasar

Dan takarar jam’iyyar Adawa na kasar Kamaru yace shine ya lashe zaben shugaban kasar

Duk Labarai
Jagoran adawar Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya yi iƙirari samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi. Cikin wani bidiyo da ya fitar, da tsakar daren da ya gabata, Mista Bakary ya gode wa al'ummar Kamaru kan ''yarda da samar da canji'' da ya ce sun yi a ƙasar. Iƙirarin nasa na zuwa a daidai lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ke ci gaba da tattara sakamakon zaɓukan. “Ina son bayyanawa cikin girmamawa da nutsuwa cewa al'ummar Kamaru sun yi zaɓinsu, don haka ya kamata a martaba zaɓinsu,'' in ji Bakary. Ya kuma alƙawarta wallafa cikakken sakamakon zaɓukan daga rumfunan zaɓen ƙasar. “Haƙiƙa wannan nasara ba tawa kaɗai ba ce ni kaɗai, ta kowa ce,'' in ji shi. Kawo yanzu hukumomin Kamaru ba su ce komai ba game da iƙirarin jagorar adawar, to amma a baya ministan ci...
Gwamnan Jihar Edo, Okpebholo ya bayyanawa Kwamishinoninsa cewa, rashin saka hular Shugaba Tinubu zuwa wajan aiki babban laifi ne

Gwamnan Jihar Edo, Okpebholo ya bayyanawa Kwamishinoninsa cewa, rashin saka hular Shugaba Tinubu zuwa wajan aiki babban laifi ne

Duk Labarai
Gwamnan jihar Edo, Okpebholo ya bayyanawa ma'aikatan jiharsa cewa dolene duk wanda zai je wajan aiki ya zamana yana sa hular shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Yace rashin saka hular babban laifine wanda ba zai yafe ba. https://twitter.com/dammiedammie35/status/1978343107671273696?t=bC020eNHsq9RA8MLEvr4JA&s=19
Matashi me suna Abdullahi dan jihar Katsina da ya yi ridda ya koma Kirista ya fito ya godewa Allah inda yace da yana hanyar bata Amma yanzu Allah ya nuna masa hanyar gaskiya

Matashi me suna Abdullahi dan jihar Katsina da ya yi ridda ya koma Kirista ya fito ya godewa Allah inda yace da yana hanyar bata Amma yanzu Allah ya nuna masa hanyar gaskiya

Duk Labarai
Matashin nan na jihar Katsina wanda yayi ridda ya koma Kirista, ya fito ya kara tabbatarwa da mutane maganar komaw Kirista da yayi. Yace yana tuba ga Allah bisa kuskuren da yayi a baya na kasancewa a cikin addinin Musulunci. A yanzu yace ya kama Kiristanci wanda a tunaninsa shine daidai. https://www.tiktok.com/@mohammedmhammed76/video/7560690225362504968?_t=ZS-90YxF7JPKb2&_r=1
Kalli Bidiyo: Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu yana tunanin kasar Faransa ce zata bashi mulki karo na 2 shiyasa yake musu biyayya>>Inji Shugaban Nijar

Kalli Bidiyo: Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu yana tunanin kasar Faransa ce zata bashi mulki karo na 2 shiyasa yake musu biyayya>>Inji Shugaban Nijar

Duk Labarai
Shugaban mulkin soji na kasar Nijar, Tchani ya yi zargin cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na Najeriya, yana tunanin kasar faransa ce zata bashi damar sake cin zabe a shekarar 2027. Yace dalili ma kenan da shugaba Tinubu kewa kasar ta Faranaa biyayya. Ya bayyana hakane a wara hira ta musamman da aa yi dashi inda ya bayyana irin gudummawar da kasar Nijar ta baiwa Najeriya a shekarun baya. https://www.tiktok.com/@habibou.adamou..227/video/7560880169209171212?_t=ZS-90XH5ls0HdB&_r=1
Kalli Bidiyon: Malmin Imamu Malik Dan Shi’ane sannan Turawan Ingila ne suka kawo Wahabiyanci dan raba kan Musulmai >>Inji Malam Nura Khalid

Kalli Bidiyon: Malmin Imamu Malik Dan Shi’ane sannan Turawan Ingila ne suka kawo Wahabiyanci dan raba kan Musulmai >>Inji Malam Nura Khalid

Duk Labarai
Malam Nura Kalid ya bayyana cewa da yawa basu sani ba, malamin Imamu Malik dan shine, yana daya daga cikin limaman Shi'a. Sannan yace Ita kuma Wahabiyanci, Turawan ne suka kawo ta fan raba kan musulmai. Ya bayyana hakane a wannan Bidiyon na kasa: https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7560201522907319559?_t=ZS-90YJWxqxAxN&_r=1
Nine na roki Shugaba Tinubu ya yafe mata, saboda yanke mata hukunci ba zai dawo da dana ba>>Inji Mahaifin Mijin Maryam Sanda

Nine na roki Shugaba Tinubu ya yafe mata, saboda yanke mata hukunci ba zai dawo da dana ba>>Inji Mahaifin Mijin Maryam Sanda

Duk Labarai
Mahaifin mijin Maryam Sanda, Alhaji Ahmed Bello Isa ya bayyana cewa, shine ya roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa matar dansa duk da itace ta kashe dan nasa. Alhaji Ahmed Bello Isa yace aiwatarwa da Maryam Sanda hukuncin kisa ba zai dawo da dansa,Bilyaminu Bello ba. Yace maimakon haka ya zabi yafe mata dan a saketa ta kula da 'ya'yanta kanana. Ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata wadda suka gudanar shi da mahaifin Maryam Sanda, Alhaji Garba Sanda
Mun rabawa ‘yan Najeriya tallafin Naira Biliyan 300>>Inji Gwamnatin Tarayya

Mun rabawa ‘yan Najeriya tallafin Naira Biliyan 300>>Inji Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta rabawa 'yan Najeriya kudin Tallafi har Naira Biliyan 300. Gwamnatin tace ta raba wadannan kudade ne ga gidaje Miliyan 8.1. Karamin Ministan Jin kai, Yusuf Sanunu ne ya bayyana hakan a Abuja a wajan wani taro da aka gudanar. Yace hakan ya karfafa mutane ya inganta Iliminsu, ya kuma Inganta Lafiyarsu. Hakanan yace akwai shirin baiwa wanda iftila'in Ambaliyar ruwa ta fadawa a fadin Najeriya tallafin Naira Biliyan 6.3 na bashi wanda babu ruwa. Yace mutane 21,000 ne zasu amfana da wannan bashin.
Kalli Bidiyo: Idan ba debabben Albarka ba, babu wanda zai rika maganar yanda akawa mahaifinsa Kachiya>>Inji Sheikh Maqari

Kalli Bidiyo: Idan ba debabben Albarka ba, babu wanda zai rika maganar yanda akawa mahaifinsa Kachiya>>Inji Sheikh Maqari

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, idan ba debabben Albarka ba, babu wanda zai rika tattauna yanda aka yiwa mahaifinsa kachiya. Yace dan haka tattauna maganar ma bata kamata ba, idan daliban Ilimi sun ji hakan su daina shiga. https://www.tiktok.com/@habibou.adamou..227/video/7560880169209171212?_t=ZS-90XH5ls0HdB&_r=1