Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kasuwar Kiripto ta yi mummunar asarar da bata taba yi ba a Tarihi, An yi Asarar da Biliyan $19.6

Kasuwar Kiripto ta yi mummunar asarar da bata taba yi ba a Tarihi, An yi Asarar da Biliyan $19.6

Duk Labarai
Rahotanni sun ce kasuwar Kirypto ta tafka gagarumar Asarar da ba'a taba ganin irinta ba a Tarihi. Rahotanni sun ce a cikin awanni 24, kasuwar ta tafka asarar dalar Amurka Biliyan $19.6. Hakan na zuwa ne bayan da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da shirin kakabawa kasar China sabon haraji na kaso 100. Hakanan labarin cewa an yiwa manhajar Binance kutse ya kawo tarnaki a kasuwar ta Crypto inda daga baya mutane suka kasa amfani da Binance din da Coinbase. Saidai an ga wani sun kintaci wannan yanayi sun ci ribar makudan kudade wanda hakan yasa ake zargin cewa ko dai da gangan aka yi hakan ko kuma sun samu bayanan sirri game da karyewar kasuwar.
Ko Miliyan 10 za’a bani ba zan iya sumbhatar ‘yar guda ba>>Inji Gfresh Al-amin

Ko Miliyan 10 za’a bani ba zan iya sumbhatar ‘yar guda ba>>Inji Gfresh Al-amin

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa ko Miliyan 10 za'a bashi ba zai iya yiwa 'yar gida Sumbata ba. Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya kafe hotonta yana mata ba'a. Yar guda dai ta dauki hankula tun bayan da aka kama abokin tabararta, Idris Maiwushirya. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7558996798803594503?_t=ZS-90RbimeeS3N&_r=1
Kalli Bidiyon:Yanda Matar aure ta kama Mijinta yana cin Amanarta da yayarta uwa daya uba daya a Kano

Kalli Bidiyon:Yanda Matar aure ta kama Mijinta yana cin Amanarta da yayarta uwa daya uba daya a Kano

Duk Labarai
Wata matar aure ta kama mijinta yana cin amanarta tare da yayarta Uba daya Uba daya. Matar ta aikawa Malam Abdallah Gadon kaya da tambaya. Inda tace yayar tata ta je gidansu ne inda mijin ya rika shiga dakin da take yana lalata da ita. shine take neman shawara. https://www.tiktok.com/@dr_abdallah_gadon_kaya/video/7558867759086669074?_t=ZS-90RYMiRGHdg&_r=1
Shin da Gaske Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam’iyyar ADC? Ji bayani dalla-dalla

Shin da Gaske Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam’iyyar ADC? Ji bayani dalla-dalla

Duk Labarai
Rahotanni nata yawo a kafafen sada zumunta cewa babban malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya koma jam'iyyar ADC daga jam'iyyar APC. A kwanannan dai ana ta ganin shuwagabannin jam'iyyun siyasa na ta zawarcin Pantami inda suke kai masa ziyara gida. Lamarin ya dauki hankula inda ake ta muhawara masu zafi. Saidai har yanzu shi Pantami ko wata kafa me zaman kanta bata fito ta tabbatar da komawarsa jam'iyyar ADC ba.
Da Duminsa: WhatsApp zasu daina Amfani da lambar waya inda zasu koma amfani da Username kamar sauran Social Media

Da Duminsa: WhatsApp zasu daina Amfani da lambar waya inda zasu koma amfani da Username kamar sauran Social Media

Duk Labarai
Manhajar sada zumunta ta WhatsApp zasu daina amfani da lambar waya wajan gane mutum. WhatsApp zasu koma amfani da Username inda hakan wani mataki ne na baiwa mutane sirri. Tuni Rahotanni suka bayyana cewa, an fara gwajin hakan amma ba'a bayyanashi ga sauran Al'umma ba. Nan gaba kadanne ake tsammanin kowa zai fara amfani da wannan sabon tsari da zarar an kammala gwajinsa.
Ana Binciken karamin yaro me shekaru 17 saboda sayen fili Hectares dubu goma sha hudu (14,000 Hectares) a jihar Edo

Ana Binciken karamin yaro me shekaru 17 saboda sayen fili Hectares dubu goma sha hudu (14,000 Hectares) a jihar Edo

Duk Labarai
Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya sanar da cewa suna binciken wani karamin yaro me shekaru 17 bayan da ya sayi filaye masu girman Hectares dubu goma sha hudu(14,000 Hectares). Yaron dai ya biya kudin filayen da ya siya. Gwamnan yace suna binciken inda matashin ya samu wadannan kudade. Sannan yace an dakatar da C of O da akewa filayen da yaron ya siya.