Muna tabbatar da ingancin man fetur din da ake shigo dashi Najeriya>>Gwamnati ta mayarwa da Dangote Martani
Hukumomin SON, da NMDPRA sun mayarwa Dagote Martanin cewa duk man fetur din da za'a shigo dashi Najeriya sai sun tabbatar da ingancinsa.
Hukumomin sun bayyana hakane bayan da Dangote yayi zargin cewa 'yan kasuwar man fetur na zuwa kasashen waje dan siyo man fetur da bashi da inganci cikin kasarnan mai makon su sayi na matatar man fetur dinsa.
Dangote dai ya kai 'yan kasuwa da suka hada da A.A Rano, AY Shafa,da kamfanin man fetur na kasa NNPCL kotu inda yake neman kotu ta hanasu shigo da man fetur cikin kasarnan har sai idan matatarsa ta kasa samar da man fetur din.
Saidai A.A Rano da AY Shafa sun zargi Dangote da kokarin kare kasuwancinsa.