
Bayan da Kiraye-Kiraye suka yi yawa a karshe dai EFCC tace zata binciki tsohon Tsageran Niger Delta, Tampolo saboda wulakanta Naira
Mutane da yawa ne suka yi ta kiran EFCC ta binciki Tubabben tsageran Naija Delta, Tampolo saboda yanda aka ganshi yana wulakanta Naira kamar yanda aka hukunta mutane da yawa a baya.
Hukumar ta EFCC ta fito tace lallai babu wanda yafi karfin doka kuma zata gayyaci Tampolo dan ya amsa tambayoyi kan wulakanta Nairar.