Monday, April 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

EFCC ta saki Tambuwal bayan tsare shi na kwana guda

EFCC ta saki Tambuwal bayan tsare shi na kwana guda

Duk Labarai
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC ta saki tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal. Wasu makusantan Sanatan ne suka tabbatar wa BBC sakin nasa, kuma yanzu haka yana gidansa na Abuja. A ranar Litinin ne hukumar ta tsare shi a Abuja, bayan amsa gayyata kan zarge-zargen fitar da maƙudan kuɗaɗe da suka kai Naira biliyan 189. Kamun da aka yi masa ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, musamman tsakanin ƴan hamayya, waɗanda ke zargin hakan na da alaƙa da rawar da yake takawa a tafiyar ƴan jama'iyyar haɗaka ta ADC.
Bello El-Rufai da Sadiq Zololo sun sayi Kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees

Bello El-Rufai da Sadiq Zololo sun sayi Kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees

Duk Labarai
Dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Bello El-Rufai tare da Dan wasan kungiyar Real Sociedad, Sadiq Zololo sun sayi kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees. Kungiyar Kwallon kafa ta Ranchers Bees ta kasance a gasar Premier league ta Najeriya tun daga shekarar 1970. Da yake magana game da sayen Kungiyar, Sadiq ya bayyana farin ciki da kokarin da suke na dawo da martabar kungiyar. Sadiq ya bayyana cewa, ya taso tun yana yaro yake son Kungiyar ta Ranchers Bees.
ABIN FARIN CIKI: Jami’ar Musulunci Ta Madina Ta Ayyana Littafin Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo A Kololuwar Mataki

ABIN FARIN CIKI: Jami’ar Musulunci Ta Madina Ta Ayyana Littafin Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo A Kololuwar Mataki

Duk Labarai
Daga Khalid Yusuf Sambo Kamar yadda a ke ganin a hoton da ke kasa, shahararriyar Jami'ar nan ta Musulunci ta Duniya da ke Birnin Madinar Manzon Allah (S.A.W) ta ayyana Littafin: ضوابط الجرح والتعديل عند الحافظ الذهبي Wallafar Prof. Muhd Sani Umar R/lemo (Hafizahullah) a cikin jerangiyar littafan da za ta yi wa daliban da ke gurbin karatun Digiri na uku (Ph.D) Jarrabawa a cikinsa. Shi ne Littafi daya tilo na mutumin yankin kaf Afirka da ya samu wannan tagomaci. Hakika wannan yana sake nuna karbuwar Littafin da ficensa a Duniyar ilimi. Da ma kuma Littafi ne da ba a shaida kamarsa a bangarensa ba. Littafin shi ne kundinsa na samun shaidar kammala matakin Digiri na biyu a Jami'ar Musulunci ta Madina, wanda a lokacin ya rabauta na samun koluluwar mataki da jinjina mafi girma a fanni...
ADC TA RIKICI A KEBBI: Shugabanin Jam’iyar ADC A Jihar Kebbi Sun Dakatar Da Ciyaman Engr. Sufiyanu Bala Da Mataimakinsa Junaidu Muhd Da Kuma Sakataren Jam’iyyar Hauwa’u Muhammad

ADC TA RIKICI A KEBBI: Shugabanin Jam’iyar ADC A Jihar Kebbi Sun Dakatar Da Ciyaman Engr. Sufiyanu Bala Da Mataimakinsa Junaidu Muhd Da Kuma Sakataren Jam’iyyar Hauwa’u Muhammad

Duk Labarai
ADC TA RIKICI A KEBBI: Shugabanin Jam'iyar ADC A Jihar Kebbi Sun Dakatar Da Ciyaman Engr. Sufiyanu Bala Da Mataimakinsa Junaidu Muhd Da Kuma Sakataren Jam'iyyar Hauwa'u Muhammad A sanarwar da suka fitar ga manema labarai, Shugabannin su sha bakwai dukkansu sun aminta da dakatarwa a bisa zaŕge-zargen da suka gabatar.
Masu Laifi 16 sun tsere daga gidan gyara hali dake Keffi jihar Nasarawa

Masu Laifi 16 sun tsere daga gidan gyara hali dake Keffi jihar Nasarawa

Duk Labarai
Masu laifi 16 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Keffi dake jihar Nasarawa Lamarin ya farune da sassafiyar ranar Talata. Me magana da yawun hukumar kula da gidajen gyara hali na kasa, Umar Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace jami'an hukumar 5 ne suka jikkata sanadiyyar lamarin. Yace 2 daga ciki suna cikin mawuyacin hali Saidai yace an kama 7 daga cikin wadanda suka tsere kuma ana bin sahun sauran.
Amarya, Rahama Sadau ta godewa ‘yan Uwa da abokan arziki da suka tayata Biki

Amarya, Rahama Sadau ta godewa ‘yan Uwa da abokan arziki da suka tayata Biki

Duk Labarai
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta mika sakon godiya ga 'yan uwa da abokan arziki da suka tayata Biki. Rahama ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace bata da kalaman godiya da zata iya bayyana irin farin cikin da take ciki. "Ina mika sakon godiya ta musamman ga dangi, ’yan uwa da abokan arziki bisa fatan alheri da addu’o’in ku a game da Auren mu. Kalmominku da addu’arku sun karfafa mana guiwa kuma sun sa ranar ta kasance ta musamman. Allah Ya saka da alkhairi. Bani da kalmomin yi muku godia sai dai nace Allah ya saka muku da alheri, Allah yabar zumunchi na gode, na gode, Allah ya biyawa kowa bukatun sa na alheri. Ameen Ni kuma Allah ya bamu zaman lafia da Miji na Allah ya Albarkachi rayuwar auren mu. Ameen ya rabbil Alameen. Ina yiwa kowa fatan alhe...
Wasu magoya bayan Tinubu sun gaya min cewa ‘yan Arewa jahilaine>>Inji Babachir Lawal

Wasu magoya bayan Tinubu sun gaya min cewa ‘yan Arewa jahilaine>>Inji Babachir Lawal

Duk Labarai
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya bayyana cewa, Akwai wata kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da yake cikinta wadda suka ce 'yan Arewa jahilaine. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace ya gaya musu cewa wannan mutane sune ake neman kuri'arsu. Yace Salon Mulkin Tinubu bai yi masa ba inda yace da ace yana cikin gwamnatin Tinubu da tuni ko dai ya sauka daga mukaminsa ko an koreshi ko wani abun.