Maganin rashin sha’awa ga mace
Rashin sha'awa ko raguwar karfin sha'awa ga mata abune dake faruwa yau da gobe kuma yana faruwa da kowace mace a iya tsawon rayuwarta.
A wani lokacin zaki ji karfin sha'awarki ya ragu na dan lokaci ko na kwanaki kadan, a wani lokacin kuma zai iya daukar kwanaki da yawa ko ma watanni.
Kowane mutum da irin karfin sha'awarsa, wani zai ji yana son yin jima'i kullun wani sai bayan satuka ko bayan watanni kai wata ma a shekara ba zata so yin jima'i sosai ba, kowa da kalar karfin sha'awarshi.
Yanayin karfin sha'awarki ba zai taba iya zama a matsayi guda ba a kowane lokaci, ma'ana zai rika yin sama yana kasa, kuma hakan ba matsala bane.
Saidai idan rashin sha'awarki yayi yawa kuma ya fara damunki, to ya kamata a tuntubi likita ko a nemi magani.
Sannan kuma a sani, mafi yawanci ana g...