Monday, February 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Jam’iyyun NNPP, PDP, da ADC na tattauna yanda zasu hade dan kayar da Tinubu a 2027

Jam’iyyun NNPP, PDP, da ADC na tattauna yanda zasu hade dan kayar da Tinubu a 2027

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyun Adawa na NNPP da PDP da ADC na tattaunawa dan hadewa waje daya su kayar da shugaba Tinubu zabe a shekarar 2027. Hakan ya fito ne daga bakin me magana da yawun jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi. Ya bayyana cewa yanayin mulkin da APC ke yi a Najeriya baya bayar da sakamakon da ake bukata. Fan hakane ake bukatar hada kai dan kayar da ita mulki a 2027. https://twitter.com/i/status/2009710056368156994
Kalli Bidiyon: Ji Sabon Sunan da Kwankwaso ya sakawa Abba

Kalli Bidiyon: Ji Sabon Sunan da Kwankwaso ya sakawa Abba

Duk Labarai
A yayin da siyasar Kano ta Dauki Dumi. Shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fara mayar da martani a yayin da ake tsammanin gwamnab Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC. A wajan wani taro, Kwankwaso yace duk wanda ya bar tafiyarsu ta Kwankwasiyya, sunan siyasarsa 'yar Wada. https://twitter.com/i/status/2009515958189080598 Kwankwaso a baya dai ya bayyana cewa, Kamata yayi Abha ya ajiye musu kujerarsu kamin ya koma APC.
Kasar Amurka ta bayyana cewa a yanzu ta Fahimci ba Kiristoci kadai ake Mhuzghunawa a Najeriya ba

Kasar Amurka ta bayyana cewa a yanzu ta Fahimci ba Kiristoci kadai ake Mhuzghunawa a Najeriya ba

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, kasar ta ce ta fahimci hadda Musulmai ayyukan Tshàgyèràn Dhàjì na tabawa ba Kiristoci kadai bane. Hakanan shugaban kasar Donald Trump ya bayyana cewa idan ba'a daina Khisan ba, zai iya sake kawo Khari Najeriya. A baya dai, kasar Amurka ta kawo Khari Najeriya a jihar Sokoto. A yanzu dai ana ta tsammanin wace jiha ce kasar ta Amurka zata kawowa Khari? Wasu dai na cewa Jihar Borno.
Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 7 dan inganta Wutar Sola dake fadar shugaban kasa, watau Villa

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira Biliyan 7 dan inganta Wutar Sola dake fadar shugaban kasa, watau Villa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 7 dan inganta wutar Sola dake fadar shugaban kasar. An ware wadannan kudade ne a kasafin kudin shekarar 2026. A shekarar 2025 gwamnatin ta ware naira Biliyan 10 ne dan saka wutar Solar a fadar shugaban kasar. Hakan na zuwane a yayin da lamarin wutar lantarki ke kara tabarbarewa a Najeriya.