Friday, January 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Sojar Amurka ta bayyana Nawa ake biyansu Albashi kuma ta bayyana nawa ake biyan Danginsu idan suka rigamu gidan gaskiya a bakin aiki

Kalli Bidiyon: Sojar Amurka ta bayyana Nawa ake biyansu Albashi kuma ta bayyana nawa ake biyan Danginsu idan suka rigamu gidan gaskiya a bakin aiki

Duk Labarai
Wata sojar Amurka 'yar Asalin Najeriya ta bayyana nawa akw biyansu Albashi duk wata. Tace ana biyansu dala $4000 ne duk wata a matsayin albashi, Kwatankwacin Naira Miliyan 5,740,000. Sannan tace idan suka rasa ransu a wajan aikin, akan ba iyalansu dala $500,000, kwatankwacin Naira Miliyan 717,500,000 Ta bayyana hakane a wani Live da suka yi ita da Peller. Lamarin ya dauki hankula sosai. https://twitter.com/i/status/2013492598824939547
Kalli Bidiyon ganawar da shugaba Tinubu yayi da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Kalli Bidiyon ganawar da shugaba Tinubu yayi da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da Gwamnan kano, Abba Kabir Yusuf a fadarsa dake Abuja a yammacin ranar Litinin. Ganawar tasu na zuwane yayin da ake ta rade-radin cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC. A sanarwar da me magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa ya fitar, yace gwamna Abba ya gabatarwa da shugaba Tinubu tsare-tsaren gwamnatinsa ne da suka hada da samar da Tsaro, da Ayyukan ci gaba da kuma Hada kai da Gwamnatin tarayya. A sanarwar da Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya fitar, yace a yau, Talata ne Gwamna Abba Kabir Yusuf zai karbi katinsa na zama dan jam'iyyar APC. https://twitter.com/i/status/2013278927289012474
Kallli Bidiyon:Yanda DSS suka sake kama tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami jim kadan bayan da aka sakeshi daga gidan yarin Kuje

Kallli Bidiyon:Yanda DSS suka sake kama tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami jim kadan bayan da aka sakeshi daga gidan yarin Kuje

Duk Labarai
Abubakar Malami, tsohon Ministan shari'a ya kara shiga komar DSS bayan fitowa daga gidan yarin Kuje bayan da aka bayar da belinsa. An ganshi yana fitowa daga gidan yarin inda DSS duka tareshi suka ce ya shiga sun kamashi. An jishi yana tambayarsu wanene shugabansu sannan ya tambayesu su nuna masa ID card dinsu na aiki. https://twitter.com/i/status/2013271478372811196 Ana dai yiwa Malami sabon zargin mallakar makamai da aka gani a gidansa.
Kalli Bidiyon abinda shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA yayi bayan da Morocco ta barar da Penalty da ya dauki hankula sosai

Kalli Bidiyon abinda shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA yayi bayan da Morocco ta barar da Penalty da ya dauki hankula sosai

Duk Labarai
An ga shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA da yaje kallon wasan karshe tsakanin kasar Morocco da Senegal ya ji ba dadi bayan da Morocco ta barar da bugun Penalty da aka bata. Da yawa abin ya basu mamaki inda wasu ke cewa ashe suma hukuma na daukar wani bangare da suka fi so. Wasu kuma sun yi zargin cewa bakake ne ba'ason su ci kofin. https://twitter.com/i/status/2013214153549263288
‘Yan Najeriya na nuna fushinsu bayan da aka ga shugaban hukumar tattara Haraji ta kasa da agogunan Naira Miliyan 90 data Naira Miliyan 150

‘Yan Najeriya na nuna fushinsu bayan da aka ga shugaban hukumar tattara Haraji ta kasa da agogunan Naira Miliyan 90 data Naira Miliyan 150

Duk Labarai
'Yan Najeriya na nuna fushinsu bayan zargin shugaban hukumar tattara Haraji ta kasa, Zach Adedeji ya saka agoguna masu tsada. Wasu hotunansa guda biyu sun bayyana inda aka ganshi sanye da agoguna kirar Patek Philippe daya farashin ta Naira Miliyan 91,898,970 inda kuma dayar farashinta Naira Miliyan 157,905,530. Saidai masu kareshi sun bayyana cewa dama can me kudi ne. Da yawa dai na cewa zasu biya haraji amma ba zasu lamunci a rika satar musu kudi ba. https://twitter.com/i/status/2013141601523060756 https://twitter.com/i/status/2012993406629273664
Kalli Bidiyon: Abinda dan Atiku, Abba Atiku da ya koma APC yace akan mahaifinsa ya baiwa mutane mamaki

Kalli Bidiyon: Abinda dan Atiku, Abba Atiku da ya koma APC yace akan mahaifinsa ya baiwa mutane mamaki

Duk Labarai
Dan Atiku Abubakar, Abba Atiku da ya koma jam'iyyar APC ya dauki hankula bayan jawabin daya gabatar na farko bayan komawarsa APC. An ga Bidiyon sa yana cewa, duk wani me goyon bayansa ko wanda suke karkashinsa su daina goyon mahaifinsa, Atiku Abubakar su koma goyon bayan shugaba Tinubu. https://twitter.com/i/status/2013136856678879496 Saidai wani abu na daban da ya kara daukar Hankula akan Abba Atiku shine yanda aka ga yana magana, baya iya tsayawa da kyau. Da yawa sun yi zargin cewa yana shaye-shaye.