Wednesday, March 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ƴànbìndìgà sun yi gàrkùwà da mata 25 a hanyar zuwa biki a Zamfara

Ƴànbìndìgà sun yi gàrkùwà da mata 25 a hanyar zuwa biki a Zamfara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, ƴan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mata 25 a garin Kurmi na ƙaramar hukumar Maru An ce dai an yi garkuwa da matan ne suna kan hanyar zuwa gidan bikin. Haka ma wasu ƴan bindigar sun yi garkuwa da aƙalla mutum 19 yayin da suka raunata ƙarin wasu da dama, a garin Galadi da ke ƙaramar hukumar Tsafe, duk dai a jihar ta Zamfara.
Kalli Bidiyon yanda Rarara ya kai matarsa ta gaishe da shugaban kasa, Tinubu

Kalli Bidiyon yanda Rarara ya kai matarsa ta gaishe da shugaban kasa, Tinubu

Duk Labarai
A yayin ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a daren ranar Juma'a, Tauraron mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara ya gabatarwa da shugaba Tinubu da matarsa, A'isha Humaira inda ta gaishe da shugaban kasar. https://twitter.com/abdullahayofel/status/1918552250688975253?t=ujjnjfaaHXn-GJEWleawMw&s=19 Shugaba Tinubu dai ya ji dadin wakar da Rarara ya masa sosai.
Kudin da ake zargin tsohon shugaban NNPCL da ma’aikatan sa da sacewa zasu iya fin wanda ake zargin tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Emefiele da sacewa>>EFCC

Kudin da ake zargin tsohon shugaban NNPCL da ma’aikatan sa da sacewa zasu iya fin wanda ake zargin tsohon shugaban babban bankin Najeriya, Emefiele da sacewa>>EFCC

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC zata fara binciken tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL watau Mele Kolo Kyari. Tare da kyari, akwai mutane 13 da suma za'a bincikesu wanda suka yi aiki tare dashi. Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa, Tuni aka kama wasu daga cikin tsaffin ma'aikatan sannan ana kan bin sahun sauran dan suma a kamasu. Majiyar tace sauran wadanda ake bincike tare da kyari sune: Abubakar Yar’Adua, Mele Kyari, Isiaka Abdulrazak, Umar Ajiya, Dikko Ahmed, Ibrahim Onoja, Ademoye Jelili, da Mustapha Sugungun. Sauran sune Kayode Adetokunbo, Efiok Akpan, Babatunde Bakare, Jimoh Olasunkanmi, Bello Kankaya da Desmond Inyama. Ana zargin dai Kolo Kyari da ma'aikatansa sun sace kudaden da aka ware dan gyaran matatun man ...
Da Duminsa: Kamar Yanda aka yi a jihar Rivers, Gwamnatin Tarayya na shirin saka dokar tabaci da dakatar da gwamnonin jihohin Zamfara da Benue

Da Duminsa: Kamar Yanda aka yi a jihar Rivers, Gwamnatin Tarayya na shirin saka dokar tabaci da dakatar da gwamnonin jihohin Zamfara da Benue

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya na shirin kakaba dokar ta baci da dakatar da gwamnonin jihohin Benue da Zamfara saboda matsalar tsaro. Tuni majalisar tarayya ta aikewa wadannan jihohi da majalisunsu wasikar gayyata kan su je su yi bayanin dalilin da zai hana kada a saka dokar tabaci a cikin jihohin nasu. Wata kungiyar kare hakkin bil'adama me suna Guardians of Democracy and Rule of Law ce ta aikewa majalisar tarayya da bukatar hakan. Kungiyar tace Gwamnonin wadannan jihohi sun kasa samar da tsaro ga al'ummarsu inda ta nemi majalisa ta kai dauki wadannan jihohin. Majalisar dai ta tabbatar da aikewa da wannan bukata.
Rarara Na cikin Alheri Dumu-Dumu: Kalli Bidiyon Abinda Shugaba Tinubu yayi bayan da ya saurari wakar da Rarara ya masa

Rarara Na cikin Alheri Dumu-Dumu: Kalli Bidiyon Abinda Shugaba Tinubu yayi bayan da ya saurari wakar da Rarara ya masa

Duk Labarai
Wakar da shahararren mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara yawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ziyarar da ya kai jihar Katsina ranar Juma'a ta dauki hankula sosai. A cikin wakar an ji Rarara yana hadawa hadda Yarbanci. A yayin da yake wakar, an ga Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna tafawa Rarara. https://www.tiktok.com/@mubeedabai/video/7499990461390572806?_t=ZM-8w2Z8lzNfFv&_r=1 https://twitter.com/AbbaM_Abiyos/status/1918528231256281299?t=67glgoHt45PaLFyb4oCNBw&s=19 Da yawa sun jinjinawa Rarara inda suka ce wakar ta yi dadi.
Kalli Bidiyo: Gwamnan Rivers da Tinubu ya dakatar, Fubara ya dawo Najeriya bayan kwashe makonni 2 yana hutu a kasashen waje

Kalli Bidiyo: Gwamnan Rivers da Tinubu ya dakatar, Fubara ya dawo Najeriya bayan kwashe makonni 2 yana hutu a kasashen waje

Duk Labarai
Dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara ya dawo gida Najeriya bayan makonni 2 yana hutawa a kasashen waje. Da misalin karfe 7 na yammacin Ranar Juma'a ne Fubara ya sauka a birnin Fatakwal na jihar Rivers. https://twitter.com/thecableng/status/1918543339411919205?t=TlaLrwl97IM1QzdRXmbpXA&s=19 Rahotanni sun bayyana cewa, yayi hutunne a kasar Jamus.