Gwamnatin Kano na neman a kama Ganduje, saboda yunkurin kafa kungiyar tsaro ta sa kai
Majalisar zartaswar jihar Kano ta yi kira da a gaggauta gudanar da bincike tare da kama tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa wasu kalamai da ta bayyana a matsayin tsokana da kuma tada zaune tsaye kan matsalar tsaro a jihar.
Hakan ya biyo bayan tattaunawa ne a taron majalisar zartarwa karo na 34 da aka gudanar a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar Kano, inda ƴan majalisar suka yi nazari kan kalaman Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin na baya-bayan nan, inda suka yi zargin cewa Kano na kara fuskantar matsalar ƴan fashi da kuma bayyana shirin ɗaukar mutane 12,000 aikin ƴan sandan rundunar tsaro mai suna Khairul Nas.
Da yake yiwa manema labarai ƙarin haske game da sakamakon taron a ranar Juma’a, kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim...








