Da Duminsa: Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon babban lauyan Gwamnati, Abubakar Malami
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC ta gayyaci tsohon babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami.
Malami ne da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta.
Ya kuma tabbatar da cewa, zai amsa wannan gayyatar saboda ya yadda da bincike kuma shi dan kasa ne me bin doka.








