Tuesday, June 30
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Ma’aikata a ma’aikatar kudi sun saka hoton Ministan kudi da shugaba Tinubu ya kora daga aiki, Wale Edun a jikin akwatin gawa yayin da suke murnar sukeshi daga mukamin

Kalli Bidiyon: Ma’aikata a ma’aikatar kudi sun saka hoton Ministan kudi da shugaba Tinubu ya kora daga aiki, Wale Edun a jikin akwatin gawa yayin da suke murnar sukeshi daga mukamin

Duk Labarai
Ma'aikata a ma'aikatar kudi ta tarayya sun saka hoton Ministan kudi, Wale Edun da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sallama daga aiki a jikin Gawa suna Murnar sallamarsa daga aiki. An ga yanda ma'aikatan ke bi suna rijistar wai sun je jana'aizarsa. Lamarin ya dauki hankula sosai inda ake ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. https://twitter.com/i/status/2046714720854425751
Da Duminsa: Dangote zai fara yin Omo da Sabulun wanki da kuma Robobi

Da Duminsa: Dangote zai fara yin Omo da Sabulun wanki da kuma Robobi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Attajirin Najeriya Aliko Dangote zai fara yin Robobi da Omo da sabulun wanki. Dangote zai fara hakanne a matatar man fetur dinsa dake Lekki Lagos inda ya hada kai da kamfanin Honeywell. Matatar ta Dangote tana samar da sinadaran samar da sabulu da omon wanki da kuma robobi. Hakanan ba a Najeriya kadai zai rika sayar dasu ba hadda kasashen Duniya Wannan sabon kamfani nasa rahotanni sun ce idan ya tabbata zai zama mafi girma irinsa a fadin Duniya.
Farashin Dala a kasuwar Chanji ta yau

Farashin Dala a kasuwar Chanji ta yau

Duk Labarai
Farashin dala a kasuwar Chanji ta Gwamnati a yau, Laraba, 22 ga watan Afrilu ya kai Naira 1,348.77 NGN akan kowace dala. Farashin ya dan sauka zuwa Naira 1,346.30 NGN kamin daga baya ya sakw hawa. A kasuwar bayan fage kuwa ta garuruwan Abuja, Legas da Kano, Farashin dalar ya kai Naira 1,450 NGN zuwa naira 1,470 NGN akan kowace dala.
Kalli Bidiyon: Hudubar Adam A. Zango ta yi aiki a kaina, daga yau na daina nuna matata a kafafen sada zumunta>>Inji Gfresh Al-amin bayan daya kalli sabon fim din Adam A. Zango

Kalli Bidiyon: Hudubar Adam A. Zango ta yi aiki a kaina, daga yau na daina nuna matata a kafafen sada zumunta>>Inji Gfresh Al-amin bayan daya kalli sabon fim din Adam A. Zango

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin yace Hudubar Adam A. Zango ta yi aiki akansa inda yace shima daga yau ya daina tallar matarsa a kafafen sada zumunta. Yace duka abokansa na da mata amma babu wanda yake ganin matansa sai shi sakarai ake ganin matarsa. Yace ya hau shafinta na Tiktok ya goge Bidiyon data dora sannan wanda take friends dasu ma ya gogesu. https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7631339680214076680?_r=1&_t=ZS-95kERbNKtg9
Kalli Bidiyon: Gwamnati ta fara bin gidaje masu Amfani da Sola tana bukatar a biya Harajin Amfani da sola

Kalli Bidiyon: Gwamnati ta fara bin gidaje masu Amfani da Sola tana bukatar a biya Harajin Amfani da sola

Duk Labarai
A yayin da matsalar rashin wutar Lantarki ta damu Al'ummar Najeriya, suka koma amfani da Solar. Wani sabon salo shine da aka ga jami'an gwamnati sun fara bi gidaje dake amfani da Solar suna cewa, a basu harajin Amfani da Solar. Lamarin ya fara a Legas ne inda wani Magidanci yace ba zai biya ba bayan da aka rutsashi aka ce wai sai ya biya Harajin saka Solar. Bidiyon faruwar lamarin ya karade kafafen sadarwa inda ake ta cece-kuce akai. https://twitter.com/i/status/2046706370271981996
Mun Rabu da matatane saboda ita kullun take son a rika yi kuma sau biyu ya mata kadan>>Inji Roby Ekpo

Mun Rabu da matatane saboda ita kullun take son a rika yi kuma sau biyu ya mata kadan>>Inji Roby Ekpo

Duk Labarai
Shahararren ma'aikacin gidan rediyo daga kudancin Najeriya,Roby Ekpo ya bayyana cewa dalilin da yasa suka rabu da matarsa shine baya iya biya mata bukatar aure. Yace shi ba yaro bane, yayi aure yana da shekaru 37. Yace matarsa amma kullun take son su rika kwanciyar aure. Yace amma shi ba zai iya ba inda yace saidai sau biyu a sati amma taki amincewa da hakan. Yace dole saidai rabuwa suka yi
Kalli Bidiyon: Ashe Ministan Kudi, Wale Edun, Karyata shugaba Tinubu yayi shiyasa aka saukeshi

Kalli Bidiyon: Ashe Ministan Kudi, Wale Edun, Karyata shugaba Tinubu yayi shiyasa aka saukeshi

Duk Labarai
A dazune dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauke ministan kudi, Wale Edun daga mukaminsa. Gwamnati dai bata bayyana dalilin sauke shi daga mukamin nasa ba a hukumance. Lamarin ya zowa mutane da mamaki duk da yake cewa a kwanakin baya an yi ta rade-radin cewa, Ministan yayi fama da rashin lafiya. Saidai a yanzu a kafafen sada zumunta, ana ta yada wani Bidiyo daya nuna shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana cewa sun cimma yawan kudin shiga da suke nema a shekarar 2025. Saidai a wani Bidiyo daban kuma, an ga Ministan kudin, Wale Edun na cewa Tiriliyan 40 suke nema a shekarar 2025 amma kudin shiga Tiriliyan 10 kacal suke tsammani. Wannan magana ta ci karo data shugaban kasa, wadda wannan yasa wasu ke ta hasashen cewa, dalili kenan da yasa...