Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Nifa a wajena Musulmai da Kiristoci Shedan suke Bautawa>>Inji Ibrahim El-Rufai

Nifa a wajena Musulmai da Kiristoci Shedan suke Bautawa>>Inji Ibrahim El-Rufai

Duk Labarai
Dan gidan Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, watau Ibrahim El-Rufai ya bayyana cewa shi a wajansa, Musulmai da Kiristoci shedan suke bautawa. Ya bayyana hakane a cikin Bidiyon sa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda ya bayyana cewa shi bai yadda da Allah ba. Ya kuma zargi mutanen Arewa da aurar da mata da wuri inda yace abin na ci masa tuwo a kwarya. https://twitter.com/Nawas_masood/status/1993329847247032719?t=XVxpLZEtxV4Sx23UlFcCpw&s=19
Wai Me ya farune: Yaya aka yi, Ban ji an kama kowa ba, Ban ji an kira sunan kowa ba, Tattaunawa aka yi, ko kuwa kawai dawowa gida suka yi? Dan Sarkin Kano, Adam Lamido Sanusi ya tambaya kan Daliban jihar Kebbi

Dan gidan me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II me suna Adam Lamido Sanusi na tambayar shin me ya faru game da kubutar da daliban jihar Kebbi? Ya tambayi cewa shin Sulhu aka yi, bai ji an kama kowa ba sannan bai ji an kira sunan kowa ko kuwa yaran kawai dawowa suka yi da kansu? A jiya ne dai gwamnati ta sanar da Kubutar da dalibai 24 na makarantar MAGA dake jihar Kebbi da aka yi garkuwa dasu. https://twitter.com/Adam_L_Sanusi/status/1993382979180368121?t=ILXFfPx0rdCFBFEzRRt6RQ&s=19
Kalli Bidiyon Gwanin Ban Tausai yanda Tshàgyèràn masu neman kafa Qàsàr Bìàfrà sùkà Hàllàqà Sojan Najeriya suka kuma Wùlàqàntà gàwàrsà akan Titi

Kalli Bidiyon Gwanin Ban Tausai yanda Tshàgyèràn masu neman kafa Qàsàr Bìàfrà sùkà Hàllàqà Sojan Najeriya suka kuma Wùlàqàntà gàwàrsà akan Titi

Duk Labarai
Wasu da ake zargin 'yan Kungiyar ÌPÒB ne masu son kafa kasar Biafra a birnin Aba na jihar Abia, sun hallaka wani sojan Najeriya me suna David. Sun hallaka sojan ne yayin da ya dauki hutu ya je gidan mahaifinsa dan ya gana dasu. Sun hallakashi ne biyo bayan yankewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai da kotu tayi. Hukumar sojojin Najeriya ta baiwa sojoji shawarar su rika kula da mutanen da suke tare dasu sannan idan ba a kungiyance suke ba, su daina saka kayan aiki su rika saka kayan gida. Danna Nan dan kallon Bidiyon https://twitter.com/Nnamdi14108597/status/1993096998380073107?t=aEq6pn2TdOUQ5V92h1_65w&s=19
Kalli Bidiyon Yanda Hàrsàsàì suka fado daga cikin wata Mota data je wucewa ta kofar jami’ar ABU Zaria

Kalli Bidiyon Yanda Hàrsàsàì suka fado daga cikin wata Mota data je wucewa ta kofar jami’ar ABU Zaria

Duk Labarai
Rahotanni daga garin Zaria, Jihar Kaduna na cewa, Harsasai sun fado daga cikin wata mota da ta je wucewa ta kofar jami'ar ABU dake garin. Saidai kamin a ankara motar ta tsere. An ga yanda mutane suka rika tattara harsasan dake zube a kan titi bayan tserewar motar. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1993595283163296074?t=VnHyYZBpBXKh1XXSyu2KOQ&s=19
Ni fa nafi damuwa da Tshàgyèràn Dhàjì fiye da mutanen da suke Dàukà>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Ni fa nafi damuwa da Tshàgyèràn Dhàjì fiye da mutanen da suke Dàukà>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, yafi damuwa da Tshàgyèràn Dhàjì fiye da mutanen da suke yin Garkuwa da su. Malam ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace kamar a Asibiti ne idan aka kawo mutum na zubar da jini, ana fara tsayar da jinin ne farko kamin a fara gyaran ciwo ko dinki. Malam yace misali Mahaukaci ne a kasuwa ya cakawa mutane da yawa wuka, kamata yayi a fara kwace wukar dake hannunsa kamin a fara kula wadanda ya cakawa wukar. Yace bawai bai damu da wadanda lamarin 'yan Bindigar ke shafa ba, abinda yake magana akai shine a fara dakatar da zubar da jinin tukunna.
Kalli Bidiyon: Gwamnati ta kàsà kàrbàr daliban Kebbi daga hannun mu ta Qarfi, sai dai Sulhu aka yi muka badasu>>Inji Tshàgyèràn Dhàjì

Kalli Bidiyon: Gwamnati ta kàsà kàrbàr daliban Kebbi daga hannun mu ta Qarfi, sai dai Sulhu aka yi muka badasu>>Inji Tshàgyèràn Dhàjì

Duk Labarai
'Yan Bìndìgà da suka yi garkuwa da daliban makarantar MAGA dake jihar Kebbi sun bugi Qirji cewa Gwamnati ta kasa karbar dalibai ta Qarfi sai Sulhu aka yi suka bayar da daliban. A Bidiyon da suka saki, an jisu suna tambayar daliban shin Jiragen sama nawa suka ji sun wuce ta saman su suka ce basu san iyaka ba. Sannan sun tambayi daliban cewa, ko an tabasu ko an ci zarafinsu? Suka ce a'a. https://twitter.com/AM_Saleeeem/status/1993429655479566738?t=ADbi262pk3LD7RWtFJBNUQ&s=19
Kalli Bidiyon: Naga matata dana saki Maryam maza sun baibayeta wai zasu aureta, amma ni nasan Ummaruntane kawa zai sha Dùkà su watse su barta>>Inji Gfresh

Kalli Bidiyon: Naga matata dana saki Maryam maza sun baibayeta wai zasu aureta, amma ni nasan Ummaruntane kawa zai sha Dùkà su watse su barta>>Inji Gfresh

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, yaga masa sun baibaye Matarsa daya saka watau Maryam. Yace suna mata Qaryar wai zasu aureta. Yace amma shi yasan Ummaruntane kawai za sha duka su watse su barta. Dana nan dan kallon Bidiyon Gfresh dai ya saki matarsa, Maryam ne bayan da fada ya kaure tsakaninsu kan zuwansa gidan tsohuwar matarsa, Safiya Haruna.
Fatana shine a Samu Wani Minista ya aureni, Shi kuma Gfresh Baqin ciki ya hàllàqàshì>>Inji Tsohuwar Matar Gfresh, Maryam

Fatana shine a Samu Wani Minista ya aureni, Shi kuma Gfresh Baqin ciki ya hàllàqàshì>>Inji Tsohuwar Matar Gfresh, Maryam

Duk Labarai
Tsohuwar matar Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin wadda ya saka kwanannan, watau Maryam ta yi fatan a samu wani Minista ya aureta shi kuma Gfresh Al-amin Baqin ciki ya Hallaqashi. Ta wallafa hakanne a shafinta na Tiktok. Wani ne ya mata comment din hakan inda saboda jin dadi da amincewa da comment din ta hadashi da hotonta ta dora a shafinta. Kalli Bidiyon anan https://hutudole.com/fatana-shine-a-samu-wani-minista-ya-aureni-shi-kuma-gfresh-baqin-ciki-ya-hallaqashiinji-tsohuwar-matar-gfresh-maryam/