Thursday, February 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ya kamata a hukunta Alkalin da yace sake nada Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba daidai bane>>Inji El-Rufai

Ya kamata a hukunta Alkalin da yace sake nada Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba daidai bane>>Inji El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bukaci cewa ya kamata a hukunta Alkalin babbar kotu tarayya da yayi hukuncin cewa sake nada me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin sarki baya kan ka'ida. El-Rufai wanda abokin Sarki Sanusi II ne ya bayyana hakane a ta shafinsa na sada zumunta inda yake taya Sanusi II murnar tabbatar dashi a matsayin sarkin Kano da kotun daukaka kara tayi. A baya dai Kotun tarayya ta yi hukuncin cewa, sake nada Sarki Sanusi II baya kan doka amma a yanzu kotun daukaka kara ta soke wancan hukunci. El-Rufai ya kara da cewa, babbar kotun tarayya bata da hurumin shiga maganar masarauta wadda bata cikin garin Abuja. An ga dai yanda masoya sarki Sanusi II suka barke da murna bayan da aka tabbatar dashi a matsayin sarkin Kanon.
Gwamnatin tarayya ta bayyana sanda zata sake yiwa ma’aikata karin albashi

Gwamnatin tarayya ta bayyana sanda zata sake yiwa ma’aikata karin albashi

Duk Labarai
Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta bayyana sanda gwammati zata sake yiwa ma'aikata karin albashi. Ta bayyana hakane ranar Alhamis a ziyarar da ta kai jihar Abia. Tace a baya sai bayan shekaru 5 ne ake karawa ma'aikata Albashi amma a yanzu, za'a rika yin karin albashinne duk bayan shekaru 3. Tace nan da kasa da shekaru 2 za'a sake yiwa ma'aikatan karin Albashi.
Gwamnatin tarayya tace zata saka karuwanci cikin hanyar samun kudin dake karawa tattalin arzikin Najeriya karfi

Gwamnatin tarayya tace zata saka karuwanci cikin hanyar samun kudin dake karawa tattalin arzikin Najeriya karfi

Duk Labarai
Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa zata saka karuwanci a matsayin daya daga cikin alkaluman da take amfani dasu wajan tantance karfin tattalin arzikin Najeriya Hakanan bayan karuwancin, za'a kuma saka harkar kwaya a cikin hanyoyin da ake samarwa gwamnati kudi da kara karfin tattalin arziki. Shugaban hukumar, Dr. Baba Madu ne ya tabbatar da hakan i da yace akwai kasashen da kwaya ce babbar hanyar samun kudin shigarsu sannan akwai wanda kuma ke karuwanci kuma suna samun kudi fiye ma da masu aikin yi. Yace duka wadannan za'a sakasu a cikin masu taimakawa karfin tattalin arzikin Najeriya.
Mace me zaman kanta ta Kkashe me sayar da giya a jihar Adamawa

Mace me zaman kanta ta Kkashe me sayar da giya a jihar Adamawa

Duk Labarai
Wata mata me zaman kanta a jihar Adama ta kashe me sayar da giya bayan da rikici ya barke a tsakaninsu akan canjin Naira 200. Matar me suna Riyanatu Musa ta kashe Yohanna Musa ne ta hanyar caka masa wuka a kirji. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargi ta amsa laifin da ake zarginta dashi. Tace a lokacin data kashe Yohanna Musa bata cikin maye inda tace amma ta yi nadamar abinda ta aikata. Kakakin 'yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje yace kwamishinan 'yansandan jihar, Morris Dankombo ya bayar da umarnin yin bincike kan lamarin.

Sunayen mata kyawawa

Sunaye
Ga sunayen mata kyawawa kamar haka: Fatima. Nafisa. Bilkisu Halima. Shamsiyya. Shafa'atu. Raliya. Ramlatu. Rukayya. Zahara. Sahara. Maryam. Maimuna. Mufeeda. Khadija. Fadila. Fiddausi. Hafsa. Faiza. Salamatu. Rufaida. Saratu. Safiya. Farida. Amira. A'isha. Habiba. Suwaiba. Amina. Hannatu. Hafiza. Rahama. Hassana. Usaina. Lubna. Rasheda Karima. Lubabatu Zainab. Jidda Ummukhulsum. Naja'atu. Sultana. Fauziyya. Nawwara. Sa'adatu. Yasmin. Atika. Nabila Sakina. Salima Sumayya. Sulaim. Saudat. Hanifa. Jamila. Khausar. Umaima. Widad. Nasreen. Afifa. Juwairiyya. Basma Ummi Momi Umma. Hauwa. Iftihar...
Kotun Ɗaukaka ƙara ta yi watsi da umarnin kotun taraiya na soke dawo da Sarki Sanusi

Kotun Ɗaukaka ƙara ta yi watsi da umarnin kotun taraiya na soke dawo da Sarki Sanusi

Duk Labarai
Kotun daukaka kara ta Kano a yau Juma’a, ta yi watsi da umarnin babbar kotun da ta soke nadin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16. Wani kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara, a hukuncin da ta yanke, karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Mustapha, ya yi watsi da hukuncin da kotun tarayya ta yanke a ranar 20 ga watan Yuni, 2024, ƙarƙashin mai shari’a Abubakar Liman, na babbar kotun tarayya, wanda ya soke dokar masarautar Kano ta 2024 da ta sake nada Sanusi. A cewar kotun daukaka kara, Mai shari’a Liman ya yi watsi da hurumin soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka bisa dokar majalisar masarautu ta 2024. Ta kara da cewa, karar da wani basarake a jihar, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar, wanda alkalin babbar kotun ya dogara da ita wajen bayar da wanna...
Gwamnan Akwa Ibom ya kori gaba ɗaya kwamishinonin sa

Gwamnan Akwa Ibom ya kori gaba ɗaya kwamishinonin sa

Duk Labarai
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya sallami gaba ɗaya kwamishinonin jihar, inda ya ce ya na so ne ya kawo sabon-jini. A jawabin a yayin taron sallama da kwamishinonin a gidan gwamnati, Eno ya ce dukkan su babu wanda bai yi kokari a muƙamin da aka bashi ba. Sai dai ya ce duk da ko wanne daga cikin kwamishinonin ya yi kokari a ma'aikatar sa, akwai buƙatar a kawo wasu sabbin kwararru domin ci gaban jihar.
Mu na fama da matsanancin ƙarancin ma’aikata – NAFDAC

Mu na fama da matsanancin ƙarancin ma’aikata – NAFDAC

Duk Labarai
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC, ta koka kan matsanancin ƙarancin ma'aikata. Da ta ke ganawa da manema labarai a Legas a jiya Alhamis, shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ta baiyana cewa a yanzu haka hukumar na da ma'aikata dubu 2 kacal a fadin ƙasar, inda ta ce hakan adadi ne mai matuƙar kankanta duba da irin aikin hukumar. Ta yi kira da a ninka adadin ma'aikatan hukumar sau biyu ko sau uku, inda ta ce aikin da su ke yi na kare lafiyar al'ummar ƙasa baki daya na buƙatar wadatuwar ma'aikata don a samu sakamako mai kyau.
Ɗan bayan Liverpool Kuma dan ƙasar Netherlands, Virgil Van Dijk ya rattaba hannu a tsawaita kwantaragi na shekaru 2 a ƙungiyar

Ɗan bayan Liverpool Kuma dan ƙasar Netherlands, Virgil Van Dijk ya rattaba hannu a tsawaita kwantaragi na shekaru 2 a ƙungiyar

Duk Labarai
Ɗan bayan Liverpool Kuma dan ƙasar Netherlands, Virgil Van Dijk ya rattaba hannu a tsawaita kwantaragi na shekaru 2 a ƙungiyar. Hakan na zuwa ne yayin da rahotanni daga Transfer News Live ke nuni da cewa Luiz Diaz ya ƙi karɓar tayin tsawaita kwantaragi daga Liverpool, inda shi hankalin sa ya yi kan Barcelona.