Rashin kunyarta da rashin bin dokar majalisa ce tasa muka dakatar da ita ba zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio ba>>Majalisar Dattijai ta mayarwa da majalisar Dinkin Duniya martani kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti
Majalisar Dattijai ta mayarwa da taron mata 'yan majalisa na Duniya dake gudana a majalisar Dinkin Duniya dake New York City na kasar Amurka martani kan dakatar da sanata Natasha Akpoti.
Sanata Natasha Akpoti da majalisar dattijai ta dakatar ta halarci taron inda ta gabatar da korafin dakatar da ita da aka yi, duk da majalisar tace mata ba abinda ya tarasu a wajan kenan ba amma ta sha alwashin ji daga bakin majalisar dattijai ta Najeriya kamin daukar mataki.
A martanin majalisar dattijai ta Najeriya wanda shugaban majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ya aikewa majalisar Dinkin Duniya kuma 'yar majalisar wakilai dake halartar taron, wadda kuma itace shugabar kwamitin kula da harkokin mata da jin dadi na majalisar watau, Honorable Kafilat Ogbara ta karanto ta kishi cewa.
Muna sanar ...








