Attajirin Duniya, Elon Musk ya zama na farko a Duniya da Darajar kudinsa ta haura Dala Biliyan $600
A yanzu, Jaridar Forbes ta bayyana cewa kudinsa sun kai dala Biliyan $677.
Hakan ya farune biyo bayan hauhawar darajar kamfaninsa na SpaceX
Dan wasan barkwanci, Sale Naci ya bayyana cewa yasan abinda yake yi Haramun ne amma ba zai taba dainawa ba.
Yace hakane bayan da wani Boka yace zai bashi tallar bokancin da yake ya tayashi tallatawa zai biyashi daga Miliyan 10 zuwa sama.
Saidai Sale Yace ba zai karbi wannan tallar ba.
https://www.tiktok.com/@sulenaci_/video/7584114589726559496?_t=ZS-92GY12TS1s9&_r=1
Tauraron mawakin Hausa Rarara da aka yiwa nadin Sarautar Sarkin Wakar Qasar Hausa ya dauki hankula sosai saboda nadin rawanin da aka masa
An ga Rarara zaune da nadin da aka masa wanda ya jawo cece-kuce sosai.
https://www.tiktok.com/@m.shafiu.mai.rapi/video/7583807564345888007?_t=ZS-92GWziQup2P&_r=1
Wani yayi ikirarin hango Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa tana Tafiya a kasa da dare.
Yace wai GLK dinta babu mai ne.
Samha M. Inuwa na daga cikin jaruman fina-finan Hausa da suka dauki hankula bayan da suka sayi Motar GLK.
https://www.tiktok.com/@amb00121/video/7584168595329142038?_t=ZS-92GVLUN4Uwz&_r=1
Wannan wani Ladani ne da ya nuna Makogoronsa a yayin da yake Alhinin rasuwar Ladanin Hotoro wanda aka cirewa Makogoro.
Ladanin ya baiwa 'yan uwansa Ladanai shawarar su rika shiga Masallaci da makami yayin da suka je kiran Sallah.
Hakanan kuma ya Yace Ladanai su rika kulle kofofin Masallaci yayin da suke kiran Salah.
https://www.tiktok.com/@shugaba_tv1/video/7584208558418398485?_t=ZS-92GRMDQt7Vg&_r=1
Wannan shine hoton wanda ake zargin ya yanke Maqogoron Ladani a masallacin Hotoro dake Kano.
Rahotanni sun ce tuni mutane shima suka taru suka shèkyèshi kuma an je an kona gidansu.
Hakaan Rahotanni sun ce ba dan Najeriya bane dan kasar Chadi ne chirani suka zo Najeriya.
https://www.tiktok.com/@abis_fulani/video/7584218871389850902?_t=ZS-92GOLK0HB6u&_r=1
https://www.tiktok.com/@harun.shalele/photo/7584172216699325716?_r=1&_t=ZS-92GPCHgIKDh
https://www.tiktok.com/@muhammadyahaya573/video/7584036450144898322?_t=ZS-92GPJOifNKL&_r=1
Wannan wata Kirista ce data Musulunta, ta bayyana cewa abu na farko daya fara jan hankalinta kan Addinin Musulunci shine yanda ta fahimci cewa musulmai sun yadda da Annabi Isa (AS).
Tace ta ci gaba da bincike inda daga baya ta gano cewa, Jesus yayi Sallah amma gashi Kiristoci basa yi.
Tace dan haka ne yasa ta Musulunta.
https://twitter.com/A_Y_Rafindadi/status/2000553931500585139?t=yhb2-45JaS_e3ksy0AVWew&s=19
Matar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewa, marigayi mijin nata ya amince da cewa tana son kasheshi.
Tace an rika yada rade-radin cewa, tana son ta kashe Mijin nata a fadar shugaban kasar inda tace har ta kai ga Buharin ya fara yadda da abinda mutanen ke cewa.
Tace Buhari ya canja mata kwata-kwata ya rika kulle kofa da sauransu.
Tace rashin lafiyar da yayi na da alaka da canjin abinci da rashin samun abinci me gina jiki.
Tace amma da aka kaishi kasar waje ya samu sauki.
Tace babu gaskiya a maganar cewa, guba ce aka sawa Buharin.
Rahotanni sun bayyana cewa, Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio na can asibiti a birnin landan inda yake jinya.
Hutudole ya ruwaito muku jiya cewa, Akpabio ya yanke jiki ya fadi ne inda Sabbin Rahotannin da muka sau suka ce Dangote ya bayar da jirgi aka tafi dashi Landan inda yake jinya.
Kuma mun samu cewa Lamarin ya farune ranar 10 ga watan Disamba, kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.
Hutudole ya fahimci cewa, Likitoci sun ce Aiki ne yawa Akpabio yawa shiyasa wannan lamari ya sameshi, da haka suke bashi shawarar ya ajiye aiki ya koma ya kula da lafiyarsa.
Akpabio dai an ganshi a karshe a zauren majalisar tun ranar da majalisar ta amincewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika da sojoji kasar Benin Republic.
Wani malami ya bayyana cewa 'yan Dariqar Tijjaniyya basu da banbanci da Yahudawa.
Malamin ya bayyana cewa akwai a rubuce-rubucen litattafan dariga da suke inkarin wasu abubuwan addini dan haka yace basu da banbanci da Yahudawa.
https://www.tiktok.com/@sarkinyakinsunnah_/video/7583741478225169685?_t=ZS-92FoZrXahcX&_r=1