Thursday, March 12
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Hotuna: Sojan Najeriya ya ajiye aiki bayan shekaru 11, Ji abinda ya fada

Hotuna: Sojan Najeriya ya ajiye aiki bayan shekaru 11, Ji abinda ya fada

Duk Labarai
Wani Sojan Najeriya ya ajiye aiki bayan shekaru 11 yana aikin na Soja. Ya bayyana cewa, yana alfahari da aikin kuma bai yi nadamar bari ba. https://twitter.com/optama/status/1851985467274858662?t=8XTyq468UB9TAtyQ3wZ1Kg&s=19 Sojan dai ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa kuma ya yadda da amincewa da shugabancin hukumar soja ta Najeriya sannan yana jinjinawa sojojin dake ci gaba da bayar da rayuwarsu dan gina kasa. Saidai ya bayyana cewa shi zai canja sana'a ne shiyasa ya dauki wannan mataki.
Bidiyo: Ji yanda Hadiza Gabon ta kutuntuma zagi bayan da wasu suka gaya mata ba daidai ba

Bidiyo: Ji yanda Hadiza Gabon ta kutuntuma zagi bayan da wasu suka gaya mata ba daidai ba

Hadiza Gabon
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta mayar da raddi ta hanyar zagi bayan da wasu suka rika tsokanarta ta hanyar yi mata ba'a da jikinta. Hadiza dai ta saka wani gajeren Bidiyo ne a shafinta na Instagram inda mabiyanta da yawa suka yaba. Kalli bidiyon anan Saidai an samu wasu da suka rika mata ba'a da jikinta. Wata me suna Sadeeka Musa ta bayyanawa Hadiza Gabon cewa, "Inata neman nonuwanki ban gani ba ko ina yaje oho" Hadiza Dai ta mata martanin cewa "Uwarki na bama tafi bukatarsu" ...
Kuma Dai: An sake kama dan daudu Bobrisky, Kalli Bidiyon yanda aka fizgoshi daga kan jirgin sama har ya ji ciwo

Kuma Dai: An sake kama dan daudu Bobrisky, Kalli Bidiyon yanda aka fizgoshi daga kan jirgin sama har ya ji ciwo

Duk Labarai
Hukumar shige da fici ta kasa ta kama dan daudu, Bobrisky a yayin da yake shirin barin Najeriya. An kamashine a filin jirgin sama a yayin da yake shirin hawa jirgin sama na KLM zuwa Amsterdam. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1852245396766052779?t=NIQaQ-Puh5zHf0gC6Qml5Q&s=19 Ya bayyana cewa an ji masa ciwo yayin kamen sannan ya zargi cewa hukumar EFCC ce ke da hannu wajan kamun nasa. Hakanan an ga Bidiyon yanda aka janyoshi daga kan jirgin da karfin tsiya zuwa waje inda da yawa ke tambayar yaya aka yi ya wuce jami'an tsaro ba tare da ganeshi ba. Wasu dai sun soki yanda aka kamashi inda suke tambayar laifin me ya aikata inda wasu ke cewa an yi daidai kamun da aka masa.
Hotuna: Zaman Budurwa akan cinyar mahaifinta ya jawo cece-kuce

Hotuna: Zaman Budurwa akan cinyar mahaifinta ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wata budurwa data zauna akan cinyar mahaifinta ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta. An ga budurwar da shigar banza inda ta zauna akan cinyar mahaifinta tana masa murnar zagayowar ranar haihuwarsa. Saidai da yawa sun yi Allah wadai da abinda ta aikata inda suka ce bai dace ba. https://twitter.com/LeratorMm/status/1851586213536206995?t=G0rrfEtWALv255NKgdxzng&s=19 Da yawa dai sun bayyana abinda budurwar ta aikata a matsayin rashin da'a.
Ba zamu yadda a saka shari’ar Musulunci a cikin tsarin kudin mulkin Najeriya ba>>Inji Lauya Kola Alapinni

Ba zamu yadda a saka shari’ar Musulunci a cikin tsarin kudin mulkin Najeriya ba>>Inji Lauya Kola Alapinni

Duk Labarai
Lauya Kola Alapinni ya aikewa da ofishin kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio cewa basu amince da saka shari'ar Musulunci cikin kudin tsarin mulkin Najeriya ba. Yayi hakan ne bayan kudirin dokar da dan majalisa Aliyu Bappa Misau ya gabatar a gaban majalisar cewa ya kamata a saka shari'ar Musulunci a tsarin kasuwanci da kwangila da sauransu. An yi muhawara sosai a farfajiyar majalisar kan lamarin inda hakan ya jawo cece-kuce. Lauyan ya kawo misali da cewa a kwanakin baya an rika kisa da kama wasu da suke aikata abubuwan da suka sabawa shari'ar Musulunci a Arewa inda yace su a kudu ba zasu akince da hakan ba.
Kuma Dai: An kara kara farashin Man Fetur

Kuma Dai: An kara kara farashin Man Fetur

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da 'yan kasuwar man fetur ke shirin fara dauko mai daga matatar man fetur ta Dangote gidajen man fetur da yawa sun kara farashin litar man. Hakan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta amince 'yan kasuwar su dauki man fetur kai tsaye daga matatar man fetur ta Dangote ba tare da dillancin kamfanin man fetur na kasa NNPCL ba. Wasu gidajen man fetur din sun mayar da farashin litarsu zuwa Naira 1,250 inda wasu kuma suka mayar da farashin zuwa 1,300. Wasu na sayarwa akan farashin 1,150 inda wasu ke sayarwa akan farashin 1230. Majiyar Hutudole ta yi hira da wasu masu ababen hawa da suke shan man fetur inda suka rika bayyana rashin jin dadinsu akan lamarin hauhawar farashin man fetur din a kusan duk kwanaki kalilan. Cire tallafin man fetur dai na...
Yabon Tinubu ya kamata a yi game da cire tallafin man fetur ba zagi ba saboda sauran shuwagabanni Najeriyakasa cirewa suka yi amma shi ya cire>>Inji Hadiminsa, Sunday Dare

Yabon Tinubu ya kamata a yi game da cire tallafin man fetur ba zagi ba saboda sauran shuwagabanni Najeriyakasa cirewa suka yi amma shi ya cire>>Inji Hadiminsa, Sunday Dare

Duk Labarai
Hadimin shugaban kasa dake bashi shawara akan harkar sadarwa da wayar da kan al'umma, Sunday Dare ya bayyana cewa kamata yayi a yabi shugaban kasar, Bola Ahmad Tinubu akan cire tallafin man fetur. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV inda yace shuwagabannin kasashe da aka yi a baya da yawa sun kasa cirewa sai shine yayi namijin kokari ya cire tallafin man fetur din sannan ya kuma cire tallafin dala. Yace wasu kalilan ne a kasarnan ke samu makudan kudade da tallafin wanda ke sa gwamnati na tafka mummunar asara. Cire tallafin dai ya sanya farashin man fetur ya tashi daga sama da Naira 200 akan kowace lita zuwa sama da Naira 1000 akan kowace lita kuma man fetur ne hanyar da 'yan Najeriya ke amfani da ita wajan samun makamashi a gidajensu da w...
Mun baiwa ‘yan Najeriya Miliyan 24 tallafi>>Inji Gwamnatin tarayya

Mun baiwa ‘yan Najeriya Miliyan 24 tallafi>>Inji Gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da baiwa 'yan Najeriya miliyan 24 tallafi daban daban da suka hada dana bashi dana koya sana'a da dai sauransu. Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai. Ya kara da cewa tallafin da suka bayar sun hada da bangaren Noma, Makamashi, masana'antu kiwon lafiya da dai sauransu. Hakan na zuwane a yayin da 'yan Najeriya ke ta fama da kokawa da matsin tattalin arziki wanda yasa kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi.
Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana baiwa masu boye da dalar Amurka a gidaje su fito da ita su kai banki wata tara. Gwamnatin tace idandai kudaden na halas ne ba na sata ba ko zamba cikin aminci ba,babu wani hukunci da za'a wa mutum idan ya fito dasu. Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka inda ya zargi cewa masu boye dalar na taimakawa wajan kara karancinta da tsadarta a Najeriya.
NAFDAC ta yi gargadin daina Amfani da wani turaren Nivea Roll-On saboda illarsa

NAFDAC ta yi gargadin daina Amfani da wani turaren Nivea Roll-On saboda illarsa

Duk Labarai
Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta yo gargadin daina amfani da wani kalar Turaren Nivea Roll-on saboda illar da yake dauke da ita. Kalar turaren da ta ja kunne kan amfani dashi shine Nivea Black & White Invisible Roll-on deodorant saboda yana dauke da wani sinadari da aka haramta amfani dashi a cikin turaruka. Tuni kungiyar Kasashen Turai ta EU ta fitar da sanarwa akan daina amfani da wannan turare inda tace duk ma wadanda suka sayeshi su mayar dashi ga kamfanin. Shi wannan sinadari dai na taba lafiyar haihuwar masu amfani dashi inda yawan amfani dashi na iya kai ga mutum ya kasa haihuwa sannan yana taba lafiyar yaron da ba'a haifa ba idan mace me ciki na amfani dashi sannan kuma yana sanya kaikai a jikin mutum. Shi wannan sinadari dai sunansa 2-(4-tert...