Saturday, July 4
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan Hakar ma’adanai saboda matsalar tsaro

Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan Hakar ma’adanai saboda matsalar tsaro

Duk Labarai
Jihar Plateau ta dakatar da ayyukan hakar ma'adanai saboda magance matsalar tsaro dake karuwa a jihar. Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang ne ya bayyana hakan a wata sabuwar doka da ya sakawa hannu. Yace wannan mataki ya zama dole saboda yanda ake samun karuwar matsalar tsaro a jihar da suka hada da garkuwa da mutane da sayar da kwayoyi da shigowar 'yan kasar waje da sauransu. Ya bayyana cewa, dokar zata fara aiki ne ranar Juma'a 21 ga watan Janairu. Sannan yace daga yanzu sai wanda aka baiwa lasisin zasu rika hakar ma'adanai a jihar.
Hukumar ‘Yansandan Najeriya zata kammala jarabawar daukar ‘yansanda ta shekarar 2023

Hukumar ‘Yansandan Najeriya zata kammala jarabawar daukar ‘yansanda ta shekarar 2023

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya na shirin kammala jarabawar daukar sabbin 'yansandan da aka fara a tsakanin shekarun 2022/2023. Me magana da yawun hukumar ta PSC,Ikechukwu Ani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manem labarai. Yace abu na gaba da za'a yi yanzu shine gwajin lafiyar wadanda za'a dauka aikin wanda zai fara daga February 26 zuwa March 12, 2025. Ya kara da cewa, wadanda suka yi jarabawar kwamfuta a ranekun 5th zuwa 6th March, 2024 amma sunayen su basu fito cikin wadanda suka yi nasara ba su sake zuwa shafin daukar aikin su duba ko sunayensu sun fito. Yace za'a yi gwajin lafiyar sabbin daukar aikinne a Asibitoci 17 Yace za'a bude shafinne a ranar February 22nd, 2025 da misalin karfe 12 na rana. Yace kuma duk wadanda aka gayyata zuwa wajan gwajin lafiy...
Karanta Jadawalin bakaken fata 22 da suka fi kudi a Duniya>>Dangote ne na daya

Karanta Jadawalin bakaken fata 22 da suka fi kudi a Duniya>>Dangote ne na daya

Duk Labarai
Jadawalin bakaken fatar da suka fi kudi a Duniya ya bayyana inda ake ta yadashi a kafafen sada zumunta. 'Yan Najeriya 6 ne suka bayyana a cikin jadawalin wanda Dangote ne ya zo na daya sannan akwai Mike Adenuga da Abdulsamad Rabiu da dai sauransu: Ga jadawalin kamar haka: 1. Aliko Dangote - $23. 9B (Manufacturing) 2. Robert F. Smith - $23.9B (Private Equity) 3. David Steward - $11. 4B (IT Services) 4. Alexander Karp - $10. 2B (Technology -Palantir) 5. Mike Adenuga - $6.8B (Telecommunications & Oil) 6. Abdul Samad Rabiu - $4.7B (Manufacturing) 7. Patrice Motsepe - $2.8B (Mining) 8. Jay-Z - $2. 5B (Music & Business Ventures) 9. Adebayo Ogunlesi - $2.3B (Investment Banking) 10. Oprah Winfrey - $3. OB (Media & Entertainment) 11. Michael Jordan...
Daliba daya ta Mùtù wasu da dama sun jikkata bayan da ginin Aji ya fado kusu a jihar Yobe

Daliba daya ta Mùtù wasu da dama sun jikkata bayan da ginin Aji ya fado kusu a jihar Yobe

Duk Labarai
Ginin Aji ya fadawa dalibai mata a makarantar mata ta Government Girls Science Technical College, Potiskum dake jihar. Lamarin ya farune yayin da ake tsaka da karatu kamar yanda rahotanni suka bayyana wanda yayi sanadiyyar dalibai da yawa suka makale a karkashin gini. Mutane da yawa ciki hadda malaman makarantar sun kaiwa daliban daukin gaggawa. An garzaya da daliban da suka jikkata zuwa Asibitin dake garin Fataskum. zuwa yanzu dai suna karbar kulawa ta musamman daga likitoci.
Janar Ibrahim Babangida ya amince Abiola ne ya ci zaɓen 1993 da ya rushe

Janar Ibrahim Babangida ya amince Abiola ne ya ci zaɓen 1993 da ya rushe

Duk Labarai
A karon farko, tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya amince cewa Cif Mashood Bashorun Abiola, ɗantakarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar SDP a 1993 ne ya ci zaɓen da aka soke. Janar Babangida wanda ya bayyana hakan a cikin littafinsa da ya rubuta wanda kuma aka ƙaddamar a Abuja. Littafin mai suna " A Journey in Service" wanda tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi bitarsa, ya ce Cif Abiola na jam'iyyar SDP ne ya samu nasara kan Alhaji Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC . "Lallai Mashood Abiola shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 bayan da ya samu ƙuri'u fiye da miliyan takwas inda ya samu nasara a kan Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC mai ƙuri'a fiye da miliyan biyar." In ji Janar Babangida a cikin ...
Kalli Bidiyo: Bana jin tsoronka, Sanata Natasha Akpoti ta gayawa kakakin Majalisar tarayya bayan da yace a fitar da ita daga majalisar

Kalli Bidiyo: Bana jin tsoronka, Sanata Natasha Akpoti ta gayawa kakakin Majalisar tarayya bayan da yace a fitar da ita daga majalisar

Duk Labarai
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bukaci a fitar da sanata Natasha Akpoti daga jikar Kogi daga majalisar. Lamarin ya samo asali ne bayan da sanata Natasha ta bayyana rashin jin dadin canja mata kujerar zama ba tare da saninta ba. Ta tashi tana bayyana rashin jin dadinta ne inda anan ne Sanata Akpabio ya umarci ta fita daga majalisar. Saidai tace ba zata fita ba. Daga karshe dai sai da aka kashe abin maganarta sanan aka samu sa'ida. https://www.tiktok.com/@officialaitlive/video/7473482401713311031?_t=ZM-8u4r9xPcJXj&_r=1 Kalli Bidiyon faruwar lamarin anan:
Nan da ranar 1 ga watan Maris, Gwamnatin Tarayya zata hana motocin dakon man fetur me nauyi hawa titunan Najeriya

Nan da ranar 1 ga watan Maris, Gwamnatin Tarayya zata hana motocin dakon man fetur me nauyi hawa titunan Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da fara hana motoci masu daukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 hawa titunan Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris. Gwamnatin tace zata dauki wannan mataki ne saboda rage yawan hadarurrukan dake faruwa akan titunan Najeriya. Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin hukumar kula da hadadar man fetur ta (NMDPRA). Hukumar tace nan da karshen shekarar 2025 ba zasu bar mota me daukar man fetur sama da lita 45,000 ta rika hawa titunan Najeriya ba. Wakilin hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da ya wakana a Abuja ranar Laraba. Ya kara da cewa an samu cimma matsaya tsakanin hukumar tsaron farin kaya ta DSS da hukumar kula da dokokin hanya ta FRSC, da kungiyar direbobi ta NARTO, da kungiyar ma'aikatan man fetur ta NUPENG, da saur...