Wednesday, December 24
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: Kotu ta daurewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai

Da Duminsa: Kotu ta daurewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai

Duk Labarai
Rahotanni daga babbar kotun tarayya dake Abuja na cewa, Kotun ta daure shugaban kungiyar ÌPÒB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai. Kotun tace ta sassauta masa ne maimakon hukuncin Khisa shine ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Mai shari'a Justice James Omotosho ne ya yanke wannan hukunci inda yace laifin da ake zargin Nnamdi Kanu dashi yayi muni sosai shiyasa.
Matasa ga dama ta samu: Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da shirin daukar Sabbin sojoji har guda dubu ashirin da hudu dan magance matsalar tsaro

Matasa ga dama ta samu: Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da shirin daukar Sabbin sojoji har guda dubu ashirin da hudu dan magance matsalar tsaro

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta sanar da daukar matasa guda 24,000 a cikin watanni 6 masu zuwa dan magance matsalar tsaron data addabi Najeriya. Hakan ya fito daga bakin shugaban sojojin kasa,  Lieutenant General Waidi Shaibu ne a yayin ziyarar da ya kai rundunar sojoji ta 1 dake kaduna ranar Laraba. Ya bayyana cewa, zasu yi amfani da guraren horas da sojoji guda 3 da ake dasu wajan horaa da sojojin. Ya bayyana bukatar karin sojoji dan magance matsalar tsaro da ake fama da ita.
Kalli Karin Hotuna da Bidiyo na abinda tshageran Dhaji sukawa sojojin Najeriya da suka je ceto daliban jihar Kebbi

Kalli Karin Hotuna da Bidiyo na abinda tshageran Dhaji sukawa sojojin Najeriya da suka je ceto daliban jihar Kebbi

Duk Labarai
A wani Bidiyo da ya kara bayyana, an ga yanda tsageran daji suka yiwa sojojin Najeriya kwantan Bauna suka jikkata da yawa daga cikin sojojin. An ji wani soja yana cewa, Albashin nawa akw biyanshi duka duka inda yace ba zai iya ba. Danna nan dan kallon Bidiyon Jaridun Leadership da na Sahara Reporters duk sun tabbatar da wannan harin kwantan bauna da 'yan Bindiga suka kaiwa tawagar sojojin da suka tafi kubutar da 'yan mata 'yan makarantar jihar Kebbin. Babu dai wata sanarwa a hukumance da aka fitar.
Inada masaniya kan Inda ake tsare da ‘yan mata ‘yan makaranta na jihar Kebbi>>Inji Sanata Garba Maidoki

Inada masaniya kan Inda ake tsare da ‘yan mata ‘yan makaranta na jihar Kebbi>>Inji Sanata Garba Maidoki

Duk Labarai
Sanata Garba MaiDoki daga jihar Kebbi ya bayyana cewa suna da masaniya kan inda 'yan Bindiga suka boye 'yan mata 'yan makaranta da suka sace. Ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Channels TV inda yace ba'a fita da 'yan matan daga yankin Kebbi ta kudu ba. Ya kuma bayar da tabbacin nan da kwanaki 1 zuwa 2 za'a dawo da 'yan matan. 'Yan mata 'yan makaranta su 25 ne dai aka sace daga Maga jihar Kebbi.
Mun samu nasara sosai akan tshageran Dhaji amma kalaman Shugaban Amurka, Trump ya sa suka samu karfin Gwiwar dadowa har suka dauke daliban jihar Kebbi>>Inji Gwamnatin tarayya

Mun samu nasara sosai akan tshageran Dhaji amma kalaman Shugaban Amurka, Trump ya sa suka samu karfin Gwiwar dadowa har suka dauke daliban jihar Kebbi>>Inji Gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana rashin jin dadi kan kalaman shugaban kasar Amurka, Donald Trump na cewa zai kawowa Najeriya hari. Gwamnatin tace wadannan kalaman ne suka karfafa 'yan ta'dda har suka dawo suka kai hari makarantar 'yan mata ta jihar Kebbi. Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ne ya bayyana hakan ranar Laraba. Yace sun samu nasara sosai akan 'yan Bindigar amma kalaman na Trump yasa suka dawo har suke samun kara fadada ayyukansu. Yace sojojin Najeriya na da kwarewa kuma a baya sun samu nasara sosai akan tsageran dajin dan sun kwato wasu garuruwa dake hannun tsageran dajin. Yace abinda Najeriya ke bukata ba wai wata kasa ta shigo ta yaki 'yan ta'adda ba, tana neman hadin gwiwa ne ta hanyar bayanan sirri da makamai da sauran su musamman daga kasashe irin su Amur...
Kasar Rasha zata shiryawa kasashen da basu kai ga gasar cin kofin Duniya ba wasan cin kofi na musamman wanda shima ta sama mai sunan Kofin Duniya

Kasar Rasha zata shiryawa kasashen da basu kai ga gasar cin kofin Duniya ba wasan cin kofi na musamman wanda shima ta sama mai sunan Kofin Duniya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Rasha na shiryawa kasashen Duniya da basu kai ga gasar cin kofin Duniya ba wasanni na musamman dan cin kofin data sakawa auna Kofin Duniya. Za'a buga gasar cin kofinne a daidai lokacin da ake buga gasar cin kofin Duniya a shekara me zuwa. Rasha zata aikata hakanne dan matsawa hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA lamba ta dage mata takunkumin hana shiga gasar cin kofin Duniyar data kakaba mata. Kasashen da ake tsammanin zasu shiga wannan gasa sun hada da. Russia, Serbia, Greece, Chile, Peru, Venezuela, Nigeria, Cameroon, China, da sauransu.
Kalli Bidiyo: Wannan matashin yayi kira ga gwamnatin Tarayya data hana yada Bidiyon yanda Janar Muhammad Uba ya rigamu gidan gaskiya

Kalli Bidiyo: Wannan matashin yayi kira ga gwamnatin Tarayya data hana yada Bidiyon yanda Janar Muhammad Uba ya rigamu gidan gaskiya

Duk Labarai
Wani matashi dan kudu me suna Scott Iguma ya bayyana cewa, sai da ya zubar da hawaye saboda yanda ya ga aka kashe Janar Muhammad Uba. Yace bai ji dadin yanda ya ga Bidiyon na ta yawo a kafafen sada zumunta ba inda yace yanzu yaya iyalansa zasu ji idan suka ga Bidiyon. Sannan kuma yace ganin Bidiyon zai iya ragewa Sojoji karfin Gwiwa. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1991059518629794281?t=8UXiMJ5p5gOuDKXIu-qGvg&s=19
Kalli Bidiyon Da Duminsa: Kasar Amurka ta sassauto kan zargin Mhuzghunawa Kiristoci da tace ana yi a Najeriya bayan haduwa da wakilan Gwamnatin Tarayya

Kalli Bidiyon Da Duminsa: Kasar Amurka ta sassauto kan zargin Mhuzghunawa Kiristoci da tace ana yi a Najeriya bayan haduwa da wakilan Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Wakilin Amurka ya bayyana cewa kasarsa ta sassauto kan zargin Khisan Kyiyashi da tace anawa Kiristoci a Najeriya. Hakan na zuwane bayan ganawar da wakilan kasar Amurkar suka yi da wakilan Gwamnatin Najeriya. A yanzu kasar Amirkar ta yadda da cewa kowane bangare na musulmi da Kirista na fuskantar wannan barazana ta tsaro. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1991475623479636137?t=Q4V7EXCctJ9XAW0w3TKElA&s=19 Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro malam Nuhu Ribadu ne ya jagoranci tawagar wakilan Gwamnatin Najeriyar a ganawar da kasar Amurka.
Da Duminsa: Kotu ta samu Nnamdy Khanu da Laifi a Tunzura Magoya bayansa su aikata Munanan Laifuka

Da Duminsa: Kotu ta samu Nnamdy Khanu da Laifi a Tunzura Magoya bayansa su aikata Munanan Laifuka

Duk Labarai
Kotu ta tabbatarwa da Shugaban haramtacciyar Kungiyar ÌPÒB dake son kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu da laifukan tà'àddànci guda 3. Gwamnatin tarayya ta shigar da kara kan laifukan ta'addanci guda 7 da take zargin Nnamdi Kanu da aikatawa. Mai Shari'a, James Omotosho ne ya bayyana haka a ranar Alhamis. An samu Nnamdy Kanu da tunxura mabiyansa su aukata ayyukan tà'àddànci.
Kalli Bidiyon yanda jami’an tsaro suka zagaye Nnamdy Khanu suna ta kokarin kwace abin magana daga hannunsa yayin da yake ta zhaghin Alkali

Kalli Bidiyon yanda jami’an tsaro suka zagaye Nnamdy Khanu suna ta kokarin kwace abin magana daga hannunsa yayin da yake ta zhaghin Alkali

Duk Labarai
Shugaban kungiyar ÌPÒB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya rika zagin Alkali a kotu yana cewa bai san shari'a ba. Kanu yace babu ta yanda za'a yi a yanke mai hukunci da dokar da babu ita a rubuce. Ya rika maganane yana rike da abin magana watau Lasifika. Saidai Jami'an DSS sun zagayeshi inda suka rika kokarin Kwace abin maganar daga hannunsa. Lamarin ya dauki hankula saboda ya ki bayarwa sai da aka yi amfani da karfi. https://twitter.com/Morris_Monye/status/1991448455332655354?t=nNIGKpQvqAqpSwkVRRcgFw&s=19