Babu kananan yara a cikin wadanda muka kai kotu, duk manyan mutanene wasunsu ma suna da aure>>Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu kananan yara a cikin wadanda ta gabatar a kotu da take zargi da cin amanar kasa ta hanyar kifar da gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad.
Lauyan Gwanatin, Rimazonte Ezekiel ne ya bayyana haka a ganawarsa da manema labarai.
Ya kara da cewa, laifin su shine suna kiran sojoji su kwace mulki da daga tutar kasashen waje da kuma tayar da hankula.
https://twitter.com/channelstv/status/1852450588178460769?t=9Ads0XRv52vEALHwdLs_Mg&s=19
Saidai da yawa sun kalubalanceshi da cewa maganar tasa ba gaskiya bane musamman tunda gashi mutane na gani yara ne suka gabatar.
A baya dai hutudole ya kawo muku yanda kakakin 'yansandan Najeriya ya kare kama yaran inda yace doka tace ko da shekaru 7 za'a iya kaishi kotu.
Ya kara da cewa kuma cikin yaran da...








