Tuesday, January 7
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir

Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir

Duk Labarai
Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir. A baya dai malam ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima basu sani ba aka kara kudin man fetur. Inda malamin yayi ikirarin cewa, jaridarta Daily Trust ce ta ruwaito hakan. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa. Inda da yawa suke ganin cewa bai kamata malamin yayi wannan magana ba. Me zaku ce ?
‘Yan kasuwar man fetur sun ce man fetur dina yayi arha da yawa basa samun ribar da suke so>>Dangote

‘Yan kasuwar man fetur sun ce man fetur dina yayi arha da yawa basa samun ribar da suke so>>Dangote

Duk Labarai
Aliko Dangote ya koka da cewa, 'yan kasuwar man fetur sun koka da cewa man fetur dinsa yayi arha da yawa. Dangote ya bayyana hakane ta bakin wakilin kamfaninsa,me suna Devakumar Edwin. Ya kara da cewa,tuni 'yan kasuwar suka aikawa da shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu korafi akan wannan lamari. Yace da kyar suke samun suna sayar da tankar Gas 29 saboda 'yan kasuwar basa son saye, yace dan haka dole suke fitar da sauran zuwa kasashen waje. Kamfanin dai na Dangote ya rage farashi daga Naira 1200 zuwa Naira 1000 zuwa Naira 900 akan kowace lita.
Hotuna: Kalli Yanda mata ke neman maza suna biyansu suna lalata dasu

Hotuna: Kalli Yanda mata ke neman maza suna biyansu suna lalata dasu

Duk Labarai
Matan Turawa na zuwa yawon shakatawa a kasar Turkiyya inda suke biyan matasan kasar suna lalata dasu. Garin dai gabar teku yake inda ake kiransa da sunan Marmaris. Matan turawan dake tsakanin shekaru 20 zuwa 70 na tururuwa sosai zuwa wannan gari dan neman matasan kasar na Turkiyya su biya musu bukatunsu. Katie me shekaru 22 wadda taje wannan gabar tekun ta kasar Turkiyya daga yankin Wales na kasar Ingila ta bayyana cewa tana da saurayi Omar dake biya mata bukatarta kuma ya iya kwanciya da mace. Tace duk da tasan yana da wasu mata 10 da yake kwanciya dasu amma hakan bai dameta ba dan kuwa tazo jin dadine kawai. Jaridar theSun ta kasar Ingila ta ruwaito cewa akwai wani Facebook group da aka bude ake tozarta mata da maza dake irin wannan aikin masha'a a kasar ta Turkiyya wanda...
‘Yan Bindiga sun kashe ‘yansanda 5 da sojoji 2 a Jihar Zamfara

‘Yan Bindiga sun kashe ‘yansanda 5 da sojoji 2 a Jihar Zamfara

Duk Labarai
Kwamishinan 'yansandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalinja ya tabbatar da mutuwar 'yansanda 5 da sojoji 2 wanda 'yan Bindiga suka kashe a karamar hukumar Tsafe dake jihar. Ya bayyana cewa 'yan Bindigar sun yiwa jami'an tsaron kwantan baunane inda suka bude musu wuta a kan hanyar Gusau zuwa Funtua ranar Alhamis. Ya bayyana cewa, 'yan Bindigar sun tafi kaiwa kamfanin gini na Setraco Company Hari ne inda jami'an tsaron suka samu bayanan sirri suka tafi dan taresu. Yace yanda aka yi suka kashe musu jami'ai kenan.
‘Yan kasuwar Man fetur da yawa basa sayen man fetur din daga matatar mu>>Dangote

‘Yan kasuwar Man fetur da yawa basa sayen man fetur din daga matatar mu>>Dangote

Duk Labarai
Wakilin kamfanin Dangote, Devakumar V. G. Edwin ya bayyana cewa, mafi yawan 'yan kasuwar man fetur na Najeriya basa sayen man fetur din daga matatarsu. Ya bayyana hakane a wata hira ta musamman da aka yi dashi inda yace kaso 95 na 'yan kasuwar man fetur din basa saye daga wajensu. Yace hakan yasa dole suke fitar da man fetur din nasu zuwa wasu kasashe dan sayarwa.