Sirrin man kadanya
DAMINA UWAR ALBARKAWannan KADANYA kenan. Itama tana daga cikin 'ya'yan itatuwan da ake samun wadatuwarsu a lokutan DAMINA.
Masana sun tabbatar tana dauke da:
Vitamins: A, C, E da kuma K
Minerals: potassium, magnesium da kuma iron
Tana dauke da Antioxidants
Nutritional fibre
Fatty acids masu Kara lafiyar jiki
A irin wannan yanayi da abincin namu sai a hankali, ya kamata mu dinga amfani da ita kuma mu bawa iyalanmu gwargwadon Hali.
Allah Ka wadace mu da lafiya, kwanciyar hankali da wadatuwar arziki a duka kasar nan tamu.
Man kadanya na taimakawa wajan hana fata tsufa da wuri.
Yana hana kaikayin fata.
Yana kare fata daga zafin rana.
Idan ana amfani da Man kadanya yau da kullun, Yana taimakawa wajan kara Hasken Fata.
Ana iya hada man kadanya da man da a...