Gwamatin Tarayya Ta Sanar Da Shirinta Na Zuba Jarin Dalar Amurka Biliyan 4.8 a Fannin Kiwon LafiyaNajeriya
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayinda yake karin haske kan sauye-sauyen da gwamnatin ta yi a fannin kiwon lafiya wanda a cewarsa, zai lashe sama da dala biliyan 4.8 wajen zuba jari duk a yunkurin gwamnati na ganin an farfado da ingancin kiwon lafiya a Najeriya tare da magance Kalubalen da ya jima yana addabar bangaren kiwon lafiyar
Shettima, ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da rukunin asibitocin Sahad a birnin Abuja,
"Gwamnatin mu ta kuma Kaddamar da gyare-gyare a kan bangarori huɗu masu mahimmanci wanda suka haɗa: sauya tsarin kula da kiwon lafiya, samar da ingatattun bangarorin binciken lafiya, buɗe Sabbin Cibiyoyin , da ƙa...
Ma'aikacin dake aiki a filin jirgin sama na malam Aminu Kano dake jihar Kano, Auwal Dankode wanda ya tsinci dala $10,000 kwatancin sama da Naira Miliyan 15 ya mayar da ita ga maisu ya samu karin girma.
Auwal ya samu karin girma da kyautar kudi sannan an bashi aikin jakadar hukumar NAHCO da yakewa aiki.
Shugaban hukumar, Mr. Indranil Gupta ne ya bayyana haka inda yace auwal ya nuna kwarewa da jajircewa da gaskiya wajan aikinsa inda ya karfafeshi cewa ya ci gaba da wannan aiki.
Auwal dai ya tsinci kudinne yayin da yake aikin share jirgin saman Egypt Air, kuma nan take ya mika kudin ga shugabansa.
Akwai yiyuwar Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zai canja wasu ministoci a majalisarsa ta zartaswa.
Hakan wani mataki ne na cire ministocin da basa tabuka wani abin azo a gani.
Shugaban dai ya jima yana fuskantar matsi akan ya canja ministocin da basa yin aikinsu yanda ya kamata.
A shekarar da ta gabata ne dai shugaban kasar ya kafa wani tsari na auna kokarin ministocin inda yayi gargadin duk wanda ba ya kokari za'a koreshi daga aiki.
BABBAR MAGANA: Bello Ťùŕjì Da Tawagarsa Šùñ Ķwaçe Mòťàŕ Ýàķìn Śòjòji Da Sauran Màķamaì Bayan Wani Artabu Da Suka Ýi.
A wani bidiyon dake dauke da lamarin, an nuno 'ýañ ta'àďďañ sun kewaye motar suna ta murna da shewa.
Jarumin Finafinan Hausa, Yakubu Muhammad Ya Dauki Nauyin Karatun Wasu Yara Guda Biyu Har Zuwa Jami'a.
Jarumin ya dauki nauyin karatun yaran ne bayan ya ga wani bidiyon su a kafar sadarwa inda suke kalaman aluta da 'yan jami'a suke yi. Wanda hakan ya sa ya yi tattaki har zuwa garin Wudil domin ganawa da yaran da kuma iyayensu.
Babban bankin Najeriya,CBN ya kori manyan jami'an bankin NIRSAL Bank wanda mallakin CBN dinne.
A sanarwar da aka gani CBN din ta bayyana dalilan gyara da canja tsarin ayyuka na bankin a matsayin dalilin yin korar.
Hakanan akwai yiyuwar a kara yin wata korar inda yanzu haka ake binciken wasu karin ma'aikatan bankin.
Shugabaɲ Kungiyar Malamai Masana Ilimin Taurári na Nájeriya, Shéikh Imam Habibi Abdallah Assufiyyu ya bayyana cewa "mun gano céwa kowanne ɗan Adam yana ɗauke da wata lambar sirri wacce Ubaɲgiji ya halicce shi da ita, da mutane za su iya tantance nasu da kowa zai iya bacéwa kamar yadda jinsin aljannu ke bacewa, kuma da kowa zai iya magana da dan uwansa ba tare da kiran waya ba ko haduwa ta zahiri a ko'ina suke a doran kasa "
Shehin Malamin ya kara da cewa "da yiwuwar hakan zai fara kasancewa a shekaru masu zuwa".
Me za ku ce?
Gwamnatin tarayya ta umarci shuwagabannin sojoji da su koma jihar Sokoto da zama.
Hakan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro musamman ta garkuwa da mutane ke kara kamari a yankin arewa maso yamma.
Sanarwar hakan na kunshene a cikin bayanan da sakataren yada labarai, Henshaw Ogubike ya fitar.
Yace wannan kokari ne na kawar da matsalar ta'addanci da garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro da ake fama dasu a yankin.
Gwamnatin ta bayyana takaici da matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a yankin na Arewa maso yamma inda tace wannan mataki alamu ne na daukar matsalar da muhimmanci da gwamantin ta yi.