Thursday, January 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Yau Sule Lamido Ke Cika Shekaru 76 Da Haihuwa

Yau Sule Lamido Ke Cika Shekaru 76 Da Haihuwa

Duk Labarai
Yau Juma'a, 30 ga watan Augusta 2024, jigo a jam'iyyar PDP, kuma jagoran ta a Jihar Jigawa Alhaji Dr. Sule Lamido CON, yake cika shekaru 76 a duniya. Ya samu nasarori da yawa, ya kuma samar da yawa, daga ciki shine maida jihar Jigawa Birni, da kuma yadda ya kula da ayyukan raya jihar, tattalin arziki, tsaro, kawo hadin kai da kuma zumunci. Allah Ya k'ara masa lafiya da nisan kwana. Daga Hon Saleh Shehu Hadejia

Gyaran nono su tsaya

Nono
Akwai hanyoyin gyaran nono da yawa, a wannan rubutu zamu yi maganane akan yanda zaki gyara nonuwanki su tsaya. Saidai kamin mu fara bayani,bari mu gaya muku abubuwan da a likitance aka tabbatar suna sanya nonuwa su zube. Shekaru: Idan mace shekarunta suka fara ja, nonuwanta zasu zube. Rashin Kuzari: Idan na fama da rashin kuzari wanda yawanci ke samo asali daga rashin samun ingantaccen abinci me gina jiki shima yana sanya nonuwa su zube. Rashin Sha'awa: Idan ya zamana mace bata da sha'awa ta jima'i ko sha'awarta ta yi kasa sosai, bata damu da jima'iba, hakan yana iya kaiwa ga zubewar nono. Abinda ke jawo hakan shine yawanci rashin cin abinci me gina jiki da kuma rashin samun nutsuwa da aikin karfi. Gravity: Yanayi ne da babu yanda mace zata yi indai tana raye sai nonuwant...
Hukumar NCC ta gano mutum 1 me layukan waya dubu dari(100,000) a Najeriya

Hukumar NCC ta gano mutum 1 me layukan waya dubu dari(100,000) a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar kula da sadarwa,NCC ta bayyana cewa ta gano wani mutum 1 wanda ke da layukan waya dubu dari (100,000) shi kadaai. Wakilin Hukumar, Reuben Muoka ne ya bayyana hakan inda ya jaddada cewa ranar 14 ga watan Satumba me zuwa ne rana ta karshe ga kowa ya hada layinsa da lambar NIN. Yace suna aiki ne tare da ofishin Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu dan dakile barazanar tsaro. Sannan yace suna aiki tukuru dan hana sayar da layukan wayar da aka riga aka musu rijista.
Abin a Yaba: Ya tsinki Dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ya mayarwa mesu

Abin a Yaba: Ya tsinki Dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ya mayarwa mesu

Duk Labarai
Wani ma'aikacin filin jirgin sama a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano me suna Auwalu Ahmed Dankade ya tsinci dala $10,000 kwatankwacin Naira Miliyan 15 amma ya mayar da ita ga maishi. Auwalu Ahmed Dankade yanawa wani kamfanin kula da karbar sako aiki ne a filin jirgin saman kjma a hirarsa da Daily Trust ya bayyana cewa iyayensa sun masa tarbiyyar kada ya dauki duk wani abu da ba nashi ba, ya wadata da abinda Allah ya bashi. Kamfanin da yakewa aiki dake Legas,ya gayyaceshi zuwa Legas din inda ake tsammanin za'a girmamashi ne.