Kuma dai: Kasar Israela bata daddara ba, ta sake kai harin da ya kashe sojan kasar Iran
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a birnin Aleppo na kasar Syria da kashe mutane da yawa ciki hadda wani sojan kasar Iran.
Saidai zuwa yanzu, kasar ta Israela bata kai ga bayyana cewa itace ta kai harin ba.
Wannan ne dai hari na farko tun bayan na 1 ga watan Afrilu wanda Israelan ta kai kan babban birnin Syria, Damascus wanda yayi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar Iran.
A wancan lokaci dai, kasar Iran din ta mayar da martani ta hanyar jefawa kasar Israela makamai da yawa wanda sai da kasashen Amurka, ingila da Faransa suka taru suka taresu.
Wannan karin kuma ba'a san wane mataki ne kasar Iran din zata dauka akan wanan harin da Israelan ta kai mata ba.