Obasanjo ya bayyana cewa a zamanin mulkin Marigayi shugaban kasa, Umar Musa ‘Yar’adua Dangote yaso Gwamnati ta sayar masa da matatar man Fatakwal data Kaduna amma ‘Yar’adua yaki yadda
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a zamanin mulkin marigayi, Tsohon shugaban kasa, Umar Musa 'yar'adua, Dangote ya so sayen matatar man fetur ta Kaduna da Fatakwal amma 'yar'aduan yaki yadda.
Obasanjo da yake bayani ranar 2 ga watan Janairu ya zargi kamfanin man fetur na kasa, NNPCL da yaudarar 'Yar'adua a wancan lokaci suka hanashi amincewa da dala Miliyan $750 da Dangoten yaso biya a wancan lokacin dan kula da matatun man fetur din guda biyu.
Obasanjo yace a wancan lokacin watau 2007, tuni har Dangote ya biya kudin, Dala Miliyan $750 amma 'Yar'adua ya mayar masa da kudin yace Kamfanin NNPCL zai ci gaba da kula da matatun man.
Obasanjo yace, ya saka baki dan kokarin ganar da shugaba 'yar'adua kan lamarin amma sai bai fahimceshi ba ya nace akan matsayarsa na ...