Saturday, February 21
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon yanda sojan Najeriya yayi bayanin Abashi da Alawus da suke dauka dalla-dalla

Kalli Bidiyon yanda sojan Najeriya yayi bayanin Abashi da Alawus da suke dauka dalla-dalla

Duk Labarai
Wani sojan Najeriya yayi bayanin Albasinda akw biyansu dalla-dalla tun daga fara aiki har ka gama. Saidai yayi maganane akan kurtu inda yace yayi wannan bayanine musamman ga wadanda ke son shiga aikin na soja. Yace albashin farko idan aka daukeka aiki Naira 104,000 ne. Daga nan ne idan ka shekara 5 aka kara maka matsayi, zaka samu karin Albashin zuwa Naira 112,000. Yace idan mutum yayi shekaru 10 za'a kara masa albashi zuwa Naira 115,000. Yace idan ka shekara 15 za'a kara maka albashi zuwa Naira 125,000. Yace idan ka shekara 20, za'a kara maka albashi zuwa Naira 150,000. Yace amma akwai alawus na Naira dubu 20 duk wata da ake biyansu. https://twitter.com/Teeniiola/status/1996090687670903014?t=hFwHR8pD9yrEWgZptQAyTw&s=19
Wani ya koka da cewa a lokacin Christopher Musa na shugaban sojojin Najeriya, sau 3 ana Jèfà Bàmà-Bàmàì akan Musulmai wanda basu ji ba basu gani ba da sunan kuskure

Wani ya koka da cewa a lokacin Christopher Musa na shugaban sojojin Najeriya, sau 3 ana Jèfà Bàmà-Bàmàì akan Musulmai wanda basu ji ba basu gani ba da sunan kuskure

Duk Labarai
Wani bawan Allah ya koka dacewa a lokacin Janar Christopher Musa na shugaban sojojin Najeriya, sau 3 ana jefawa musulman da basu ji ba basu gani ba bama-bamai da sunan Kuskure. Ya ce an jefawa masu Maulidi Bam a Tudun Biri ranar 3 ga watan Disamba 2023 inda mutane 126 suka rasa rayukansu. Hakanan yace akwai wani kauye a Sokoto da shima aka jefawa bama-bamai mutane 10 suka rasa rayukansi. Sannan yace ranar 13 ga Janairun 2025 ma an jefawa mutane bama-bamai a Zurmi jihar Zamfara inda mutane 16 suka rasa rayukansu. Yace saidai tun bayan sauke Janar Christopher Musa ba'a sake samun irin wannan matsalar ba. Yace nadashi Minista rashin girmama Musulmai ne kuma ya sa musulmai da yawa sun kadu, inda yayi fatan Sanatoci Musulmai ba zasu amince dashi ba a matsayin sabon ministan tsa...
Zamu fara kera wasu bangarori na jirgin sama>>Inji Shugaba Tinubu

Zamu fara kera wasu bangarori na jirgin sama>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Najeriya zata fara kera sassan jirgin sama. Shugaban ta bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar kan jiragen sama na kasa da kasa a Najeriya. Sakataren Gwamnati, George Akume ne da ya wakilci shugaban kasar a wajan taron ya bayyana haka. Ya bayyana cewa kudin shigar Najeriya daga bangaren harkokin jiragen sama zasu kai Dala biliyan $2.56 nan da shekarar 2029.
Wannan Matar Aure ce aka yi Ghàrkùwà da ita a Abuja ana neman Naira Miliyan 50 kudin Fànsà

Wannan Matar Aure ce aka yi Ghàrkùwà da ita a Abuja ana neman Naira Miliyan 50 kudin Fànsà

Duk Labarai
Wannan wata matar aure ce da aka yi garkuwa da ita a Abuja. Tun ranar Lahadi data shiga motar once chance a Lugbe ba'a kara jin duriyarta ba sai dai suka kira suka ce a tura musu Dubu 50 Bayan an tura musu sai suka ce suna neman Miliyan 50, mijin yace bai da kudin. Ya je wajan 'yansanda amma sai yawo ake msa da hankali babu alamar zasu taimaka masa su ceto matar tasa. https://twitter.com/OzorNdiOzor/status/1995818456147496977?t=UVdq0SIrgGtF8WABwxM7SA&s=19
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda sojoji suka Làkàdàwà wani Dansanda Dùkàn Tsìyà sannan suka kwace masa Byndìghà a Jos

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda sojoji suka Làkàdàwà wani Dansanda Dùkàn Tsìyà sannan suka kwace masa Byndìghà a Jos

Duk Labarai
Bidiyon wani fada daya kaure tsakanin wasu sojoji da wani dansanda a Jos babban Birnin jihar Filato ya dauki hankula a kafafen sada zumunta An ga yanda sojojin suka kwace Bindigar dansandan. Sannan wasu rahotanni sun ce sun kuma lakada masa na jaki. https://twitter.com/General_Somto/status/1995745568430195194?t=aI2Krr87XuBEHQiurxIgDA&s=19 https://twitter.com/General_Somto/status/1995920361846604155?t=MH9hRN7bF7-VytrMP0ySsQ&s=19
Hadiza Gabon ta sabunta dakin da take Hira da mutane inda ta saka hotunan manyan jarumai saidai Rashin ganin Hoton Adam A. Zango ya jawo cece-kuce

Hadiza Gabon ta sabunta dakin da take Hira da mutane inda ta saka hotunan manyan jarumai saidai Rashin ganin Hoton Adam A. Zango ya jawo cece-kuce

Duk Labarai
Tauraruwar Kannywood, Hadiza Gabon ta sabunta dakin daukar shirye-shiryen hirar da take da mutane inda ta saka hotunan manyan jarumai amma babu hoton Adam A. Zango. Lamarin ya dauki hankula inda aka ga mutane nata mayarwa Hadiza Gabon da raddi kala-kala inda da yawa ke nuna mata rashin dacewar hakan. https://www.tiktok.com/@prince_abdool/video/7578566841547640072?_t=ZS-91taL7CYyvp&_r=1 https://www.tiktok.com/@hadizaaliyugabon/video/7578602441503952150?_t=ZS-91tZCAa9pGj&_r=1 https://www.tiktok.com/@umarpitykhalid0/video/7579216257484868871?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7579216257484868871&source=h5_m&timestamp=1764709276&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wL...
Kalli Bidiyon: Duk da cin mutuncin da sukawa Juna a Media, Gfresh zai mayar da matarsa

Kalli Bidiyon: Duk da cin mutuncin da sukawa Juna a Media, Gfresh zai mayar da matarsa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gfresh zai mayar da matarsa ko ma ya mayar da ita. Hakan na zuwane bayan da aka ga matar tasa a Tiktok Live din Gfresh din kuma har ma ya dorata a babban allo. An jima tana wa masu musu bakin ciki habaici ita da mijin nata. Wasu dai da suka shigar mata fadan da ta yi da Gfresh an gansu suna fadin ta koma da wuri ya kamata ta jawa Gfresh din aji. https://www.tiktok.com/@mrs.gfresh/video/7579053809305980180?_t=ZS-91tVrYF4hjV&_r=1