Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kaiwa tsohon kwamishinansa, Bashir Sa’idu dake daure a gidan yari kan zargin satar sama da Naira Biliyan 3 ziyara
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kaiwa tsohon Kwamishinansa,Bashir Sa'idu ziyara a gidan yari.
An kama Tsohon kwamishinan ne bisa zargin satar kudi da cin amana.
Wasu daga cikin laifukan da ake zarginsa dasu sun hada da sayar da daloli daga asusun ajiyar kudi na jihar akan farashin Naira 410 maimakon farashin 498.
Wanda hakan ya kawowa Gwamnatin asarar Naira Biliyan 3.96.
Sannan kuma akwai maganar sayar da rukunin gidajen Marafa wanda shima ana neman Naira Miliyan 244 daga hannun tsohon kwamishinan.
Wasu dai sun yi zargin bita da kullin siyasa a zarge-zargen da akewa tsohon kwamishinan amma hukumomi sun yi Alkawarin yin Aldaci a binciken da akewa tsohon Kwamishinan.
Bayan ziyarar tasa, El-Rufai yaki yace uffan kan abinda ya faru inda ya shiga mota ya...