Friday, January 10
Shadow

Duk Labarai

‘Yanbindiga sun kai hari kasuwar Shinkafi tare da sace gomman mutane

‘Yanbindiga sun kai hari kasuwar Shinkafi tare da sace gomman mutane

Duk Labarai
Al’ummar garin shinkafin jihar Zamfara sun ce 'yanta’adda sun kai wani hari kasuwar garin inda suka tafi da gwammon mutane tare da jikkata wasu. Mazauna yankin sun ce 'yanbindigar sun kai harin ne ana tsaka da cin kasuwar Shinkafin da ranar yau Alhamis. Sai dai har kawo yanzu rundunar 'yansandan jihar ta Zamfara ba ta ce komai kan harin. Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da gawurtaccen ɗanbindingar nan da ke cin karensa babu babbaka a jihar Zamfara, Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan al'umma. A makon da ya gabata ne dai sojoji suka kama wani makusancin ɗanbindigar al'amarin da ya ce ya fusata shi kuma zai ɗauki fansa.
Shan Giya ba haramun bane >>Inji malamin Kirista, Apostle Abel Damina

Shan Giya ba haramun bane >>Inji malamin Kirista, Apostle Abel Damina

Duk Labarai
Babban malamin Kirista, Apostle Abel Damina ya bayyana cewa Annabi Adamu (AS) da Hauwa (AS) basu ci komai a gidan Aljannah ba. Ya bayyana hakane a yayin da yake magana a cocinsa. Ya yi ta nanata cewa basu ci komi ba inda yace waye a wajan da zai iya bayar da labari? Hakanan ya kara da cewa, Shan giya da shan taba ba haramun bane mutum ne da kansa zaiwa kansa fada dan daina yinsu. Wadannan maganganu nashi sun jawo cece-kuce sosai inda da yawa suna tafi akan cewa baya kan daidai. Kalli bidiyon jawabin nasa anan
Ƙudurin dokar haraji zai ƙara jefa jama’armu cikin talauci – Gwamnatin Kano

Ƙudurin dokar haraji zai ƙara jefa jama’armu cikin talauci – Gwamnatin Kano

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana hamayyarta ga ƙudirin dokar harajin da yanzu haka ke gaban majalisar dokokin Najeriya wanda shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta ne ya bayyana haka a yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025 a dandalin Ma'ahaha da ke birnin Kano. Wata sanarwa da ke ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba ta ce gwamnan ya ce "wannan kundin dokar harajin ba za ta magance matsalar tattalin arziƙinmu ba. Kano tana hamayya da wannan ƙudiri da zai shafi walwalaw al'umma." Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da tankiyya tsakaninta da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda ya soki kundin.
Kalli Kwalliyar Sabuwar Shekara ta Rahama Sadau

Kalli Kwalliyar Sabuwar Shekara ta Rahama Sadau

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata data sha kwalliyar Sabuwar shekara. Tawa masoyanta fatan Alheri.
Kungiyar Kwadago tace zata nemi karin mafi karancin Albashi a shekarar 2025 saboda tsadar rayuwa

Kungiyar Kwadago tace zata nemi karin mafi karancin Albashi a shekarar 2025 saboda tsadar rayuwa

Duk Labarai
Kungiyar kwadago tace zata nemi a kara mata yawan mafi karancin albashi daga dubu 70 zuwa sama a shekarar 2025. Kunguyar tace a kowace shekara ya kamata a rika lura da yanayin tsadar rayuwa dan karawa ma'aikata Albashi. Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan inda yace me zai hana a rika la'akari da yanayin tsadar rayuwa kowace shekara dan karawa ma'aikata Albashi maimakon jira sai bayan shekara 5. Yace su da NLC sun fara tattaunawa kan maganar. A watan Yuli da ya gabata ne dai kungiyoyin kwadagon da gwamnatin tarayya suka cimma matsaya game da karin Albashi zuwa Naira dubu 70 maimakon Naira dubu 30 da ake biya a baya. Hakan na zuwane bayan shekaru 5 da yin karin farko.
An haramta jin wakokin Rarara a Jamhuriyar Nijar bayan da yawa shugaban kasar Barazana

An haramta jin wakokin Rarara a Jamhuriyar Nijar bayan da yawa shugaban kasar Barazana

Duk Labarai
Rahotannin da muke samu daga kasar Nijar na cewa hukumomi a kasar sun sanar da haramta jin wakokin mawakin siyasa Dauda Kahutu, Rarara. Hakan na zuwane bayan da Rarara yawa shugaban kasar Nijar Tchadi Barazanar ya dawo da Bazoum kan mulki ko kuma ya fara zubo masa wakoki. Rarara yace "Na bawa Tchani kwana 20 ya dawo da Bazoum ko ya sanya lokacin zabe, ko kuma na soma zubo masa wakoki ba kakkautawa" A sanarwar da kafar Damagaram Post ta ruwaito tace ne kawai an haramta jin wakokin Rarara din a Jamhuriyar Nijar amma basu bayar da cikakken bayani ba.
Babban Abin Alfaharina shine har shekarar 2024 ta kama ta kare ban sha giya ko sau daya ba>>Inji Mawakiyar kasar Amurka, Rihanna

Babban Abin Alfaharina shine har shekarar 2024 ta kama ta kare ban sha giya ko sau daya ba>>Inji Mawakiyar kasar Amurka, Rihanna

Duk Labarai
Shahararriyar mawakiyar kasar Amurka, Rihanna ta bayyana cewa, abinda take Alfahari dashi a shekarar 2024 shine har shekarar ta fara ta kare bata sha giya ko sau daya ba. Rihanna dai ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta yayin da take murnar shigar sabuwar shekara. A kwanaki dai Rihana ta bayyana cewa ta yi nadamar shigar tsiraici da ta rika yi a baya inda tace babban abinda ya sata nadama shine da ta ga ta zama uwa.
Da Yardar Allah Shekarar 2025 Za Ta Kasance Shekarar Cika Alkawura Da Burikanmu, Sakon Shugaba Tinubu Ga ‘Yan Nijeriya

Da Yardar Allah Shekarar 2025 Za Ta Kasance Shekarar Cika Alkawura Da Burikanmu, Sakon Shugaba Tinubu Ga ‘Yan Nijeriya

Duk Labarai
SAKON SHIGA SABUWAR SHEKARA ZUWA GA 'YAN NIJERIYA Yan uwana ƴan Nigeria, A yayin da muka shiga 2025, ina yi wa kowa fatan alheri. Ina fatan mun shiga shekarar da ƙafar-dama, ƙunshe da farinciki, wadata nasara, da lafiya mai ɗorewa. Wannan sabuwar shekara da muka shiga, cike take da fatan samun ingantattun kwanaki a cikinta, kuma da yardar Allah, shekarar 2025 za ta kasance shekarar cika alkawura, da burikanmu na bai ɗaya. Duk da cewa shekarar 2024 ta kasance ɗauke da ƙalubale mai tarin yawa ga ƙasarmu da ƴaƴanta, ina da ƙwarin gwiwar cewa sabuwar shekara za ta zo mana da ƙafar -dama. Ƴar manuniya ta nuna cewa, juma'ar tattalin arzikin mu ta fara yin kyau tun daga larabarta ga al'ummarmu, farashin man fetur ya fara sauka sannu a hankali, mun sami rara a cinikayyar ƙasa da ...
Ka Çìŕè Ģìŕman Ķai Ka Saurari Koken Al’umma Kan Illolin Manufofin Haraji, Sakon Gwamnan Bauchi Ga Tinubu

Ka Çìŕè Ģìŕman Ķai Ka Saurari Koken Al’umma Kan Illolin Manufofin Haraji, Sakon Gwamnan Bauchi Ga Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Gwamnonin jam’iyyar PDP, kuma Gwmana jihar Bauchi Bala a Muhammad ya gargadi Shugaban ƙasa cewa kada ya nuna ģìŕman kai, ya kuma saurari ra’ayin al’umma akan illolin haraji. Gwamna yana mai jaddada cewa, idan aka amince da dokokin haraji da aka gabatar, hakan zai iya haifar da barazana ga ci gaban ƙananan hukumomi da jihohi. Mohammed ya soki matsayin Tinubu kan dokokin harajin da ya kira “ba na dimokuradiyya ba,” yana cewa ko wadanda suke mulkin soja za su saurari al’umma kuma su magance matsalolinsu. Kaura ya yi suka ga dokokin harajin Tinubu a gaban Majalisar Ƙasa, yana mai cewa an tsara su ne don fifita wata yanki fiye da wata.
Ni Ma Na Goyi Bayan Sarki Sanusi II Kan Batun Takaita Haihuwa, Duba Da Yadda Wasu Magidantan Ba Sa Iya Kula Da Kiwon Da Allah Ya Ba Su Na Iyalansu, Inji Sheik Pantami

Ni Ma Na Goyi Bayan Sarki Sanusi II Kan Batun Takaita Haihuwa, Duba Da Yadda Wasu Magidantan Ba Sa Iya Kula Da Kiwon Da Allah Ya Ba Su Na Iyalansu, Inji Sheik Pantami

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Ni Ma Na Goyi Bayan Sarki Sanusi II Kan Batun Takaita Haihuwa, Duba Da Yadda Wasu Magidantan Ba Sa Iya Kula Da Kiwon Da Allah Ya Ba Su Na Iyalansu, Inji Sheik Pantami Me za ku ce?