Wannan matashin Kirista ya bayyana cewa, a kokarin neman gaskiya da yake ne ya hadu da Musulunci kuma ya musulunta.
https://twitter.com/i/status/2008060497745043698
Rahotanni sun bayyana cewa, Rikicin Jam'iyyar APC ya kara ci gaba da kazancewa inda ake cacar baki tsakanin Ministan Abuja Nyesom Wike da sakataren jam'iyyar APC din, Ajibola Basiru.
Ajibola Basiru ya bayyana cewa, kamata yayi Wike ya sauka daga mukamin nasa saboda munanan kalaman da yayi akan jam'iyyar APC.
Wike a wajan taron da yayi a jihar Rivers yace duk wanda ke son yi musu katsalandan a siyasar jiharsu ta Rivers, zai kwashi kashinsa a hannu.
iHakan na zuwane dai yayin da rikici tsakanin Gwamnan Rivers, Simi Fubara da Wike din ke kara kazanta.
Wike ya dage cewa, Fubara ba zai tsaya takara ba a karo na biyu.
'Yan matannan da suka fito suka bayyana cewa ba zasuwa mahaifinsu addu'a ba bayan rasuwarsa sun ce mahaifiyarsu ce ta sakasu.
Sun bayyana cewa, kuma duk masu zaginsu, suna fatan Allah ya baiwa 'ya'yansu mazaje irin mahaifinsu.
https://www.tiktok.com/@fatima.yakubu54/video/7591800870786829589?_t=ZS-92pBiVULCjZ&_r=1
Yan matan dai sun dauki hankula bayan da suka bayyana suna murna da rasuwar mahaifinsu inda suka ce ya yaddasu bai musu komai ba, mahaifiyarsu ce ke wahala dasu har suka girma.
Marikiyarsu wadda 'yar uwa ce a wajan Mahaifiyarsu ta bayyana cewa, sun yi hakanne dan ya zama wa'azi ga sauran maza masu irin wannan hali.
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, akwai yiyuwar Tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan tsaro, Abubakar Badaru ,ai bar jam'iyyar APC zuwa ADC.
Rahoton yace hakan na zuwane yayin da baraka ke ci gaba da bayyana a tsakanin tsohon Ministan da magajinsa gwamna me ci na yanzu, watau Namadi.
https://twitter.com/i/status/2008108500493197502
Wani Bidiyon Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana inda aka jishi yana wata barazana.
An ji Wike na barazanar ne a wajan wani taron siyasa a jiharsa.
Ya bayyana cewa mutum kada ya zo ya kawo musu abinda ba shi kenan ba a jihar Rivers.
Wike bai fadi da wanda yake ba inda yace mutum ya tambayi abinda ya faru da wadanda suka yi yunkurin yiwa jihar Rivers kutse a baya.
saidai wasu sun ce da sakataren Jam'iyyar APC yake inda wasu kuma ke cewa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake.
https://twitter.com/i/status/2008170575286419869
Rahotanni na bayyana cewa, Kamfanin Man fetur na kasa, NNPCL, sun rage farashin man fetur daga Naira N835 zuwa Naira 815 akan kowace Lita
Hakan na zuwa ne yayin da Depot masu zaman kansu suka kara farashin man.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike na shirin tsayar da dansa takarar dan majalisa.
Rahoton yace Wike zai tsayar da dan nasa me shekaru 25 takarar ne a matsayin dan majalisar wakilai na Obio-Akpor.
Rahoton ya kara da cewa, Dan na Wike zai maye gurbin dan majalisa me suna Obio-Akpor ne a majalisar ta wakilai.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, duk me tunanin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai zace to ba a Najeriya yake zaune ba.
https://twitter.com/i/status/2008024362163765257
Tsohon Bidiyon Mahaifiyar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf inda take yabawa Kwankwaso ya bayyana a kafafen sada zumunta.
https://twitter.com/i/status/2008099523357556939
Wannan Bidiyon na zuwane yayin da Abba ke shirin komawa jam'iyyar APC.
Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar Manchester United ta kori Ruben Amorim a matsayin kocinta.
Hakan na zuwane bayan da ya kwashe watanni 14 yana matsayin kocin Kungiyar.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin dan kasar Portugal din me shekaru 40 da kungiyar a 'yan kwanakinnan.
Manchester United dai a yanzu tana matsayi na 6 akan teburin Premier league.
Manchester United ta sanar da Darren Fletcher a matsayin kocin wucin gadi.