Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Asibitin koyarwa na Jami’ar ABU zai fara yin aikin dashen Koda a shekarar 2025

Duk Labarai
Asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello Zaria dake jihar Kaduna zai fara aikin dashen koda ga marasa lafiya. Hakan zai kawowa mutane sauki matuka wajan yin dashen kodar. Daraktan kula da lafiya na jami'ar, Prof. Ahmed Umdagas ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Lahadi, yace tsakanin nan da watan Maris ne za'a fara aikin dashen kodar. Yace mafi yawan kayan aikin da ake bukata suna kasa kuma ma'aikatansu an horas dasu kan yanda zasu gudanar da aikin. Ya kuma bayyana cewa suna kokarin kawo kayan aikin kula da masu cutar daji watau Cancer.
Mun bar gidan kakan mu ba gyarane saboda bamu saci kudi ba, ba zamu iya kula da gidan ba>>Inji Jikan Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari

Mun bar gidan kakan mu ba gyarane saboda bamu saci kudi ba, ba zamu iya kula da gidan ba>>Inji Jikan Tsohon Shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari

Duk Labarai
Jika a wajan tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari, Bello Shagari ya bayyana cewa sun kasa kula da gidan kakansu, tsohon shugaban kasar ne saboda basu saci kudi ba kuma dalilin haka yasa ba zasu iya kula da gidan ba. Ya bayyana hakane a matsayin martani ga wani dake tambayarsa me yasa suka kasa kula da gidan kakan nasu. Alhaji Shehu Shagari na daya daga cikin tsaffin shuwagabannin da akewa kallon mutanen kirki saboda basu yi sata ba.
Rundunar ‘yansanda a Katsina ta ce ta kashe ‘yanfashi 40 a 2024

Rundunar ‘yansanda a Katsina ta ce ta kashe ‘yanfashi 40 a 2024

Duk Labarai
Kwamashinan 'yansanda na jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, Aliyu Musa, ya ce rundunarsu ta kashe 'yanfashin daji 40 daga farko zuwa ƙarshen shekarar 2024. Da yake magana yayin wani taron manema labarai na ƙarshen shekara a birnin Katsina ranar Litinin, kwamashinan ya ce sun kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su 319, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito. Kazalika a cewarsa, sun kama aƙalla mutum 916 a wannan tsakanin. "Mun samu nasarar ɗaiɗaita gungun miyagu da dama, mun ƙwato makamai, mun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, sannan mun yi nasarar gurfanar da wasu da dama a gaban kotu," in ji shi.
Akwai yiwuwar Man United ta koma ƙasan teburi – Amorim

Akwai yiwuwar Man United ta koma ƙasan teburi – Amorim

Duk Labarai
Shekara 50 kenan rabon da Manchester United ta faɗi daga gasar Premier League. Man United na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka zarta kowacce samun nasara a Ingila da ma duniya baki ɗaya, kuma mun saba ganin kulob ɗin yana shiga tsaka mai wuya a lokuta daban-daban. Sai dai a wannan karon lamarin ya sha bamban. A daren da ya gabata ne Newcastle ta doke Man United 2-0 har gida. Bayan kammala wasan da Newcastle ɗin ta ɗaiɗaita United a minti 30 na farko, mai horarwa Ruben Amorim ya fara tunanin faɗawa "relegation zone" - wato komawa ƙasan teburi. Da sashen BBC Sport ya tambaye shi game da ko suna ƙoƙarin guje wa faɗawa ƙasan teburin a yanzu, Amorim ya amsa da cewa: "ina akwai yiwuwar hakan. Dole ne mu faɗa wa magoya bayanmu gaskiya." Sakamakon wasan ya sa United ta koma ta 14 a...
Hisbah ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan Kano

Hisbah ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan Kano

Duk Labarai
Gwamnatin Kano ta fara kwashe 'dubban' yara da ke rayuwa a kasuwanni da ƙasan gadoji a Kano, babban birnin jihar. Gwamnatin ta fara ɗaukar matakin ne a jiya Litinin, inda ta samar da wani sansanin ajiyewa da kuma tantance yaran. Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce "mun samu rahoton akwai ɗaruruwa ko kuma dubban ƙananan yara da ba su haura shekara 15 ba waɗanda suke kwana a ƙarƙashin gadoji da cikin tashoshi da kuma kasuwanni." "Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da ta zamantakewa a nan gaba," in ji Daurawa. Shugaban na hukumar Hizba ya ce alƙaluman da suke da su sun nuna cewa akwai irin waɗannan yara masu gararamba a kan tituna sama da 5000. Ya kuma bayyana cewa za a tara yaran da aka kwashe ne a wata cibiya, ind...
Tinubu na cikin mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da rashawa a 2024 – OCCRP

Tinubu na cikin mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da rashawa a 2024 – OCCRP

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu na cikin na gaba-gaba a jerinn mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da kuma aikata cin hanci da rashawa, a cewar rahoton cibiyar kula da aikata manyan laifuka da rashawa ta duniya. CIbiyar Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP) kan nemi 'yanjarida da ƙwararru da ɗaiɗaikun mutane su kaɗa ƙuri'a wajen zaɓen mutanen da suka fi aikata tsararrun laifkuka a ɓangaren cin hanci da rashawa duk shekara. Tinubu ne ya zo na uku a jerin, yayin da tsohon Shugaban Syria Bashar al-Assad ya zo na ɗaya "saboda abubuwan da suka faru a ƙasar a baya-bayan nan," in ji OCCRP. Sai dai zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ko Tinubu kansa ba su ce komai ba game da sakamakon ƙuri'ar. Duk da cewa shi ne ya fi kowa yawan ƙuri'u, Shugaban Kenya William Ruto n...