Saturday, June 27
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: Yanda jirgin sama a Najeriya yayi batan hanya, ya sauka akan titin da motoci ke bi

Kalli Bidiyon: Yanda jirgin sama a Najeriya yayi batan hanya, ya sauka akan titin da motoci ke bi

Duk Labarai
Wani jirgin sama a jihar Delta yayi batan hanya inda ya sauka akan titin da motoci ke bi. Daga baya an ga jirgin ya tashi akan titin wanda na siminti ne. Da yawa sun yi mamakin cewa ashe Jirgin sama zai iya tashi akan titin mota. Tuni dai Ministan sufuri jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa, an kama matuka jirgin dan bincike. Wasu dai na zargin cewa kayan laifine jirgin ya je ya ajiye a wajan shiyasa suka yi karyar sun bata hanya. https://twitter.com/i/status/2064820164567183531
Kalli Bidiyon yanda VeryDarkman da mutanensa suka je barikin sojoji a Abuja suna cewa Shugaba Tinubu ya sauka daga Mulki, Wike ya sauka, Sojoji su karba

Kalli Bidiyon yanda VeryDarkman da mutanensa suka je barikin sojoji a Abuja suna cewa Shugaba Tinubu ya sauka daga Mulki, Wike ya sauka, Sojoji su karba

Duk Labarai
Wata zanga-zanga ta barke a babban birnin tarayya Abuja inda VeryDarkman yake jagorantarta. An gansu sun je barikin soji sun fadar cewa shugaba Tinubu ya sauka daga mulki, Shima Wike ya sauka daga Ministan Abuja. Sun kuma yi kira ga sojojin da su yi abinda ya dace. https://twitter.com/i/status/2064816103474307550
Kalli Bidiyon: An kama wata mahaifiya data yadda danta saboda shekararsa 5 da haihuwa amma baya kara girma

Kalli Bidiyon: An kama wata mahaifiya data yadda danta saboda shekararsa 5 da haihuwa amma baya kara girma

Duk Labarai
Wannan wata mahaifiyace da aka kama ta yadda danta a cikin ruwa. Yaron dai shekararsa 5 da haihuwa amma baya girma. Shine taje wajan wani Boka yace mata dan nata ba mutum bane kuma idan bata jefashi a ruwa ba duk wanda zata haifa irinsa ne zata ci gaba da haihuwa. Shine kuwa ta je ta jefa dan nata a ruwa amma an ganta shine aka kamata. https://twitter.com/i/status/2064272227567038867
A binciken da Sanatoci suka yi, sun gano wata badakala a ma’aikatar raya yankin Naija Delta, NDDC, inda aka gano sun kama ofis me daki daya akan Naira Miliyan 150

A binciken da Sanatoci suka yi, sun gano wata badakala a ma’aikatar raya yankin Naija Delta, NDDC, inda aka gano sun kama ofis me daki daya akan Naira Miliyan 150

Duk Labarai
Majalisar Dattijai ta binciki ma'aikatar raya yankin Naija Delta i da aka bukaci su yi bayanin yanda suka kashe Naira Biliyan 16 da aka basu. Saidai sun kasa. Daya daga cikin abinda aka gano sun yi shine kama ofis me daki daya akan Naira Miliyan 150. A yanzu dai an basu sati daya su je su tattaro bayanai kan yanda suka kashe kudaden. https://twitter.com/i/status/2064432604149866677
Kalli Bidiyon: Yanda Tsohon Mijin Sadiya Haruna, Isa A Isa ya je kasar Saudiyya yayi Addu’ar cewa duk me masa qazafin yana Luwqdy Allah ya saka masa

Kalli Bidiyon: Yanda Tsohon Mijin Sadiya Haruna, Isa A Isa ya je kasar Saudiyya yayi Addu’ar cewa duk me masa qazafin yana Luwqdy Allah ya saka masa

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Isa A. Isa ya bayyana a wani Bidiyo da yake addu'a a gaban ka'aba. An jishi yana Addu'ar Allah ya saka masa akan wadanda ke maza qazafin cewa yana Liwadi. https://www.tiktok.com/@isahaisah123/video/7649212971578821896?_r=1&_t=ZS-974oR6HC5cF A baya dai, Sadiya Haruna ta zargi tsohon mijin nata da cewa dan Luwadi ne.
Matar aure ta bani labarin ta yi saurayi a Tiktok kuma suna aikata duk abinda suke so, hakanan taje wajan Boka shima ya rika nemanta, yanzu dai ta dauki ciki>>Inji Sumshey

Matar aure ta bani labarin ta yi saurayi a Tiktok kuma suna aikata duk abinda suke so, hakanan taje wajan Boka shima ya rika nemanta, yanzu dai ta dauki ciki>>Inji Sumshey

Duk Labarai
Tauraruwar me sayar da kayan mata, Sumshey tace wata matar aure ta bata labarin cewa, mijinta matafiyine, idan ya jw wajanta yayi watanni 2. Yakan yi tafiya yaje wajan uwargidansa yayi watanni 5 ita kuma ba zata iya hakura ba. Hakan yasa ta fara Tiktok har ta yi saurayi kuma suna aikata duk abinda suke so. Saidai daga baya taso kashe aurenta amma mahaifiyarta ta hana. Dan hakane ma ta fara bin boka inda shima boka ya rika amfani da ita. https://www.tiktok.com/@sumshey_kayan_mata/video/7649104162327694612?_r=1&_t=ZS-974msCaksp6 https://www.tiktok.com/@sumshey_kayan_mata/video/7649469560654957844?_r=1&_t=ZS-974nW0tiXb8
Mazan Tiktok na damuna da kira suna cewa wai suna son aikata abinda bai kamata ba dani>>Inji Habiba Dorayi

Mazan Tiktok na damuna da kira suna cewa wai suna son aikata abinda bai kamata ba dani>>Inji Habiba Dorayi

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Habiba Dorayi ta bayyana cewa, Mazan Tiktok suna damunta da kira. Tace kuma yawanci ba kiran arziki ne suke mata ba, suna kirane suce mata suna son aikata abinda bai dace ba da ita. Ta yi kira a garesu su daina saboda kannenta da mahaifiyarta na daukar wayar idan an kira. https://www.tiktok.com/@habibadorayi/video/7649364569688771856?_r=1&_t=ZS-974l0LGKhfk
Kalli Bidiyon: Saurayi zaizo Zan saki jiki musha soyayya har ta kai zan iya yin komai akansa amma ina masa maganar aure sai yace wai nafi karfinsa>>Inji Tauraruwar fina-finan Hausa, Amal Umar

Tauraruwar fina-finan Hausa, Amal Umar ta koka da cewa maza na zuwa suce suna sonta amma da ta yi maganar aure sai su gudu. Ta bayyana hakane a wata hira da Nafisa Abdullahi ta yi da ita inda tace abin takaici ne. https://www.tiktok.com/@user6098028354806/video/7648545524995460373?_r=1&_t=ZS-974YQOBJMXJ
Kalli Bidiyon: Irin wulakancin da akawa ‘yan kwallon kasar Senegal a kasar Amurka, an rika musu bincike kamar wasu rikakkun masu laifi

Kalli Bidiyon: Irin wulakancin da akawa ‘yan kwallon kasar Senegal a kasar Amurka, an rika musu bincike kamar wasu rikakkun masu laifi

Duk Labarai
A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta an ga irin binciken da akewa tawagar 'yan kwallon kasar Senegal a dilin jirgin kasar Amirka. 'Yan kwallon da suka je buga wasan gasar cin kofin Duniya ta World Cup an gansu ana musu bincike na kwakwaf wanda ya jawo Allah wadai. A lokaci guda kuma an ga irin tarbar karamci da akawa 'yan kwallon kasar Mexico. https://twitter.com/i/status/2064259200864113100
Kalli Bidiyon: Rahotannin tsaro dake kawowa daga Zamfara duk karyane, yau gani a Dajin Zamfara ba sauran wata matsalar tsaro, Bello Matawalle ya gama dasu>>Inji Usman A. Adams

Kalli Bidiyon: Rahotannin tsaro dake kawowa daga Zamfara duk karyane, yau gani a Dajin Zamfara ba sauran wata matsalar tsaro, Bello Matawalle ya gama dasu>>Inji Usman A. Adams

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Usman A. Adams yayi ikirarin cewa, matsalar tsaron da ake kawowa daga jihar Zamfara karyace. Yace Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya gama da duk wata matsalar tsaro. Ya bayyana hakane a wani Bidiyo inda aka ganshi a wani daji da yace dajin jihar Zamfara ne kuma gashi ya je babu kowa a ciki. Yace Bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta abubuwan dake faruwane a kasashen Sudan, Mali, da Somalia. https://www.tiktok.com/@horonzango/video/7649125694554819848?_r=1&_t=ZS-974FWcxuZBk