Monday, December 15
Shadow

Duk Labarai

Abin mamaki ne yayin da Miliyoyin ‘yan Najeriya ke cikin matsananciyar yunwa amma Shugaba Tinubu ya ware Naira Biliyan 712 dan gyaran filin jirgin sama>>Inji Peter Obi

Abin mamaki ne yayin da Miliyoyin ‘yan Najeriya ke cikin matsananciyar yunwa amma Shugaba Tinubu ya ware Naira Biliyan 712 dan gyaran filin jirgin sama>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana cewa, abin Takaici ne irinnyanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ware Naira Biliyan 712 dan gyaran filin jirgin sama a yayin da Miliyoyin 'yan Najeriya ke fama da yunwa. Yayi wannan maganane a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke gargadin cewa mutane Miliyan 34 a Najeriya na cikin hadarin fadawa matsalar yunwa. Peter Obi yace mutanen da Yunwa kewa barazana 'yan uwan mu ne, makwabtan mu ne kuma abokan mu ne, yace abin takaici shine a irin wannan hali ne gwamnati zata ware biliyoyin Naira ba dan ciyar da talaka ba sai dan gyaran filin jirgin sama. Obi yace a shekarar 2013 An ranto dala Miliyan 500 inda aka gyara manyan filayen jiragen saman Najeriya, dake Lagos, Abuja, Kano, Port Harcourt, da Enugu. Yace...
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Farfaɗo da Masaku a Kaduna don Inganta Tattalin Arziki Da Ayyukan Yi

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Farfaɗo da Masaku a Kaduna don Inganta Tattalin Arziki Da Ayyukan Yi

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Farfaɗo da Masaku a Kaduna don Inganta Tattalin Arziki Da Ayyukan Yi. Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani shiri na farfaɗo da masana’antun auduga, masaku da tufafi a ƙasar, inda ƙaramin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Sanata John Enoh, ya kai ziyara jihar Kaduna domin duba muhimman masana’antun da suka shafi bangaren. Ministan ya bayyana cewa sake farfaɗo da waɗannan masana’antu zai taimaka matuka wajen habaka tattalin arzikin ƙasa da samar da ayyukan yi ga matasa da ma sauran ’yan ƙasa. Bayan gudanar da wannan ziyara ta gani da ido, Sanata Enoh ya halarci wani taro tare da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen dawo da martabar masana’antun sarrafa auduga da samar da tufafi a Najeriya. Ya ja...
Da yawan rukunin gidajen da aka yi watsi dasu a Abuja ma’aikatan gwamnati ne da suka saci kudi suke ginasu>>Inji EFCC

Da yawan rukunin gidajen da aka yi watsi dasu a Abuja ma’aikatan gwamnati ne da suka saci kudi suke ginasu>>Inji EFCC

Duk Labarai
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya bayyana cewa, da yawan rukunin gidajen da aka fara ginawa aka bari dake Abuja, ma'aikatan gwamnati ne da suka saci kudade ke ginasu. Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya faru a Abuja ranar Laraba inda aka tattauna batun gidaje. Yace da yawa ma'aikatan gwamnati ne suke fara ginin amma idan suka ajiye aiki ba zasu iya ci gaba da ginin ba. Yace dan haka ya kafa kwamiti na musamman dan su rika bibiyar irin wadannan gidaje ana bincike wanda suka mallakesu da kuma ina suka samu kudin.
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur a Abuja da Legas kadai

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur a Abuja da Legas kadai

Duk Labarai
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur dinsa a Abuja da Legas zuwa Naira 875 da kuma Naira 900. Hakan na zuwane kwanaki bayan da NNPCL din ya kara farashin zuwa Naira N915 da kuma Naira N955. Saidai a ranar Laraba, kafar TheCable ta ruwaito cewa, ta lura kamfanin ya rage farashin zuwa Naira 40 akan kowacce lita. A legas, Farashin ya ragu zuwa N875, sannan a Abuja farashin aguwa yayi zuwa N900. Saidai rahoton yace Dangote da Mobil da AP duka basu rage farashinsu ba yana nan a Naira 915 kan kowace lita.
Ba zamu zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba saboda giya zai ta kawowa Arewa>>Inji wani Jigo a APC

Ba zamu zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa ba saboda giya zai ta kawowa Arewa>>Inji wani Jigo a APC

Duk Labarai
Saboda Zai Sa A Shigo Da Giya Arewa, Don Haka Ba Za Mu Zabi Peter Obi Ba — Jigo a Jam’iyyar APC Wani jigo daga yankin Arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alwan Hassan, ya bayyana cewa Arewa ba za ta kada kuri’a ga Peter Obi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ba, saboda yadda ake alakanta shi da kasuwancin shigo da giya. Yayin da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Talata, Hassan ya caccaki Obi bisa yadda ya yaba da kamfanin giya a jihar Anambra da kuma rawar da yake takawa a harkar shigo da barasa. "Wa kuke tsammani zai kayar da Asiwaju a 2027? Obi wanda a shirin nan yana rokon goyon bayan Arewa, amma a lokaci guda yana murnar girman kamfanin giya a jiharsa kuma yana da hannu a shigo da barasa mafi yawa," in ji shi. "Yanzu ...
Kalli Hoto: Ganin Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai tsaye shi kadai a filin jirgi, babu ‘yan rakiya babu jami’an tsaro yasa wasu suke cewa, mulki baya dawwama

Kalli Hoto: Ganin Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai tsaye shi kadai a filin jirgi, babu ‘yan rakiya babu jami’an tsaro yasa wasu suke cewa, mulki baya dawwama

Duk Labarai
Wani Hoton Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a tsaye a filin jirgin sama ya dauki hankula. An ga El-Rufai tsaye shi kadai babu 'yan rakiya babu jami'an tsaro. Hakan yasa wasu ke cewa, Mulki baya dawwama. https://twitter.com/AbbaM_Abiyos/status/1953032421042987076?t=hvboBBvl1YCPed_ZYvgpug&s=19
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan 23.35 daga Kuwait dan ta yi maganin matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan 23.35 daga Kuwait dan ta yi maganin matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 23.35 dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna. Gwamnatin ta saka hannu ta karbo bashin a madadin gwamnatin jihar Kaduna wanda wannan na daga shirin ciwo bashin Dala Miliyan  $62.8m dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar. Daraktan yada labarai na ma'aikatar kudi ta tarayya, Mohammed Manga ya tabbatar da hakan inda yace za'a yi amfani da wannan kudi dan inganta karatun akalla yara 100,000. Sannan za'a yi amfani da kudin wajan gyaran makarantu da sauran abubuwan da suka shafi harkar ilimi a jihar.