Sojojin da suka yi juyin Mulki a kasar Guinea Bissau sun saki tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.
Jonathan na kasar a yayin da aka gudanar da juyin mulkin a matsayin dan sa ido kan zabe.
Saidai daga baya, sojojin sun raka shi filin Jirgi inda ya bar kasar.
Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana cewa, 'yan Bindigar da ake dasu a Arewa ba daga wata kasar waje suke ba 'yan Arewa ne.
Yace Fulatanci da Hausa suke yi.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1993976116105654731?t=muq01M4Dcf1VMPJumnjRww&s=19
Me kiwon Kaji ya dauki hankula bayan da ya bayyana cewa kowane daya daga cikin kajinsa yana sayarwa akan Naira 120,000.
Da yawa sun ce kajin sun yi tsada.
https://twitter.com/rand0muser98/status/1992130159349297421?t=5_6PG1BXM3P1OfmNu3J8mg&s=19
Hakan na zuwane yayin da Kiristoci ke shirin Bikin Kirisimeti.
Wata Matar aure da ta wa mijinta karyar zuwa Ibadan, ta wuce Abuja wajan Saurayinta.
Saidai 'yan Bindiga sun yi garkuwa da ita inda suka nemi kudin Fansa har Naira Miliyan 50.
Saurayin dai ya ce bashi da kudin, inda mijin shi kuma yace ba zai biya ba, inda yaran ke ta kuka.
Wata kotu a birnin Los Angeles na kasar Amurka zata sayar da gidan Fitsararriyar mawakiyar kasar, Nicki Minaj akan Dala Miliyan $20 dan a biya wani dogarinta diyya.
Dogarin ya kai Nicki Minaj da mijinta kara inda yake neman a biyashi diyyar $500,000.
Bayan hukuncin, Alqalin ya ce dan haka za'a sayar da gidan mawakiyar a biya wannan digari nata kudin diyyar da aka dora mata.
Wasu jami'an soji sun ce sun ƙwace cikakken iko da ƙasar Guinea-Bissau a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an kama shugaban ƙasar Umaro Sissoco Embaló.
Jim kaɗan bayan an ji ƙarar harbe-harbe a Bissau babban birnin ƙasar, majiyoyin gwamnati sun shaida wa BBC cewa an tsare Embaló.
Daga nan sai jami’an soji suka bayyana a gidan talabijin na ƙasar, inda suka ce sun dakatar da gudanar da zaɓen ƙasar da aka gudanar kuma za su ci gaba da tafiyar da harkokin ƙasar.
Al'ummar ƙasar ta yammacin Afirka na dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka hana dan takarar jam'iyyar adawa tsayawa takara.
A ranar Alhamis ne ake sa ran sakamakon kuma Embaló da abokin hamayyarsa Fernando Dias sun yi iƙirarin nasara.
Janar Denis N'Canha, shugaban so...
Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara kama Tshàgyèràn Dhàjì da suka shiga Kano suke aikatawa ayyukan laifuka.
Daya da aka kama a Fanshekara ya bayyana cewa a baya ya Shyeke mutane 3 kuma sukan yiwa mutane fashi da sauransu.
Yace shi ba dan Kano bane, zuwa yayi.
https://twitter.com/Asad_Mukty/status/1993590795505746091?t=m391nCIS5dwR0VfcpqiK4w&s=19
Wani malamin Addinin Islama daga yankin Yarbawa ya bayyana cewa, akwai wata aya a Qur'ani da idan aka karantata ake bacewa.
Malam yace lokacin yana makaranta da yake shi gwanin zuwa latti ne ya sha karantata ya wuce ba tare da an ganshi ba.
Saidai bai fadi ayar ba.
https://twitter.com/AsakyGRN/status/1993682138118410335?t=cQ0dmHRjm5wokbGTVK2Fyg&s=19
Tauraron Real Madrid, Kylian Mbappe ya ci kwallaye 3 rigis a mintuna 7.
Ya ci kwallayen ne a wasan da suka buga na Championships League da Olympiacos gaba daya a wasan kwallaye 4 yaci, shine dan wasa na farko da ya ciwa Real Madrid kwallaye 4 a mafi kankanin lokaci a wasan Champions league 1 tun bayan Cristiano Ronaldo.
Wannan Hatrick din tasa itace ta biyu mafi sauri da aka ci a cikin kankanin lokaci ta farko itace wadda Moh Salah yace a wasan Liverpool da Rangers.
Tsohuwar Budurwar mawakin Arewa, Amani ta bayyana cewa, ba ita ce a Bidiyon tsiraicin da ake yadawa a kafafen sada zumunta ba.
Sannan tace duk wanda yace itace bata yafe ba sai Allah ya musu sakayya.
Ta kara da cewa, wadda ke cikin Bidiyon tana da farata da ake sakawa na kwalliya ita kuma bata saka irin wadannan faratan.
Dan haka tace ba ita bace.
https://twitter.com/Amani_ishaq001/status/1993762307135176775?t=IU4mi-LaCqjG7M1hbc-SGg&s=19