Monday, March 2
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin jihar Naija ta Haramta yin wa’azi inda tace duk wani me wa’azi sai ya nemi lasisi

Gwamnatin jihar Naija ta Haramta yin wa’azi inda tace duk wani me wa’azi sai ya nemi lasisi

Duk Labarai
Gwamnatin Jihar Neja Ta Haramta Wa’azi Ba Tare da Lasisi Ba: Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da haramcin yin kowace irin wa’azi a fadin jihar tare da umartar cewa duk wanda ke son yin wa’azi sai ya mallaki lasisi daga hukumar kula da harkokin addini ta jihar. Daraktan Hukumar Harkokin Addini ta Jihar Neja, Malam Umar Farooq, ya tabbatar da hakan a wata hira ta wayar tarho da jaridar Punch a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa duk wani mai wa’azi ya kamata ya nemi lasisi daga nan zuwa cikin watanni biyu masu zuwa. “Gaskiya ne, gwamnati ta haramta yin wa’azi ba tare da izini ba. Duk mai wa’azi dole ne ya mallaki lasisi tsakanin yanzu da watanni biyu masu zuwa. Abin da ake buƙata shi ne, su zo ofishinmu, su karɓi fom, su cike, sannan su fuskanci kwamiti da zai tantance su kafin a basu damar...
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin irin cin amanar da aka masa a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na 2

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin irin cin amanar da aka masa a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na 2

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayar da labarin yanda ta kaya a shekarar 2015 da ya nemi sake cin zabe a karo na biyu. Ya bayyana hakane a yayin da ya je bikin cikar Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe shekaru 50 da haihuwa. Yace yawanci 'yan siyasa sun yaudareshi ne a 2015, yace siyasar Najeriya akwai cin amana sosai a cikinta, yace da wuya ka samu wanda zai tsaya kan magana daya ta gaskiya. Yace amma Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe mutum ne me nagarta wanda yana sonshi da gaske.
Karanta jadawalin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya Arziki

Karanta jadawalin shuwagabannin kasashen Duniya mafiya Arziki

Duk Labarai
Wannan Jadawalin shuwagabannin kasashen Duniya ne mafiya Arziki. Vladimir Putin (Russia) – $258 Bn Donald Trump (United States) – $6.1 Bn Kim Jong Un (North Korea) – $5 Bn Xi Jinping (China) – $1.5 Bn Teodoro Obiang Nguema Mbasogo (Equatorial Guinea) – $940 Mn Ilham Aliyev (Azerbaijan) – $500 Mn Recep Tayyip Erdoğan (Turkey) – $500 Mn Paul Kagame (Rwanda) – $500 Mn Cyril Ramaphosa (South Africa) – $450 Mn William Ruto (Kenya) – $400 Mn
Bayan da wannan hoton nashi ya jawo cece-kuce Gfresh yayi Bidiyo ba Filta inda yace nasu son ganinshi ba Filta gashi

Bayan da wannan hoton nashi ya jawo cece-kuce Gfresh yayi Bidiyo ba Filta inda yace nasu son ganinshi ba Filta gashi

Duk Labarai
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin yayi Bidiyo ba Filta inda yace masu son ganinshi ba Filta to gashi yayi Bidiyo ba Filta https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7545502116895411463?_t=ZS-8zSMjK3vyfA&_r=1 Hakan na zuwane bayan hotonsa da ya bayyana inda aka ganshi a wajan biki an daukeshu hoto yayi wani iri duk tabo a fuskar.
Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan jihar Kaduna ta gayyaci El-Rufai ya gurfana a gabanta dan amsa tambayoyi

Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan jihar Kaduna ta gayyaci El-Rufai ya gurfana a gabanta dan amsa tambayoyi

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da wasu 'yan APC 6 su gurfana a gabanta dan amsa tambayoyi. A takardar data fitar yau September 4, 2025 hukumar 'yansandan tace jam'iyyar ADC ta gabatar mata da El-Rufai da wasu mutane 6. Ta zargesu da hannu wajan tunzura mutane da kuma kawo hargitsi a jihar. Sauran wadanda aka gayyata tare da El-Rufai sune Bashir Sa’idu, Jafaru Sani, Ubaidullah Mohammed, Nasiru Maikano, Aminu Abita, da Ahmed Rufa’i Hussaini
2027: Da yiwuwar Kwankwaso ya shiga APC – Kofa

2027: Da yiwuwar Kwankwaso ya shiga APC – Kofa

Duk Labarai
Ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, bai rufe kofar shiga jam’iyyar APC ba gabanin zaɓen 2027. Jibrin, jigo a jam’iyyar NNPP, ya ce Kwankwaso har yanzu ya bar kofar tattaunawa a bude da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, duk da kasancewarsa ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023. Ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels inda ya ƙara da cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ƙarfin siyasa ce da ba za a iya watsi da ita ba. Sai dai ya nuna yiwuwar wasu masu ruwa da tsaki a APC na Kano na iya hana shigar Kwankwaso saboda muradunsu na siyasa. Jibrin, wanda ya sha ganawa da Shugaba Tinubu, ya ce komai yana yiwuwa a siyasa, duk da kasancewarsa ɗan Kwankwasiyya. A zaɓen 2023, Kwankwaso ya...
Rundunar yansandan Kano ta kama masu yi mata sojan gona

Rundunar yansandan Kano ta kama masu yi mata sojan gona

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama ƴansandan bogi uku da ake zargi da yin damfara ta hanyar shigar burtu a matsayin ƴansanda a jihar Kano, bayan sun damfari wani mutum naira miliyan ɗaya da dubu talatin. Mutanen da aka kama sun fito ne daga ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina inda aka kama su a ranar 2 ga Satumba, 2025, a Danagundi Quarters. Rundunar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da Jama’a na ƴansanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar. Sanarwar ta ce "Kamar yadda bincike ya nuna, an kama su ne bayan wanda suka damfara ya nemi ɗauki, inda ya yi bayanin yadda abin ya faru. "Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargi sun yi shigar burtu a matsayin ƴansanda inda suka yi iƙirarin cewa suna da wasu ƙwarewa na musamman da za su t...
Benjamin Hundeyin ya zama kakakin rundunar ƴansandan Najeriya

Benjamin Hundeyin ya zama kakakin rundunar ƴansandan Najeriya

Duk Labarai
Babban Sifeton Ƴansandan Najeriya, Kayode egbetokun ya naɗa CSP Benjamin Hundeyin a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar ƴansandan ƙasar (FPRO) Naɗin Hundeyin na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar mai barin gado, Muyiwa Adejobi ya fitar. ‎”Babban Sifeton ƴansandan ya buƙace shi da aiki da ƙwarewarsa ta sadarwa wajen inganta aikin ɗansanda a Najeriya ta hanyar ƙarfafa hulda da jama'a,'' in ji sanarwar. Kafin sabon muƙamin, CSP Benjamin Hundeyin ya kasamnce kakain rundunar ƴansanda reshen jihar Legas, inda ya kwashe shekaru yana wannan aiki.