Saturday, February 14
Shadow

Duk Labarai

Ashe shugaba Tinubu ya halarci Daurin auren dan Atiku da ya koma APC

Ashe shugaba Tinubu ya halarci Daurin auren dan Atiku da ya koma APC

Duk Labarai
Bayan da dan Atiku Abubakar, me suna Abba Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar APC. Lamarin ya dauki hankula sosai. Inda har sai da Atikun ya fito yace ra'ayin dansa ne ya koka jam'iyyar APC kuma ba zai tursasa masa ra'ayin siyasa ba. Saidai Rahotanni sun bayyana cewa, a baya, Shugaba Tinubu kamin ya zama shugaban kasa, ya halarci daurin auren dan Atikun da aka yi a Dubai.
Har Yanzu Beli Kyautane: Duk dansandan da yace ku bashi kudin beli ku kawo mana korafi>>Inji Hukumar ‘Yansanda

Har Yanzu Beli Kyautane: Duk dansandan da yace ku bashi kudin beli ku kawo mana korafi>>Inji Hukumar ‘Yansanda

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya reshen Abuja sun bayyana cewa, Har yanzu Beli Kyautane. Hukumar tace duk dansandan daya Bukaci sai an bashi kudi kamin a bayar da beli a kai musu karansa. Hakan ya fito ne daga bakin me magana da yawun hukumar,SP Josephine Adeh. Ta bayyana hakane yayin da ake ta korafi akan wasu 'yansanda da suka ki bayar da beli suka ce sai an biya kudi.
Kasar Amurka ta ware kudi har N587 billion ($413.046m) dan magance matsalar tsaro a Najeriya

Kasar Amurka ta ware kudi har N587 billion ($413.046m) dan magance matsalar tsaro a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Amurka ta ware kudi har Naira N587 billion ($413.046m) dan magance matsalar tsaro a Najeriya da sauran wasu kasashen Afrika. Hakan na kunshene a cikin kasafin kudin shekarar 2026. Hakan na zuwane bayan da Amurkar ta kai hari a jihar Sokoto. Hakanan kuma a baya, kasar Amurka ta kawowa sojojin Najeriya tallafin kayan aiki.
Da Duminsa: Kotun Koli ta tabbatar da daurin da akawa dan gidan tsohon gwamnan Jigawa, Aminu Sule Lamido

Da Duminsa: Kotun Koli ta tabbatar da daurin da akawa dan gidan tsohon gwamnan Jigawa, Aminu Sule Lamido

Duk Labarai
Kotun koli ta tabbatar da daurin da akawa dan gidan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Aminu Sule Lamido. A yau Juma'a ne kotun ta yi wannan hukunci inda tace daukaka kara da Aminu Sule Lamido yayi bashi bata bi ka'ida ba sannan ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara da kotun Gwamnatin tarayya suka yi akansa. A baya dai kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin kotun Gwamnatin tarayya akan Aminu Sule Lamido. An dai kama Aminu Sule Lamido ne da Dala $40,000 a filin jirgin sama wanda bai gayawa hukumomi cewa yana dauke da wannan kudaden ba. A hukuncin da aka masa, an bukaci ya baiwa gwamnati kaso 25 cikin 100 na kudin nasa sannan an daureshi a gidan yari.
Da Duminsa: Shahararren malaminnan na jihar Filato, Abubakar Abdullahi, wanda ya baiwa Kiristoci 262 kariya, ya rigamu gidan gaskiya

Da Duminsa: Shahararren malaminnan na jihar Filato, Abubakar Abdullahi, wanda ya baiwa Kiristoci 262 kariya, ya rigamu gidan gaskiya

Duk Labarai
shahararren malaminnan na jihar Filato, Abubakar Abdullahi, wanda shine Imam na kauyen Nghar a Barkin Ladi jihar Filato ya rigamu gidan gaskiya. Malamin shine wanda ya baiwa Kiristoci 262 kariya a masallaci da gidansa wanda dalilin hakan ya samu yabo da kyautuka a ciki da wajan Najeriya. Dansa, Saleh Abubakar ne ya tabbatar da rasuwarsa ga gidan jaridar Daily Trust inda yace mahaifin nasu ya rasu ne a daren Alhamis.