Sunday, January 12
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Abinda wannan sojan yayi bayan kama matarshi da kwarto ya dauki hankula

Kalli Bidiyo: Abinda wannan sojan yayi bayan kama matarshi da kwarto ya dauki hankula

Duk Labarai
Wani soja da ya kama matarsa na cin amanarsa da kwarto a gidansa ya baiwa mutane mamaki saboda matakin da ya dauka. Sojan ya samo kek ne inda ya tara mutane ya daurawa matar tasa aure da kwarton. https://twitter.com/wakajugbe/status/1860247504295436555?t=IJYRzJOelxlMq8UUk0PXCQ&s=19 A wani bidiyo da ya bayyana, an ha sojan na baiwa kwarton da matarsa kek din a baki.
Bayan watanni 3 Dangote ya koma siyo man fetur daga kasar Amurka

Bayan watanni 3 Dangote ya koma siyo man fetur daga kasar Amurka

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa matatar man fetur ta Aliko Dangote ta ci gaba da siyo man fetur daga kasar waje bayan kwashe watanni 3 ba tare da yin hakan ba. Hakan ya fito ne daga jaridar Bloomberg Inda tace yanzu haka akwai jiragen ruwa biyu dauke da man fetur din sun taso daga kasar Amurka zuwa Najeriya matatar ta Dangote. Hakan na zuwane bayan da aka yi maganar cewa kamfanonin dake hako man fetur a Najeriya zasu rika sayarwa da Dangoten danyen man fetur da kudin Naira maimakon dalar Amurka. Saidai wannan sabon labari na alamta cewa ga dukkan alamu wannan yarjejeniya ta samu Matsala.
Kalli Bidiyo budurwa ‘yar Kano ta sha yabo bayan da ta ki baiwa saurayi me motar G-Wagon ta Naira miliyan 200 Lambar wayarta

Kalli Bidiyo budurwa ‘yar Kano ta sha yabo bayan da ta ki baiwa saurayi me motar G-Wagon ta Naira miliyan 200 Lambar wayarta

Duk Labarai
Wani bidiyo da ya dauki hankula sosai a kafafen sadarwa ya nuna wata budurwa Inda aka ganta saurayi na zaune cikin motar Alfarma ta G-Wagon yana rokon ta bashi lambar waya amma ta kiya. https://twitter.com/Sarki_sultan/status/1858412815230402575?t=KyqhCIuU0S0KHEZtreNdMA&s=19 Budurwar dai a karshe haka ta taxi bata baiwa saurayin lambar wayar ba.
Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka bi sahun farar hula suka tsere yayin da bata gari suka sace akwatin zabe a wata mazaba dake jihar Ondo

Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka bi sahun farar hula suka tsere yayin da bata gari suka sace akwatin zabe a wata mazaba dake jihar Ondo

Duk Labarai
A yayin zaben jihad Ondo, wani abin mamaki ya faru India aka ga masu satar akwatin zabe sun kori mutane ciki hadda jami'an 'yansanda. Bidiyon dai ya nuna yanda 'yansandan da masu zaben suna jin harbi suka tsere da guru. https://twitter.com/TrendingEx/status/1858035226699546963?t=ps2EaKGTkBs4KGNPkXb9jg&s=19 Satar Akwatin Zane ba Sabin Abu bane a siyasar Najeriya.
Ji Yanda ta kaya tsakanin Hadiza Gabon da wani da yace mata a haka zata kare ba miji

Ji Yanda ta kaya tsakanin Hadiza Gabon da wani da yace mata a haka zata kare ba miji

Duk Labarai
Taurawar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta ta saka wani hotonta inda race tana Alfahari da kanta. Da yawan masoyanta sun mata fatan Alheri, saidai kamar ko da yaushe, an samu Wanda suka gaya mata ba dadi. Wani yace mata a haka zaki kare babu miji. Inda Hadizar ta amsa da cewa, diyarkace data kare a haka. Saidai saga baya ya bayyana mata cewa yayi nadamar maganarsa inda ya bata hakuri.
Sarauniyar Kyan Najeriya ta zo ta biyu a gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya

Sarauniyar Kyan Najeriya ta zo ta biyu a gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya

Duk Labarai
Sarauniyar kyau ta Najeriya, Chidimma Adetshina ta zo ta biyu a gasar Sarauniyar kyau ta Duniya da aka kammala a gasar Mexico. Sarauniyar kyau ta Najeriya da ta kasar Denmark ne suka kai Karshen gasar bayan doke sauran matan da suka kara dasu. Saidai a karshe, Sarauniyar kyau ta kasar Denmark CE ta lashe gasar inda ta Najeriya ta zo ta biyu. Saidai duk da haka an bayyana Sarauniyar kyau ta Najeriya a matsayin gwarzuwa wadda ta nuna bajinta sosai a gasar. Da Safiyar ranar Lahadi be aka kammala gasar wadda aka Dade ba'a yi me armashi da daukar hankali irinta ba.