Sunday, January 12
Shadow

Duk Labarai

Sarauniyar Kyan Najeriya ta zo ta biyu a gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya

Sarauniyar Kyan Najeriya ta zo ta biyu a gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya

Duk Labarai
Sarauniyar kyau ta Najeriya, Chidimma Adetshina ta zo ta biyu a gasar Sarauniyar kyau ta Duniya da aka kammala a gasar Mexico. Sarauniyar kyau ta Najeriya da ta kasar Denmark ne suka kai Karshen gasar bayan doke sauran matan da suka kara dasu. Saidai a karshe, Sarauniyar kyau ta kasar Denmark CE ta lashe gasar inda ta Najeriya ta zo ta biyu. Saidai duk da haka an bayyana Sarauniyar kyau ta Najeriya a matsayin gwarzuwa wadda ta nuna bajinta sosai a gasar. Da Safiyar ranar Lahadi be aka kammala gasar wadda aka Dade ba'a yi me armashi da daukar hankali irinta ba.
Addu’o’in mu ne yasa darajar Naira bata fadi aka rika sayar da dala daya akan Naira dubu 10,000 ba>>Inji Pasto Adebayo

Addu’o’in mu ne yasa darajar Naira bata fadi aka rika sayar da dala daya akan Naira dubu 10,000 ba>>Inji Pasto Adebayo

Duk Labarai
Babban Fasto na cocin (RCCG), Fasto Adebayo ya bayyana cewa addu'o'in da suke da taimakon Allah ne yasa darajar Naira bata fadi ba aka rika sayen dalar Amirka daya akan Naira dubu 10 ba. Tun bayan da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta cire tallafin dala ne farashin dalar yayi tashin gwauron zabi zuwa sama da Naira 1,600. Hakan ya taimaka wajan hauhawar farashin kayan masarufi.
‘Yansanda sun kama masu gàrkùwà da mutane a Kano

‘Yansanda sun kama masu gàrkùwà da mutane a Kano

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Kano sun kama masu laifi gida 82. An kamasu ne tsakanin Nov. 1 zuwa Nov. 14. Wanda aka kama din ana zarginsu da aikata laifukan kwacen waya, garkuwa da mutane da safarar kwaya. Kakakin 'yansandan jihar, Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana haka a hedikwatar 'yansandan jihar dake Bompai Kano. Ya bayyana cewa sun samu wannan nasara ne bayan wasu dabaru da suka fito dasu na kama masu laifi. Yace sun kwace makaman Bindiga AK 47 guda daya da bindigu kirar gida guda 3 da adduna da wukake guda 30 sai miyagun gwayoyi da sauransu. Ya bayar da tabbacin ci gaba da kokarin kawo zaman lafiya a jihar da yaki da aikata miyagun laifuka.
Karya ake mana, bamu ce mun daina siyo man fetur daga kasar waje ba>>NNPCL

Karya ake mana, bamu ce mun daina siyo man fetur daga kasar waje ba>>NNPCL

Duk Labarai
Kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya musanta Rahotannin dake cewa ya daina shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje inda a yanzu yake sayen man daga matatar man fetur ta Dangote. Labarai sun yadu dai cewa NNPCL tace ta daina shigowa da man fetur daga kasashen waje. Saidai a sanarwar da kakakin NNPCL din Mr Femi Soneye ya fitar yace wannan rahoto ba gaskiya bane. Yace suna dubawane su ga idan shigo da man fetur din daga kasar waje yafi sauki to daga wajen zasu siyo idan kuma sayenshi a gida yafi sauki to sai su siya a gida. Yace lamarin labarin cewa sun daina shigo da man fetur ba gaskiya bane inda ya jawo hankalin 'yan jarida da su rika yin bincike kamin watsa labaransu.
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn na shekarar 2025

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn na shekarar 2025

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn a matsayin kasafin kudin shekarar 2025. Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis bayan zaman majalisar zartaswa. Yace nan da ranar Juma'a ko Litinin ake tunanin gabatarwa da majalisar tarayya da kasafin kudin a hukumance.
An gano wani gidan Alfarma a kasar Amurka da ake zargin Tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya siya da kudaden sata

An gano wani gidan Alfarma a kasar Amurka da ake zargin Tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya siya da kudaden sata

Duk Labarai
An gano wani gidan Alfarma na miliyoyin daloli da tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya saya a kasar Amurka. Sambo Dasuki dai an kamashi bisa zargin cinye Biliyoyin kudade da aka ware dan yaki da kungiyar Boko Haram a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Sannan a wannan sabon bincike da ya bayyana an gano Dasuki yayi amfani da kudaden wajan sayen godajen Alfarma a biranen Los Angeles, California da kuma babbar unguwar masu kudi ta McLean, Virginia, dake babban birnin kasar Amurka, Washington, DC. Wata kungiya dake bincike da kwarmaton yanda ake sace kudaden talakawa a kasar Afrika me suna (PPLAAF) ce ta gano lamarin. Kungiyar tace wasu dake taimakawa Dasuki sayen gidajen alfarmar Robert da Mimie Oshodin sun karbi akalla Da...
Labari me Dadi: Gwamnatin tarayya zata rika samu kudin shiga da ya kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata

Labari me Dadi: Gwamnatin tarayya zata rika samu kudin shiga da ya kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata

Duk Labarai
Rahotanni sun ce biyo bayan karuwar yawan man fetur din da kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya sanar da cewa an samu na ganga Miliyan 1.8 duk kullun, yawan kudin da gwamnatin tarayya ke samu zai karu zuwa Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata. Farashin man Brent yana a matsayin dala $81 kowace ganga. Idan ana samun ganga Miliyan 1.8 kullun hakan na nufin Najeriya zata samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata. Shugaban kamfanin man fetur dun na kasa, Mele Kolo Kyari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis inda yace yawan man fetur din da Najeriya ke hakowa ya karu.