Gwamnatin jihar Naija ta Haramta yin wa’azi inda tace duk wani me wa’azi sai ya nemi lasisi
Gwamnatin Jihar Neja Ta Haramta Wa’azi Ba Tare da Lasisi Ba:
Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da haramcin yin kowace irin wa’azi a fadin jihar tare da umartar cewa duk wanda ke son yin wa’azi sai ya mallaki lasisi daga hukumar kula da harkokin addini ta jihar.
Daraktan Hukumar Harkokin Addini ta Jihar Neja, Malam Umar Farooq, ya tabbatar da hakan a wata hira ta wayar tarho da jaridar Punch a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa duk wani mai wa’azi ya kamata ya nemi lasisi daga nan zuwa cikin watanni biyu masu zuwa.
“Gaskiya ne, gwamnati ta haramta yin wa’azi ba tare da izini ba. Duk mai wa’azi dole ne ya mallaki lasisi tsakanin yanzu da watanni biyu masu zuwa. Abin da ake buƙata shi ne, su zo ofishinmu, su karɓi fom, su cike, sannan su fuskanci kwamiti da zai tantance su kafin a basu damar...








