Monday, January 13
Shadow

Duk Labarai

Da Duminsa: An sake Samun Fashewar Tankar Man Fetur A Jihar Jigawa

Da Duminsa: An sake Samun Fashewar Tankar Man Fetur A Jihar Jigawa

Duk Labarai
Rahotanni da muke samu na cewa wata tankar dakon man fetur ta sake fashewa a jihar Jigawa. Lamarin ya farune a kan iyakar jihar ta Jigawa da Kano. Kakakin hukumar kwana-kwana ta jihar, Aliyu M. A. Ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar laraba. Yace lamarin ya farune a Tsaida, Kwanar Kalle inda yace suna samun bayanan tashin gobarar suka garzaya inda lamarin ya faru kuma suka kasheta. Hakan na zuwane wata daya bayan da aka samu tashin gobarar motar dakon man fetur wadda ta kashe mutane akalla 170 a jihar.
Wani Dan Kabìlar Ibo Keñan Da Ya Karbi Musùĺùnci A Sansanin Masu Bautar Kasa Dake Garin Karaye A Kano, Inda Ya Sauya Sunansa Zuwa Yusuf

Wani Dan Kabìlar Ibo Keñan Da Ya Karbi Musùĺùnci A Sansanin Masu Bautar Kasa Dake Garin Karaye A Kano, Inda Ya Sauya Sunansa Zuwa Yusuf

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Dan Kabìlar Ibo Keñan Da Ya Karbi Musùĺùnci A Sansanin Masu Bautar Kasa Dake Garin Karaye A Kano, Inda Ya Sauya Sunansa Zuwa Yusuf Wace fata za ku yi masa?
Dan Gidan Attajiri Dahiru Mangal, Zai Auri ‘Yar Sanata Kwankwaso

Dan Gidan Attajiri Dahiru Mangal, Zai Auri ‘Yar Sanata Kwankwaso

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Za a daura auren ne a fadar Sarki Sanusi II dake birnin Kano a ranar Asabar mai zuwa, inda Gwamna Abba zai bada auren, yayin da ake sa ran halartar manyan baki a wajen bikin.
Trump ya naɗa Elon Musk shugaban ma’aikatar inganta aikin gwamnati

Trump ya naɗa Elon Musk shugaban ma’aikatar inganta aikin gwamnati

Duk Labarai
Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya naɗa Elon Musk a matsayin shugaban sabuwar ma'aikatar inganta ayyukan gwamnati. Kwamatin yaƙin neman zaɓen Trump ya kuma sanar da Vivek Ramaswamy, mai zuba jari a harkokin fasaha, domin yin aiki tare da Musk a ma'aikatar ta Department of Government Efficiency (Doge). Sunanta ya yi kama da sunan kuɗin kirifto da Elon Musk ya fi so mai suna Dogecoin, kuma an ƙirƙire ta ne domin kawo ƙarshen wahalhalu a harkokin gwamnati. Mutanen biyu za su dinga bai wa fadar White House ƙarƙashin gwamnatin Trump shawara ne kan "yadda za a gudanar da manyan sauye-sauye," a cewar Trump. Tun da farko, Trump ya sanar da naɗa mai gabatar da shiri a tashar talabijin ta Fox, Pete Hegseth, domin ya zama sakataren tsaro, sannan ya John Ratcliffe shugaban hu...
Darajar Naira ta fadi a kasuwar Canji

Darajar Naira ta fadi a kasuwar Canji

Duk Labarai
Farashin Naira ya fadi a kasuwar canji ta bayan fage data gwamnati. A kasuwar Gwamnati an sayi dalar akan Naira N1689.88 ranar Litinin inda a ranar Talata kuma aka sayi Dalar akan N1681.42. Inda a kasuwar bayan fage kuwa an sayi dalar akan Naira N1735 ranar Litinin amma ranar Talata aka sayeta akan Naira N1740. Hauhawar farashin dala dai na daya cikin abubuwan dake sanya kayan masarufi na tsada a Najeriya.
Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu’amulla da bankuna – CBN

Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu’amulla da bankuna – CBN

Duk Labarai
Babban Bankin Najeriya ya ce akwai 'yan ƙasar sama da miliyan 28 da ba su da hanyoyin mu'amulla da banki - yawancinsu kuma suna yankuna ne na karkara. Mataimakin gwamman bankin mai kula da fannin hada-hadar kuɗi, Philip Ikeazor, wanda ya bayyana haka jiya Talata, ya ce, bankin da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki tuƙuru domin rage wannanan matsala ta yadda za a samar da hanyoyin mu'amulla da bankuna da jama'a. Ya ce, alƙaluma sun nuna waɗanda ke cikin wannan rukuni na waɗanda ba su da hanyar samun bankuna yawanci mata ne da matasa da al'ummomin karkara da masu 'yan ƙanana da ƙanana da kuma matsakaitan sana'o'i. Mista Ikeazor, wanda ke magana a Lagos a wajen taron ƙasa da ƙasa na wannan shekara kan mu'amullar jama'a da bankuna ya ce, matakan da bankin yake ɗauka ne ma ya sa aka s...
Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa – Badaru

Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa – Badaru

Duk Labarai
Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun kammala shirye-shiryen murƙushe 'yan ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi da ke addabar jama'a a waɗansu jihohin arewa maso yammacin kasar. Hakan na zuwa ne bayan da 'yan ƙungiyar suka kai hari a makon daya wuce a jihar Kebbi inda suka hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu da dama. Ministan tsaro na Najeriya, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana ƙudurin rundunonin sojin ƙasar na tunkarar matsalar tsaron ta Lakurawa da ta kunno kai kwanannan, a hirarsa da BBC. Ministan ya ce manyan hafososhin tsaron Najeriya sun riga sun fitar da wani tsari na musamman da zai hana 'yan Lakurawan yin tasiri a arewacin kasar. Ya ƙara da cewa manyan hafsoshin rundunonin sojin ƙasa da na ruwa da na sama sun gana da hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, i...