Monday, January 13
Shadow

Duk Labarai

Dan Gidan Attajiri Dahiru Mangal, Zai Auri ‘Yar Sanata Kwankwaso

Dan Gidan Attajiri Dahiru Mangal, Zai Auri ‘Yar Sanata Kwankwaso

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Za a daura auren ne a fadar Sarki Sanusi II dake birnin Kano a ranar Asabar mai zuwa, inda Gwamna Abba zai bada auren, yayin da ake sa ran halartar manyan baki a wajen bikin.
Trump ya naɗa Elon Musk shugaban ma’aikatar inganta aikin gwamnati

Trump ya naɗa Elon Musk shugaban ma’aikatar inganta aikin gwamnati

Duk Labarai
Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ya naɗa Elon Musk a matsayin shugaban sabuwar ma'aikatar inganta ayyukan gwamnati. Kwamatin yaƙin neman zaɓen Trump ya kuma sanar da Vivek Ramaswamy, mai zuba jari a harkokin fasaha, domin yin aiki tare da Musk a ma'aikatar ta Department of Government Efficiency (Doge). Sunanta ya yi kama da sunan kuɗin kirifto da Elon Musk ya fi so mai suna Dogecoin, kuma an ƙirƙire ta ne domin kawo ƙarshen wahalhalu a harkokin gwamnati. Mutanen biyu za su dinga bai wa fadar White House ƙarƙashin gwamnatin Trump shawara ne kan "yadda za a gudanar da manyan sauye-sauye," a cewar Trump. Tun da farko, Trump ya sanar da naɗa mai gabatar da shiri a tashar talabijin ta Fox, Pete Hegseth, domin ya zama sakataren tsaro, sannan ya John Ratcliffe shugaban hu...
Darajar Naira ta fadi a kasuwar Canji

Darajar Naira ta fadi a kasuwar Canji

Duk Labarai
Farashin Naira ya fadi a kasuwar canji ta bayan fage data gwamnati. A kasuwar Gwamnati an sayi dalar akan Naira N1689.88 ranar Litinin inda a ranar Talata kuma aka sayi Dalar akan N1681.42. Inda a kasuwar bayan fage kuwa an sayi dalar akan Naira N1735 ranar Litinin amma ranar Talata aka sayeta akan Naira N1740. Hauhawar farashin dala dai na daya cikin abubuwan dake sanya kayan masarufi na tsada a Najeriya.
Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu’amulla da bankuna – CBN

Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu’amulla da bankuna – CBN

Duk Labarai
Babban Bankin Najeriya ya ce akwai 'yan ƙasar sama da miliyan 28 da ba su da hanyoyin mu'amulla da banki - yawancinsu kuma suna yankuna ne na karkara. Mataimakin gwamman bankin mai kula da fannin hada-hadar kuɗi, Philip Ikeazor, wanda ya bayyana haka jiya Talata, ya ce, bankin da sauran masu ruwa da tsaki suna aiki tuƙuru domin rage wannanan matsala ta yadda za a samar da hanyoyin mu'amulla da bankuna da jama'a. Ya ce, alƙaluma sun nuna waɗanda ke cikin wannan rukuni na waɗanda ba su da hanyar samun bankuna yawanci mata ne da matasa da al'ummomin karkara da masu 'yan ƙanana da ƙanana da kuma matsakaitan sana'o'i. Mista Ikeazor, wanda ke magana a Lagos a wajen taron ƙasa da ƙasa na wannan shekara kan mu'amullar jama'a da bankuna ya ce, matakan da bankin yake ɗauka ne ma ya sa aka s...
Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa – Badaru

Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa – Badaru

Duk Labarai
Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun kammala shirye-shiryen murƙushe 'yan ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi da ke addabar jama'a a waɗansu jihohin arewa maso yammacin kasar. Hakan na zuwa ne bayan da 'yan ƙungiyar suka kai hari a makon daya wuce a jihar Kebbi inda suka hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu da dama. Ministan tsaro na Najeriya, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana ƙudurin rundunonin sojin ƙasar na tunkarar matsalar tsaron ta Lakurawa da ta kunno kai kwanannan, a hirarsa da BBC. Ministan ya ce manyan hafososhin tsaron Najeriya sun riga sun fitar da wani tsari na musamman da zai hana 'yan Lakurawan yin tasiri a arewacin kasar. Ya ƙara da cewa manyan hafsoshin rundunonin sojin ƙasa da na ruwa da na sama sun gana da hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, i...
Ɓangarori uku da Saudiyya ta yi alƙawarin taimaka wa Najeriya

Ɓangarori uku da Saudiyya ta yi alƙawarin taimaka wa Najeriya

Duk Labarai
Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed Bin Salman ya yi alkawarin cewa gwamnatin ƙasar za ta taimaka wa Najeriya wajen inganta tattalin arzikinta. Yarima Bn Salman ya bayar da tabbacin ne bayan ganawa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu a gefen taron ƙasashen Larabawa da Musulmi a birnin Riyadh, wanda aka kammala ranar Litinin. A cewar wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Mohammed ya yaba da irin tsare-tsaren farfaɗo da tattalin arziki da Tinubu yake ɗauka, inda ya ce irinsu Saudiyya ta ɗauka domin samun ci gaba lokacin da ya zama firaminista. An shafe kimanin shekara ɗaya ana tattaunawa tsakanin Najeriya da Saudiyya kan batun zuba jarin tun bayan da aka kaddamar da kwamitin kula da harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen. Shugab...
Dan jarida ya zargi hukumar Kwastam da taimakawa masu fasa kwaurin shikafa zuwa cikin Najeriya

Dan jarida ya zargi hukumar Kwastam da taimakawa masu fasa kwaurin shikafa zuwa cikin Najeriya

Duk Labarai
Dan jarida me binciken kwakwaf, Fisayo Soyombo ya zargi hukumar Kwastam da taimakawa masu fasa kwaurin shinkafa zuwa cikin Najeriya. A bayanan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce yanzu haka ana sauke shinkafar da aka shigo da ita daga kasar Benin Republic a Lusada dake karamar hukumar Ado Odo/Ota ta jihar Ogun. Soyombo ya bayyana cewa lamarin na faruwane a ranar Laraba inda yace kuma an sallami duka wani jami'in Kwastam da zai kawo tangarda a lamarin. Dan jaridar yace sauran shinkafar za'a tafi da ita zuwa Legas. A baya dama dan jaridar ya bayar da bayanai akan shigowa da shinkafar amma hukumar kwastam ta karyatashi.
Kasar Amurka ta ki yadda ta bayar da bayanai akan rayuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda tace wakilintane dake taimaka mata wajan cimma burikanta

Kasar Amurka ta ki yadda ta bayar da bayanai akan rayuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda tace wakilintane dake taimaka mata wajan cimma burikanta

Duk Labarai
A yayin da aka shigar da wata kara a kotun kasar Amurka ake neman bayanai game da rayuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a baya inda ake zargin ya yi ta'ammuli da kwaya da kuma maganar ingancin takardun karatunsa, kasar Amurka tace ba zata bayar da wadannan bayanai ba. Dan jarida, David Hundeyin ne ya shigar da kara yake neman bayanai akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kuma tun a shekarar data gabatane dai kotun kasar Amurka ta ki yadda ta bayar da bayanan da yake nema. Dan jaridar yace hukumomin kasar Amurka, CIA, FBI, da DEA sun shigar da kara inda suma suke neman cewa kada a bashi bayanai akan shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu inda CIA wadda kungiyar leken Asiri ce ta kasar Amurka tace Bola Ahmad Tinubu wakilinta ne da take amfani dashi wajan cimma muradunta. Zuwa yanzu dai...
Na karbi mulki Najeriya na cikin wahala da matsin tattalin arziki shiyasa na dage dan kawo gyara>>Shugaba Tinubu

Na karbi mulki Najeriya na cikin wahala da matsin tattalin arziki shiyasa na dage dan kawo gyara>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya karbi mulkin Najeriya a yayin da take cikin wahalar rashin tabbas na tattalin arziki. Shugaban yace shiyasa ya dauki matakai tsaurara musamman a bangaren kudi dan ganin ya kawo ci gaba. Shugaban ya bayyana hakane a wajan rantsar da zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo inda mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilceshi. Yace a yanzu saboda matakan da ya dauka, kasar ta dauki hanyar ci gaba da nasara.