Saturday, May 16
Shadow

Duk Labarai

Ji yanda wani sabon Rikici ya kunno kai a fadar shugaban kasa dake Abuja

Ji yanda wani sabon Rikici ya kunno kai a fadar shugaban kasa dake Abuja

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Sabon Rikici ya kunno kai a fadar shugaban kasa tsakanin Sunday Dare da Daniel Bwala Rahoton yace a baya masu ruwa da tsaki a fadar shugaban kasar sun yi kuti-kuti aka kori Ajuri Ngilale daga fadar. Dalilin da yasa suka yi nasara shine dan shugaban kasar Seyi Tinubu ne ya kawoshi. Amma Shi Daniel Bwala shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne da kansa ya kirashi ya ce ya zo ya masa aiki kuma akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu. https://twitter.com/i/status/2041181867177546068
Kalli Bidiyon: Yaron Rarara ya samu karuwar da Namiji kuma saboda soyayyarsa da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya sakawa dan nasa sunan Shugaba Tinubu

Kalli Bidiyon: Yaron Rarara ya samu karuwar da Namiji kuma saboda soyayyarsa da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya sakawa dan nasa sunan Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Yaron Rarara, Abbani Rarara da ya samu karuwa da Namiji, ya saka masa sunan Shugaban kasa, Bola Ahmad. Daya daga cikin abokan Abbani dinne ya bayyana hakan. https://www.tiktok.com/@hon.bashirdanchiroma/video/7625288962000571669?_r=1&_t=ZS-95JYcXvQHAn&sp_source=7537614245375297080
Farashin Dala a kasuwar Chanji a yau

Farashin Dala a kasuwar Chanji a yau

Duk Labarai
Farashin dala a kasuwar Chanji ta gwamnati a yau Litinin, 6 ga watan Afrilu ya farane akan Naira ₦1,377.80 akan kowace dala. Idan aka kwatanta da farashin Naira ₦1,380.79 da aka sayar da dalar a ranar Juma'a, Za'a iya cewa darajar Naira ta tashi. A kasuwar bayan fage kuwa ta Legas, Kano, da Abuja ana sayar da dalar ne akan farashin 1,405 zuwa Naira 1,415
Kalli Bidiyon: Tsohon Mijina, Sani Musa Mai Iska, kamin mu tafi Ingila malamin Islamiyane amma da muka je can sai ya koma shaye-shaye, da bin mata, ya zama dan iska hadda saka dan kunne>>Inji Fati Muhammad

Kalli Bidiyon: Tsohon Mijina, Sani Musa Mai Iska, kamin mu tafi Ingila malamin Islamiyane amma da muka je can sai ya koma shaye-shaye, da bin mata, ya zama dan iska hadda saka dan kunne>>Inji Fati Muhammad

Duk Labarai
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Muhammad tawa tsohon mijinta, Sani Musa Mai Iska Tonon Silili inda ta bayyana cewa, kamin su tafi ingila tare dashi shi malamin makarantar Islamiyane. Tace amma da suka je can sai ya zama dan iska, ya fara shan Qiya, bin mata da saka dan kunne. Ta bayyana cewa, idan ya kai mace gida, sai yace mata wai ita kanwarsa ce. Tace haka taita addu'a har Allah ya rabata dashi. https://www.tiktok.com/@duniyar.kannywood8/video/7625377526969306386?_r=1&_t=ZS-95J8VlNHeJE&sp_source=7537614245375297080
A lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan an min tayin Naira Miliyan 80 in tallatashi amma naki yadda>>Inji Ali Jita

A lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan an min tayin Naira Miliyan 80 in tallatashi amma naki yadda>>Inji Ali Jita

Duk Labarai
Tauraron Mawakin Arewa, Ali Jita ya bayyana cewa, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, an masa tayin Naira Miliyan 80 ya tallata shugaban kasar amma yaki amincewa. Ya bayyana hakane a hirarsa da Fati Muhammad inda yace Har Ali Nuhu ya kira amma dai haka suka bar abin ya shiririce. https://www.tiktok.com/@speciall101/video/7624954846772202782?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7624954846772202782&source=h5_m&timestamp=1775461311&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_i...