Jimullar Bashin da ake bin Najeriya ya nuna kowane dan Najeriya ana binshi bashin Naira dubu dari shida(600,000)
Rahotanni sun nuna cewa jimullar bashin da ake bin Najeriya ya nuna cewa kowane dan kasa ana binshi bashin Naira N619,501.
Bayanai daga ofishin dake kula da bashin Najeriya sun nuna cewa ana bin Najeriya jimullar bashin Naira Tiriliyan N134.297.
Bashi dai na daya daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi dan samun kudin shiga wanda ake gudanar da ayyukan raya kasa dasu.