Saturday, May 16
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyon: ADC ta kwace mana El-Rufai, Sannan ta Kwace mana Abubakar Malami, Sannan ta kwace mana Rotimi Amaechi dan haka ba zamu barsu su zauna lafiya ba sai mun tarwatsa su>>Inji me magana da yawun APC

Jigo a jam'iyyar APC ya bayyana cewa, zasu ci gaba da ganin cewa sun yi dukkan mai yiyuwa dan tarwatsa jam'iyyar ADC. Yace ADC ta kwace musu Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da Abubakar Malami, da Rotimi Amaechi dan haka ba zasu zuba ido su gansu sun yi nasara ba. Yace Kuma suna ADC din yasan suna nasu kokarin wajan gurgunta jam'iyyar APC dan haka suma zasu yi iya nasu kokarin. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. https://twitter.com/i/status/2039869216052908509
Kalli Bidiyon: Yanda wani soja ke shan yabo bayan da ya tare wata Budurwa yake mata fada saboda shigar banza da ta yi

Kalli Bidiyon: Yanda wani soja ke shan yabo bayan da ya tare wata Budurwa yake mata fada saboda shigar banza da ta yi

Duk Labarai
An ga wani soja ya tare me mashin ya ce wata Budurwa ta sauko inda yake mata fada saboda shigar banzar data yi yana gaya mata rashin dacewar hakan. Lamarin ya farune a jihohin Inyamurai. Da yawa dai sun yabawa sojan. Saidai wasu sun ce hakan ba huruminsa bane, ya wuce yona da iri. https://twitter.com/i/status/2039630237869265011
Gwamnoni, Dangote da sauran ‘yan kasuwa sun tarawa matar shugaban kasa, Remi Tinubu Naira Biliyan 66 a rana daya bayan kaddamar da gidauniyar neman Tallafi

Gwamnoni, Dangote da sauran ‘yan kasuwa sun tarawa matar shugaban kasa, Remi Tinubu Naira Biliyan 66 a rana daya bayan kaddamar da gidauniyar neman Tallafi

Duk Labarai
Bayan kaddamar da gidauniyar neman tallafin ciyar da talakawa da matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta yi a ranar Alhamis. Gwamnoni da Dangote da sauran 'yan kasuwa sun tara mata Naira Biliyan 66. Ministan lafiya da walwala, Prof Ali Pate ne ya tabbatar da hakan a jawabin da yayi. Rahoton yace Dangote ya bayar da tallafin Naira Biliyan 20. Kamfanin mai na kasa, NNPCL sun bayar da tallafin Naira Biliyan 10 Wasu abokan matar shugaban kasar sun bayar da tallafin Naira $500,000. Gidauniyar The Emeka Offor Foundation ta bayar da tallafin Naira Miliyan 500. Yace hakanan shugaba Tinubu ya amince a fitar da Naira Biliyan 17 dan wannan aiki. Sannan kowace jihar Najeriya ana tsammanin ta bayar da tallafin Naira Miliyan 500 wanda idan jihohi 36 suka bayar, Za'a tashi da Naira Bi...
Dangote ya bayar da Tallafin Naira Biliyan 20 bayan da Matar Shugaban kasa ta bude gidauniyar neman Tallafi

Dangote ya bayar da Tallafin Naira Biliyan 20 bayan da Matar Shugaban kasa ta bude gidauniyar neman Tallafi

Duk Labarai
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya sanar da bayar da tallafin Naira Biliyan 20 a cikin gidauniyar da matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta kaddamar Dangote yace zai bayar da kudadenne a cikin shekaru 5 masu zuwa. Ya bayyana hakane a wajan kaddamar da wannan gidauniya. Gidauniyar an kafatane dan samar da abinci ga marasa karfi. Hakanan kamfanin NNPCL ya bayyana cewa, shima zai bayar da tallafin Naira Biliyan 10 cikin shekaru 5 masu zuwa.
Nifa sai kun yi hakuri, Dama can Turanci na fara iyawa, Sai da na kai shekaru 9 sannan na fara koyon Hausa>>Inji Maryam Labarina

Nifa sai kun yi hakuri, Dama can Turanci na fara iyawa, Sai da na kai shekaru 9 sannan na fara koyon Hausa>>Inji Maryam Labarina

Duk Labarai
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Fatima Hussain wadda aka fi sani da Maryam Labarina tace sai an yi hakuri da ita dan kuwa Turanci ta fara iyawa. Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita a Gabon Show. tace sai da ta kai shekaru 9 ne sannan ta fara koyon Hausa wanda dalilin hakane ma yasa kakarta ta saka mata sunan ba hausa. Tace dan haka ne ake yawan jin tana saka turanci a cikin maganganunta. https://www.tiktok.com/@asmau_haruna_auta/video/7624255101645114644?_r=1&_t=ZS-95DJjmz0Rns
Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu bai shiga cikin garin Jos ba, A filin jirgin da ya sauka aka kai jama’ar da lamarin ya rutsa dasu ya gana dasu, lamarin ya jawo cece-kuce sosai

Kalli Bidiyon: Shugaba Tinubu bai shiga cikin garin Jos ba, A filin jirgin da ya sauka aka kai jama’ar da lamarin ya rutsa dasu ya gana dasu, lamarin ya jawo cece-kuce sosai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ziyarar da ya kai jihar Filato, bai shiga cikin gari ba a filin jirgi ya tsaya. Saidai kirawo wadanda lamarin ya rutsa dasu aka yi zuwa filin jirgin saman ya gana dasu acan. Hakanan shugaban ya bayyana cewa, Filin jirgin ba wutar Lantarki gashi kuma yana son komawa gida. https://twitter.com/i/status/2039771947232272843 Wannan Lamari dai ya jawo suka da Allah wadai ga shugaban kasar
Kalli Bidiyon: Bazan baku ko sisi ba amma na muku Alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba>> Shugaba Tinubu ya gayawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Jos

Kalli Bidiyon: Bazan baku ko sisi ba amma na muku Alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba>> Shugaba Tinubu ya gayawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Jos

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyanawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a jihar Filato cewa ba zai basu ko sisi ba. Yace Amma zai musu ta'aziyya kuma zai musu alkawarin cewa hakan ba zata sake faruwa ba. Shugaban ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai jihar Filato. https://twitter.com/i/status/2039748942586315251
Nine Halastaccen Shugaban Jam’iyyar ADC, kuma rade-radin da ake cewa wai na ajiye mukami na karyane, sai naga bayansu>>Inji Nafiu Bala da ya kai su Atiku, Kwankwaso, El-Rufai da Malami kotu yace shine shugaban ADC kwace suka masa

Nafiu Bala wanda yake ikirarin shine halastaccen shugaban rikon gwarya na jam'iyyar ADC ya bayyana cewa, rade-radin da ake yi cewa ya dauka daga mukaminsa ba gaskiya bane. Nafiu Bala dai shine ya kawo rikici a jam'iyyar ADC inda ya kai jiga-jigan Adawa kotu. Yace da tsohon shugaban jam'iyyar zai sauka, shi ya barwa rikon kwarya. https://twitter.com/i/status/2039666201173934172