Wednesday, January 15
Shadow

Duk Labarai

Sarkin Musulmi Ya Karrama Matashi Mai Aikin Shara Da Ya Tsinci Kimanin Naira Milyan 16 Ya Maida A Filin Jirgin Sama Na Kano

Sarkin Musulmi Ya Karrama Matashi Mai Aikin Shara Da Ya Tsinci Kimanin Naira Milyan 16 Ya Maida A Filin Jirgin Sama Na Kano

Duk Labarai
Daga Mukhtar A. Haliru Tambuwal Sokoto Matashin nan mai aikin shara a filin jirgin sama na kasa da kasa dake Kano, Auwal Ahmad Dankode da ya tsinci makudan kudi ya maida a kwanan baya (dalar Amurka dubu goma a wancan lokacin kimanin naira miliyan 16) ya kasance cikin wadanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Saad Abubakar CFR mni ya karrama a lokacin rufe taron makon Danfodiyo karo na 11 da aka gabatar a Sokoto. A duk shekara Mai Alfarma Sarkin Musulmi na karrama zababbun mutane da kuma wadanda suka yi wata bajinta ta hidima ga al'umma, ko addini ko makamantansa. An karrama wanda ya tsinci kudi cikin Keke Napep da wadda ta cinci kudi a Aikin Hajji, duk da matsin halin da ake ciki. 'Ýan Nijeriya sun yi suna wajen tsinta da maida abin da suka tsinta ciki da wajen wannan ka...
Nan da shekarar 2074 Najeriya sai ta fi kasashen Saudiyya, Ingila, Canada da Japan karfin tattalin Arziki>>Inji Bankin Kasar Amurka

Nan da shekarar 2074 Najeriya sai ta fi kasashen Saudiyya, Ingila, Canada da Japan karfin tattalin Arziki>>Inji Bankin Kasar Amurka

Duk Labarai
Bankin kasar Amurka,Goldman Sachs ya bayyana cewa nan da shekarar 2074 Najeriya sai tafi kasashen Canada, Saudiyya, Ingila da Spain karfin tattalin arziki. Bankin ya wallafa kasashen da zasu kasance mafiya karfin tattalin arziki nan da shekarar 2074 kamar haka: Projection of world's biggest economies in 2075. China: $57 trillionIndia: $52.5 trillionUnited States: $51.5 trillionIndonesia: $13.7 trillionNigeria: $13.1 trillionPakistan: $12.3 trillionEgypt: $10.4 trillionBrazil: $8.7 trillionGermany: $8.1 trillionMexico: $7.6 trillionUK: $7.6 trillionJapan: $7.5 trillionRussia: $6.9 trillionPhilippines: $6.6 trillionFrance: $6.5 trillionBangladesh: $6.3 trillionEthiopia: $6.2 trillionSaudi Arabia: $6.1 trillionCanada: $5.2 trillionTurkey: $5.2 trillionAustralia: $4.3 trillionItaly: ...
Matata na lakada min dukan tsiya, Magidanci ya kai kara kotu a raba aurenshi da matarsa

Matata na lakada min dukan tsiya, Magidanci ya kai kara kotu a raba aurenshi da matarsa

Duk Labarai
Wani magidanci me suna Saka ya kai matarsa me suna Sadia kara kotu inda yake neman a raba aurensu saboda tana shan giya da dukansa da fitsarin kwance. Saka yace auren Sadia yasa ya rasa farin ciki inda yake zaune cikin kuncin rayuwa. Yace har Naira 50,000 ya bata dan ta fara kasuwanci amma ta kashe kudin wajan shan giya. Yace a kowane lokaci bayan ta sha giya, haka take zuwa ta kwanta ta rika fitsari akan gadonsu. Yace a duk lokacin da yayi korafi akan abinda take aikatawa takan kulleshi a daki ta rika lakada masa duka. Yace ya kaita wajan 'yansanda sau da yawa amma taki dainawa shine yace bari ya kai karanta kotu. Saidai matar itama tace ta gaji da auren a rabasu kawai, tace mijin nata bai cika hakkinsa na daukar nauyinta, Naira Dari 2 kawai yake bata. Saidai tace ko...
Gwamnan Abia ya Karrama Kwankwaso kan yadda Ya Gina Al’umma a rayuwarsa

Gwamnan Abia ya Karrama Kwankwaso kan yadda Ya Gina Al’umma a rayuwarsa

Duk Labarai
Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya karbi bakuncin Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa Sen. Rabi'u Musa Kwankwaso a gidan gwamnati dake Umuahia. Tattaunawar tasu ta ta'allaka ne kan siyasar kasa da kuma makomar Najeriya. A wani biki na musamman wanda Gwamna Otti ya karrama Sanata Kwankwaso da lambar yabo kan irin gudunmawar da ya bayar ga al’umma, a zamaninsa na Mulki da kuma bayan Mulki. Saifullahi Hassan
Cire tallafin Man fetur ne abu mafi kyau da armashi da ya faru da Najeriya>>Inji Sanata Sani Musa

Cire tallafin Man fetur ne abu mafi kyau da armashi da ya faru da Najeriya>>Inji Sanata Sani Musa

Duk Labarai
Sanata Sani Musa wanda shine shugaban kwamitin dake kula da kudi a majalisar tarayya ya bayyana cewa, cire tallafin man fetur ne abu mafi kyau da ya faru da Najeriya. Yace hakan zai bayar da damar yanayin kasuwa ya bayyana farashin man fetur din. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace wannan mataki zai bayar da damar raba arzikin gwamnati yanda ya kamata. Yace idan dai kudaden da ake turawa Gwamnoni suna aiki dasu yanda ya kamata, za'a samu ci gaba sosai. Yace cire tallafin zai sa gwamnati ta samu karin kudin shiga ta yanda zata rika kashe kudaden nata ta hanyar da ya dace.