Kotu Ta Tasa Keyar Wasu Mutane Biyar Zuwa Gidan Yari A Kano Saboda Awakinsu Sun Ci Shukar Gwamnati
Kotu ta yanke wa mutane biyar hukunci bisa sakin awaki su lalata bishiyu a Kano.
Wata kotun majistare da ke Kano ta yanke wa mutane biyar hukuncin daurin wata guda a gidan yari saboda barin awakinsu su yi yawo babu kulawa tare da lalata shuke-shuken ado da gwamnatin jihar ke yi a titunan Lodge Road da Race Course Road.
Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wadanda aka kama, karkashin jagorancin Usman Abdullahi, bisa sashe na 7(e) na dokar lafiyar jama’a ta jihar Kano ta shekarar 2019, wadda ke haramta duk wani aiki da zai lalata kayayyakin more rayuwa na gwamnati ko ya zama barazana ga muhalli.
LEADERSHIP ta rawaito cewa lamarin ya jawo hankalin jama’a makonni da suka gabata bayan jami’an ma’aikatar sun kama awaki 17 da aka samu suna kiwo a cikin ...








