Lalacewar wutar Lantarki:Majalisa ta gayyaci ministoci dan binciken yanda aka yi da Dala Biliyan $2 da aka bayar da samar da wutar Lantarki
Majalisar wakilai ta gayyaci ministoci 3 da suka hada da na Noma, da samar da abinci, Abubakar Kyari da na kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, Uche Nnaji, dana kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu dan su mata bayani kan yanda aka kashe Dala Biliyan $2 da aka bayar dan samarwa da Najeriya wutar lantarki.
Kwamitin kula da makamashi na zamani na majalisar ne suka gayyaci ministocin.
Kudin an samo su ne daga tallafi da kuma zuba jari dan samarwa da Najeriya wata hanya ta daban ta samun wutar lantarki banda wadda ake da ita.
Kuma an samu kudinne daga shekarar 2015 zuwa yanzu.
A ranar Talata da Larabane dai ministocin zasu gurfanar gaban majalisar dan bayar da ba'asi kan yanda aka kashe wadannan kudade.
Majalisar ta nuna damuwa kan cewa duk da wadannan kudade amma gashi wut...